Haske mai kama da makami mai linzami da aka gani a Sokoto da Kebbi. Hakkin Mallaka: FB/DGL
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Masu amfani da kafafen sada zumunta a Sokoto da Kebbi sun ce sun ga wani abu mai kama da makami mai linzami ko shooting star yana wucewa ta sararin samaniya da dare.

Hukunci: Yaudara ce. Binciken DUBAWA ya nuna cewa hasken da aka gani a sararin samaniya na iya kasancewa motsin taurari da ake kira Eta Aquariids, ba makami mai linzami ko shooting star ba.
Cikakken Bayani
A ranar 27 ga Afrilu, 2026, da misalin karfe 11 na dare, mazauna wasu sassan jihohin Sokoto da Kebbi sun shiga kafafen sada zumunta suna cewa sun ga wani abu mai haske yana tafiya cikin sauri a sararin samaniya da dare.
Mutane da dama sun bayyana cewa abin da suka gani yana kama da makami mai linzami ko roka.
Lamarin ya janyo fargaba cikin gaggawa, musamman saboda yadda matsalar tsaro ke kara tsananta da kuma yadda mutane suke cikin damuwa kan duk wani abu da ya shafi hare-haren sama bayan harin saman Amurka da aka kai a Sokoto a watan Disamban 2025.
Irin wannan ikirari ya fito daga mazauna Jihar Kebbi, inda mutane suka rika yada hotuna da bidiyoyin hasken da aka gani a sararin samaniya.
Wani bangare na sakon Facebook din na cewa “ CIKIN GAGGAWA: Fargaba a Birnin Kebbi bayan wani haske mai kama da makami mai linzami ya ratsa sararin samaniya da dare!”
Saboda yadda ikirarin ya sanya tsoro a zukatan jama’a, DUBAWA ta gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da mutane suka gani.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da tuntubar jami’an tsaro a jihohin Sokoto da Kebbi domin tabbatar da ko akwai wani rahoton makami mai linzami ko fashewa da ya faru.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sokoto, Ahmad Rufa’i, ya shaida wa DUBAWA cewa babu wani rahoto da ya shafi makami mai linzami, hari ta sama ko fashewa a ko’ina cikin jihar.
Haka kuma Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi ta hannun Kakakinta, Bashir Usman, ta yi watsi da ikirarin cewa wani abu mai kama da makami mai linzami ya fadi ko ya fashe a jihar.
Domin kara tantance ikirarin, DUBAWA ta gudanar da bincike ta hanyar amfani da kalmomin bincike a Google, sai dai ba a samu wani sahihin rahoto daga kafafen yada labarai masu inganci kan harin makami mai linzami, fashewa ko wani hari ta sama a jihohin Sokoto da Kebbi ba.
Daga nan DUBAWA ta duba hotuna da bidiyoyin da aka yada a WhatsApp da X.
Hotunan sun nuna wani haske mai wutsiya yana gudu a sararin samaniya da dare — abin da masana ilmin taurari ke dangantawa da motsin taurari ko wani tauraro mai wuta yayin shiga sararin duniya.
Yiwuwar motsin taurari ne
Bayan nazarin lokacin da aka ga hasken da kuma yadda yake, DUBAWA ta gano cewa lamarin ya zo daidai da lokacin da ake samun motsin taurari na Eta Aquariids meteor shower.
Bayanan masana taurari sun nuna cewa Eta Aquariids meteor shower na faruwa daga ranar 19 ga Afrilu zuwa 28 ga Mayu, 2026.
A cewar kungiyar American Meteor Society, Eta Aquariids na daga cikin motsin taurari masu saurin tafiya tare da barin doguwar alamar haske a sararin samaniya.
Kungiyar ta bayyana cewa, “waɗannan taurari ne masu matukar sauri da suke tafiya da haske a sararin samaniya…”
Me ya sa aka gan shi a Sokoto da Kebbi?
Eta Aquariids yakan fi bayyana a yankunan da ke kusa da layin Equator saboda matsayin sa a sararin samaniya.
Jihohin arewacin Nijeriya ciki har da Sokoto da Kebbi na cikin wuraren da ake iya ganin irin wannan motsin taurari idan yanayin samaniya ya kasance ba giza-gizai.
Kasancewar sararin samaniyar arewa maso yammacin Nijeriya na da karancin gajimare a lokacin rani na kara saukaka ganin irin wadannan abubuwan na ilmin taurari.
Mai yiwuwa wannan ne ya sa mutane a wurare daban-daban suka ga wannan haske a lokaci guda.
A Ƙarshe
Ikirarin cewa mazauna Sokoto da Kebbi sun ga makami mai linzami yana ratsa sararin samaniya yaudara ce.
