Dalar Amurka da Riyal na Iran. Hakkin Mallaka: Reuters
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da Facebook ya yi ikirarin cewa dala ɗaya kacal ($1) ta kai sama da miliyan ɗaya (IRR 1,137,500) a kuɗin Rial na ƙasar Iran.

Hukunci: Gaskiya ce. DUBAWA ta gano cewa kuɗin Iran (Rial) ya yi mummunar faduwa sakamakon takunkuman ƙasashen waje, durƙushewar tattalin arziki, da hauhawar farashi.
Cikakken Bayani
A ’yan kwanakin nan, kasar Iran ta sake fuskantar zanga-zanga a wasu sassa na ƙasar, sakamakon matsin tattalin arziki, hauhawar farashi, da kuma rashin jin daɗin al’umma kan yadda gwamnati ke tafiyar da lamurra.
A daidai wannan lokaci bayanai daban-daban na ci gaba da yawo a kafafen sada zumunta na Nijeriya, musamman a Facebook da WhatsApp, inda ake kwatanta halin tattalin arzikin Iran da na Nijeriya.
Daga cikin wadannan bayanai akwai ikirarin da ke cewa dala ɗaya ta kai sama da miliyan ɗaya a kuɗin Rial na Iran, lamarin da wasu ke amfani da shi wajen jaddada cewa duk da matsalolin Nijeriya, har yanzu Naira na da daraja fiye da kuɗin Iran.
Wani mai amfani da Facebook, Uthman Khan ya wallafa sakon da ke cewa (an adana a nan) dala ɗaya ($1) ta kai IRR 1,137,500 a Iran.
Zuwa ranar 15 ga watan Janairu, 2025, wallafar ta samu martani 354 (reactions) da sharhi 58, inda ta jawo ce-ce-ku-ce tsakanin masu amfani da kafar.
Daga cikin masu tsokaci, Maryam Shehu Musa ta ce: “Har gwara Naira kenan fa.” Sai dai wani mai suna Salim Ahmed ya ƙalubalanci ikirarin yana cewa: “Sam wannan zancen ba haka yake ba.”
Duba da yadda irin wannan bayani ke iya yaudarar jama’a ko haifar da fahimta mara tushe game da tattalin arzikin ƙasashe, musamman a lokacin da ake fama da tashin hankali da rikice-rikicen siyasa, DUBAWA ta gudanar da bincike domin tantance sahihancin ikirarin.
Tantancewa
DUBAWA ta duba bayanai daga manyan shafukan bayanan kuɗaɗen duniya da ke sa ido kan darajar kuɗaɗen ƙasashe.
A cewar bayanan Bonbast, wani shafin Iran da ke bibiyar kasuwar canjin kuɗi ta waje, dala ɗaya a kasuwar ‘black market’ ta kai fiye da IRR 1,100,000 a farkon 2025.
Haka kuma, shafin XE Currency Converter ya nuna cewa darajar Rial na Iran na ci gaba da raguwa sosai idan aka kwatanta da dala, kodayake gwamnati na da farashi daban na hukuma wanda ba ya aiki a zahiri a kasuwa.
Rahotanni daga kamfanin dillancin labarai na Reuters sun bayyana cewa Rial na Iran ya rasa darajarsa zuwa matakin da ba a taɓa gani ba, sakamakon tsananin hauhawar farashi da takunkuman tattalin arziki.
Bugu da ƙari, Al Jazeera ta ruwaito cewa darajar Rial ta karye sosai a kasuwar ‘open market’, inda mutane ke musayar kuɗi a farashi mafi muni fiye da na gwamnati.
Me ya sa kuɗin Iran ba ya da daraja?
Ƙasar Iran ta shafe shekaru da dama tana fuskantar takunkuman tattalin arziki daga Amurka da ƙawayenta, musamman tun bayan janyewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran a 2018.
Wannan ya rage yawan kuɗin waje da Iran ke samu, ya kuma jefa kuɗinta cikin mummunan koma baya.
Rahotanni sun bayyana cewa Iran na fama da:
- Hauhawar farashi sama da kashi 40%
- Ƙarancin kuɗin waje
- Hana fitar da ɗanyen mai a kasuwa
- Rashin zuba jari daga ƙasashen waje
Wadannan dalilai sun haɗu wajen rushe darajar Rial, har ta kai matsayin da ake buƙatar fiye da miliyan ɗaya na Rial don sayen dala ɗaya a wasu lokuta.
A Karshe
Ikirarin da ke cewa dala ɗaya ($1) ta kai IRR 1,137,500 a kuɗin Iran gaskiya ce.
