|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Issaiaka the blogger a shafinsa na Facebook ya wallafa wani bidiyon da ya nuna yadda wasu fasinjojin jirgin kasar da mahara suka yi garkuwa da su ke kuka su na neman a kawo musu dauki wanda hakan ke nuna yadda mahara ke cin zarafin ‘yan Najeriya.
Hukunci: Yaudara ce! Bidiyon da aka yadda a kafar sada zumunta na Facebook a matsayin bidiyon da aka dauka cikin kwanakin nan tsoho ne domin a shekarar 2022 ne aka dauki bidiyon a harin da mahara suka kai wa jirgin Abuja zuwa Kaduna.
Cikakken Labari
A ranar 25 ga Agusta 2026 Issiaka a shafinsa na Facebook ya wallafa wani bidiyon mai tsawon minti biyu da sakan 53 inda ya nuna wasu mutane na kuka suka neman a kawo musu dauki a wani wuri dake kama da daji yayin da maharan da suka kama su ke azabtar da su.
Bidiyon da (aka saka a nan) da da’awar “Labari mai zafi: yadda mahara ke azabtar da mutane ‘yan Najeriya da basu ji basu gani ba a Najeriya. Kungiyar Tarayyar Afrika ya kamata ta kawo mana dauki”.
A bidiyon wani murya na bayyana yadda yin garkuwa da mutane domin karban kudaden diyya ya zama babban sana’a a Najeriya inda kasawan gwamnati wajen dakile matsalolin rashin tsaro da aiyukkan ta’addanci na daga cikin matsalolin da ya haifar da haka.
A saka hotunan Babbab Hafsan Tsaro jana Olufemi Oluyede, tsohon shugaban rundunar ‘yan sanda ta kasa Usman Baba, shugaban kasa Bola Tinubu da ‘yan ta’adda aka saka a cikin bidiyon. Hotunan da bayanan da muryar ke yi na nuna matsalar rashin tsaron da ake fama da shi a Najeriya.
Zuwa ranar Asabar 29 ga Agusta 2026 mutum 534 sun nuna shi’awar su na bidiyon, 783 sun mai da martani, 566 sun sake wallafa bidiyon, da mutum 80 sun kasa alamar takarda.
Wani Katlego Daniel Moripa ya rubuta a shafinsa na Facebook “A taimake ni shin Afrika ba itace katuwar kasar Afrika bane? Ko dai dama matsayin kasan ta bai wa kanta?.
Ephraim Kaizer ya ce “ Najeriya ba kasa ba ne” sannan Cellose McLammar ya ce “Ya kamata wannan matsala ya tsaya. A nemi Donald Trump”.
DUBAWA ta amince ta gudanar da bincike musamman domin yadda bidiyon ya jawo ra’ayin mutane da yadda har yanzu ake fama da matsalar rashin tsaro a kasar nan.
Tantancewa
DUBAWA a binciken da ta gudanar ta kasa gano inda ake azabtar da mutanen da aka yi garkuwa da su sannan bidiyon da muryan dake bayani a ciki ba su nuna lokaci da inda aka dauki bidiyon ba.
Sakamakon binciken da gidan jaridar ta gudanar domin gano inda aka dauki bidiyon inda sakamakon ya nuna wasu bidiyon dake kama da wannan bidiyon da aka saka a Facebook, YouTube da Instagram.
Rahotanin da gidajen jaridu suka yi game da garkuwa da mutanen sannan da da’awar da aka rubuta kan bidiyon ya nuna cewa an saka bidiyon a yanar gizo a watan Yuli 2022.
Binciken ya kuma gano wani bidiyo da gidan jaridar Sahara Reporters ta wallafa ranar 24 ga Yuli 2022 da wanda aka saka a Facebook. A Facebook an saka wasu hotuna guda hudu da suke nuna yadda mahara ke azabtar da mutanen da suka yi garkuwa da su sannan da da’awar dake cewa “Bidiyo: yadda ‘yan ta’adda ke lakadawa fashinjojin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna da suka yi garkuwa da su dukan tsiya.
DUBAWA ta kuma gano wani rahoto da RipplesNigeria ta wallafa ranar 24 ga Yuli 2022 da taken “Maharan da suka yi garkuwa da fashinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun saki wani sabuwan bidiyo dake nuna wahalan mutanen ke sha a hannun maharan”. Rahotan ya nuna cewa maharan sun fitar da sabuwan bidiyo dake nuna yadda maharan ke azabtar da fashinjojin jirgin kasan yayin da suke tsare hannun maharan.
Rahotan ya kuma nuna cewa maharan na azabtar da wadannan mutane saboda suna fushi da gwamnatin Najeriya domin kin biyan bukatun su. rahotan ya nuna yadda mutanen ke kuka suna rokon gwamnatin Najeriya da gwamnatocin kasashen waje da su kawo musu dauki.
Jaridar Arise ta wallafa wani rahoto a ranar 24 ga Yuli 2022 da taken “yadda ‘yan ta’adda ke azabtar da fashinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna inda maharan ke wa shugaban kasa Buhari, gwamnan jihar Kaduna El-Rufa’i, sauran gwamnoni da sanatoci sannan sun saki bidiyo domin jadadda barazanar su.
Idan ba a manta ba a ranar 28 ga Maris 2022 mahara sun kai wa jirgin kasa a Kaduna hari inda har suka kashe mutum 8 tare da yin garkuwa da mutum 63.
DUBAWA ta gano wani bidiyo da gidan jaridar TVC ta wallafa wani bidiyo a YouTube (a nan da nan) inda ya nuna yadda mahara ke azabtar da mutanen da suka yi garkuwa da su. Duk wadannan bidiyon da aka gano ya taimaka wajen tabbatar da cewa an saka wannan bidiyo da dadewa kafin wanda aka saka a Facebook a shekarar 2026.
Sakamakon binciken da gidan jaridar ta gudanar ya tabbatar cewa bidiyon tsohon bidiyo ne sai dai kuma wanda aka saka a Facbook an gyara shi inda har da wata murya aka saka dake bayyana harin rashin tsaron da ake fama da shi a Najeriya sannan da saka hotun wasu manyan tsofaffi da sabbin hadiman gwamnati da yadda maharan ke azabtar da mutanen da suke yi garkuwa da su.
Sakamakon ya nuna cewa an saka wannan bidiyo a yanar gizo tun a shekarar 2022.
A Karshe
Bidiyon dake nuna yadda mahara ke azabtar da mutanen da suka yi garkuwa da su a Najeriya tsohon bidiyo ne domin DUBAWA ta gano cewa an dauki wannan bidiyo tun a ranar 28 ga Maris 2022 da mahara suka yi garkuwa da fashinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.
Wannan bincike an gudanar da shi ne a karkashin shirin Cibiyar Bunkasa Aikin Jarida da Kirkire-kirkire (CJID) tare da tallafin Tarayyar Turai (European Union).
