
Zargi: Wani bidiyo da ke yawo a soshiyal mediya musamman a whatsApp yana zargi wai gwamnonin APC sun kai ziyara wajen dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar bayan da jam’iyyar mai mulki ta tabbatar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takararta.

Wannan zargi ne da ke neman tayar da zaune tsaye domin an dauki hotunan ne daga farkon wannan shekarar sadda Atiku ya kai gaisuwar ta’aziya ga iyalan Dahiru Mangal, bisa rasuwar mahaifiyar shahararren dan kasuwar a Katsina
Cikakken bayani
Kasa da sa’o’i 24 bayan da tsohon gwamnan Legas Bola Ahmed Tinubu ya bayyana a matsayin dan takarar kujerar shugabancin kasar a karkashin inuwar jam’iyya mai mulki ta APC, wasu masu amfani da kafofin sadarwar soshiyal mediya suka fara raba wani bidiyo wanda ke zargin wai gwamnonin yankin arewacin kasar sun gana da Atiku dan takarar PDP
A bidiyon mai tsawon dakiku 29 an ga Atiku a wani daki tare da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan, gwamnan jihar Yobe Maimala Buni, gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari da gwamnan Jigawa Mohammad Badaru da dai sauransu.
Bidiyon na dauke da gajeren sakon da ke zargin wai shugabanin APC na wa Tinubu makarkashiya bayan da aka zabe shi a matsayin dan takarar shugaban kasa.
An yi wa bidiyon taken: Gwamnonin arewa na jam’iyyar APC sun ziyarci Atiku. Wadannan ne mutanen da su ka baiwa Tinubu tikitin jam’iyyarsu sa’o’i 24n da su ka gabata ga shi yanzu sun kama hanya sun je wajen abokin hamayyar sa.”
“Idan wannan ba makarkashiya ba ce me ce ce. Sun karbi dalolin shi sun mika mi shi tikiti amma nan da nan sun juya ma sa baya.
DUBAWA ta lura cewa wasu ‘yan Najeriya sun yarda da sakon bidiyon , domin akwai wani ma wanda ya hakikance a dandalin WhatsApp yana cewa shugabannin arewa da yawa za su kaurace wa jam’iyyar APC su koma PDP.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da tantance mafarin bidiyon a manhajar InVid. Sakamakon ya nuna cewa bidiyon ya bayyana a shafukan intanet a karon farko ranar 22 ga watan Janairun 2022 lokacin da Atiku ya kai gaisuwar ta’aziya ga iyalin Dahiru Mangal wannan dan kasuwa a Katsina wanda ya rasa mahaifiyarsa mai shekaru 85 na haihuwa.
Dahiru Mangal shi ne ciyaman na Afdin Group kamfanin da ya mallaki jirgin saman Max Air, kamfanin man fetur ma Afdin Petroleum da kamfanin gine-gine na Afdin Construction da sauransu.
Karin bincike ya nuna mana cewa dan takarar shugaban kasar na PDP da kan shi ya wallafa hotunan a shafin shi na tiwita.
Ga abin da ya rubuta a shafin “ Yau (22 ga watan Janairu) na kai gaisuwar ta’aziya ga iyalin Dahiru Mangal a Katsina sakamakon rasuwar mahaifiyarsa Hajiya Murja Bara’u. Ina addu’ar Allah ya bai wa iyalinta dangana ya kuma sa makomarta ta kasance Aljannah Firdaus.”
Binciken DUBAWA ya nuna cewa lallai hotunan na da alaka da bidiyon da ake zargi domin shigen kayan da mutanen da ke cikin hoton su ka sanya kusan daya ne.,
A Karshe
Labarin da ke zargin wai gwamnonin APC sun kai ziyara wajen Atiku bayan da aka zabi Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa a inuwar APC ba gaskiya ba ne. DUBAWA ta gano cewa ziyara ce shi kan shi Atikun ya kai kamar sauran wadanda su ka kasance a hoton, daga farkon wannan shekarar lokacin da Dahiru Mangal wani dan kasauwa kuma hamshakin mai kudi a Katsina ya rasa mahaifiyarsa.