Hoton dan bindigan da jami’an tsaro suka kama tsoho ne ba sabo ba

Image of suspected bandit arrested in Zamfara, not recent
Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani shafi a Facebook ya wallafa wani hoto dake nuna cewa jami’an tsaron wani kauye sun kama wani dan bindiga da ya buwayi mutane a jihohin Zamfara, Kaduna da Neja da hakan ke nuna cewa an kama maharin a cikin kwanakin nan.

Hoton dan bindigan da jami’an tsaro suka kama tsoho ne ba sabo ba

Hukunci: Yaudara ce. Hoton bai nuna cewa an kama dan bindigan a cikin kwanakin nan ba. Reverse-image ya binciki ratotani da hotuna inda sakamakon ya nuna cewa an kama dan bindigan tun a watan Afrilu 2026 sannan jami’an tsaron wani kauye ne suka kama shi bisa laifin yin jigilan makamai da boye cikin Jarka.

Cikakken Bayani

A ranar 3 ga Satumba 2026 Sagacious Bello Lukuman ya saka wani hoto da ya nuna yadda jami’an tsaro suka kama wani dan bindiga dake da alaka da shahararren dan bindiga Kachalla Gwaska.

Da’awar da aka rubuta a hoto da aka saka a (nan) y ace “Allah ya ci gaba da tona asirin mahara a Najeriya;  Jami’an tsaron sakai a jihar Zamfara sun kama wasu mutane inda a cikin su akwai masu hada baki da mahara, masu jigilar kaya wa mahara, likita da wani lauyan bogi. A cikin wadannan mutane akwai wani Abubakar Malan Ori mai shekara 20 dake da alaka da shahararren dan bindiga Kachalla Gwaska.

Da’awar ya jaro ra’ayoyin mutane da dama a Facebook inda wani Lateef Kolawole Akinsanya ya ce “Wannan gagarumar nasara ne a yakin da ake yi da ayyukan mahara a Najeriya; jami’an tsaro su ci gaba da kokari domin tabbatar da suka kama duk wadannan mutane domin yanke musu hukunci.

Jeremiah Nimfa ya ce “hassan ya fadi sunan wannan mutum a labarin da ya yi da English alhaji” Sannan Abdulsalam A. Aliyu ya nuna rasgin amincewar sa kan yadda aka nuna maharin inda yake cewa “shin wannan mutum ba kamata yayi da daure sa da sarka ba? Meneney a sa ake nuna shi a sake?

Zuwa ranar 4 ga Satumba 2026 mutum 639 sun ga hoton, 136 sun mai da martani da 85 sun sake wallafawa.

An sake ganin hoto irin haka da ya bayyana a Facebook inda a dalilin haka DUBAWA ta gudanar da bincike.

Tantancewa

DUBAWA ta yi amfani da Google reverse-image wajen tattance hoton inda ta gano cewa an wallafa labarin kama dan bindigan a watan Afrilu2026.

A ranar 24 ga Afrilu 2026 wani shafin yada labarai na Facebook Nigerian Armed Forces & Millitary News ta saka hoto kusan irin haka da ya tabbatar da dan bindigan a matsayin daya daga cikin mayakan Kachalla Gwaska amma kuma jami’an tsaron wani kauye a jihar Zamfara (ZCPG, da aka fi sanin su da sunan Askarawa) suka kama shi yayin da yake jigilar makamai.

Rahotan ya nuna cewa jami’an tsaron Zamfara ZCPG sun kama wani mahari dake da alaka da Bello Turji a jihar Zamfara yayin da yake jigilar makamai.

Jami’an tsaron sun kama dan bindigan da wadannan makamai dake boye a cikin Jarka bayan ya taso daga jihar Nasarawa za shi jihar Zamfara. A cewar jami’an tsaro.

A ranar 25 ga Afrilu 2026 Abba blogger ya saka wannan hoto da makaman da aka kama maharin da shi wanda aka alakanta shi da kungiyar ‘yan bindigan Bello Truji.

A binciken da DUBAWA ta gudanar ta gano sunan dan bindigan da aka kama a matsayin Abdulhamid Isa dake da alaka da Bello Turji da Baleri.

Gidan jaridar MediaSmartNews.com a labarin da ya wallafa ya nuna cewa maharin dan asalin kauyen Mashema ne dake karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.

Hoton wanda ya bayyana a yanar gizo tun a watan Afrilu za a iya ganinsa a nan,nan, nan da nan.

A Karshe

Hoton dake nuna an kama wani mahari dake da alaka da kungiyar mahara na Kachalla Gwaska a kwanakin nan da Askarawan ZCPG suka kama a kwanakin nan yaudara ce. An kama wannan dan bindiga tun a wata Afrilu 2026.

Wannan bincike an gudanar da shi ne a karkashin shirin Cibiyar Bunkasa Aikin Jarida da Kirkire-kirkire (CJID) tare da tallafin Tarayyar Turai (European Union).