|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook, ‘Issiaka the Blogger,’ ya yada wani bidiyo inda yayi da’awar cewa an samu sabuwar kungiyar ‘yanta’adda a Najeriya.
Hukunci: Karya ce. Mutanen da ke cikin bidiyon mambobi ne na sojojin fafutuka ne na Sudan People’s Liberation Army-In Opposition (SPLA-IO) a Sudan ta Kudu.
Cikakken Labari
Wani mai amfani da shafin Facebook, ‘Issiaka the Blogger,’ a ranar 19 ga watan Yuli,2026 ya yada wani bidiyo kamar yadda za a iya ganinsa (nan) inda yayi da’awar cewa mutanen da ake gani a bidiyon mambobi ne na sabuwar kungiyar ‘yanta’adda a Najeriya.
Ga abin da taken labarin nasa ke cewa, “Wadannan sune mambobi na sabuwar kungiyar ‘yanta’adda a Yankin Najeriya.”
Ya zuwa ranar 25 ga watan Yuli,2026 wannan bidiyo ya samu wadanda suka kalla 10,000 da wadanda suka nuna sha’awarsu 72 da masu tsokaci 50 da wadanda suka sake yada labarin 14.
Tsokaci da ake yi a dangane da wannan bidiyo ya sake nuna irin fargabar da al’umma ke da ita kan ayyukan ‘yanta’adda inda wasu ke kira ga gwamnati ta katse hanyoyi da suke samun abinci da makamai.
Sai dai a daya bangaren kuma wasu mutanen suna ta nasu martanin inda suke cewa wannan kungiya na da alaka da Sudan.
Adebimpe Margaret Ogunwumi tace, “Ya kamata gwamnati ta katse hanyar samun makamai da kayan abinci ga wadannan ‘yanta’adda.
Aliyu Xubairu yace “Kai ne shugabansu ko daga sansaninsu na Sudan zuwa na Najeriya.”
Shi kuwa Israel Adedeji yace “Ya kamata a tunkari wadannan ‘yanta’adda tun da gasu nan,Ya kamata mu karkatar da zuba jarinmu wajen samun makamai. Gwamnati ita kadai ba za ta iya wannan aiki ba, ya kamata al’umma ta farka.”
Wannan bidiyo an yada shi a wurare da dama kamar a nan da nan da nan da nan.
A Najeriya akwai kungiyoyi da dama na ‘yanta’adda a bangarori da dama na jihar, wasu daga cikin manyansu sun hadar da Boko Haram da Kungiyar mayakan IS da ke lardin Afurka ta Yamma (ISWAP) da ANSARU da wasu kungiyoyin da ke tasowa irin na Lakurawa, lamarin da ke kara tabarbara harkokin tsaro a kasar.
Amma da gaske ne akwai kungiyar ‘yanta’adda a Najeriya?
DUBAWA ta ga dacewar gudanar da binciken gano gaskiyar labarin, ganin cewa akwai alamu da ke nuna cewa zai iya kawo fargaba da yaudarar al’umma ta hanyar yin karya a alakanta wata kungiya da ke ayyukanta da wata kasa zuwa ayyukan ta’addanci a Najeriya.
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da bincike kan hoton ta hanyar amfani da Google inda ta gano cewa an fara wallafa wannan bidiyo a ranar 4 ga watan Yuni,2026 a wani shafin Facebook mai suna Naath Sky TV.
Wannan bidiyo an wallafa shi da taken “Viva SPLA-IO. Wadanan sune masu fafutukar neman ‘yanci a saki Dr Machar da dena kashe ‘yankabilar Nuer, nasara ga sojojin Viva”
DUBAWA ta gudanar da bincike ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi daga wallafar ciki kuwa har da “Viva SPLA-IO.”
Binciken da aka gudanar ya nunar da cewa SPLA-IO na nufin sojojin fafutukar ‘yantar da Sudan ta Kudu na (Sudan People’s Liberation Movement-In Opposition (SPLM-IO),wadanda ke zama masu fafutuka ta ganin an girka mulkin dimukuradiyya a karkashin jagorancin Riek Machar.
Su kuwa kalmomin “Viva SPLA-IO” wani take ne da ke nuna mika wuya da goyon baya ga masu wannan fafutuka.
DUBAWA ta kuma bincika don nemo bayanai a game da Dr. Machar sai ta gano cewa cikakken sunansa shine Dr Riek Machar Teny Dhurgon, dan siyasa a Sudan ta Kudu, tsohon jagoran adawa yayi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa na farko da aka dakatar a Sudan ta Kudu wanda yanzu yake fuskantar manyan tuhume-tuhume ciki kuwa har da zargin cin amanar kasa da aikata kisan gilla da aikata miyagun laifuka kan al’umma.
DUBAWA ta kuma binciki ma’anar kalmar “Nuer.” Bincikenmu kuma ya gano cewa Nuer wata kabila ce ta biyu mafi girma a Sudan ta Kudu, asalin aikinsu sun kasance makiyaya suna kiran kansu da suna Naath, suna kuma rayuwa a yanki kusa da kogin Nilu, suna rayuwa a kusa da kogin da ke da yawan shuke-shuke da yanki mai tsaka-tsakin yabanya.
Da DUBAWA ta duba wallafar da aka yi a shafin Naath Sky TV Facebook, mun lura cewa yana yada labarai ne da ci gaban da ake samu a Sudan ta Kudu.
Wannan bidiyo an kuma wallafa shi a shafin Facebook mai suna ‘Dr Riek Machar 4 Presidency da rubuta taken “Viva SPLA-IO” wadannan masu fafutukar neman ‘yanci ne, a saki Dr Machar haka kuma a dakatar da kisan mutane da basu ji ba basu gani ba ‘yan kabilar Nuer.Nasara na tare da Viva.’
DUBAWA ta kuma tuntubi danjarida da ke a Sudan ta Kudu mai suna Alhadi Hawari na kafar yada labaran Eye Radio, wanda ya tabbatar da cewa harshen da mutanen ke magana da shi na al’ummar Nuer ne, wanda ake amfani da shi a Sudan ta Kudu.
Yace ‘ wadannan mutane ‘yan kasar Sudan ta Kudu ne, suna kuma yin magana da harshen Nuer.”
Nuer, wanda ake kira Thok Naath, harshe ne da ake yawan amfani da shi cikin mutane daga miliyan daya zuwa miliyan biyu, wadanda ke zaune a Sudan ta Kudu, wanda ke zama harshen kabila ta biyu mafi girma a Sudan ta Kudu, wannan harshe akwai ma masu yinsa a wajen kasar kamar yammacin kasar Habasha.
Bincike ya gano cewa wadannan mutane ba sabbin mambobi na wata sabuwar kungiyar ‘yanta’adda ba ce a Najeriya, kamar yadda masu da’awar suka yi, maimakon haka wannan bidiyo ya nuna wasu mutane ne daga SPLA-IO daga Sudan ta Kudu.
A karshe
Da’awar cewa mutanen da aka gani a bidiyon mambobi ne na sabuwar kungiyar ‘yanta’adda a Najeriya karya ne. DUBAWA bincikenta ya nuna cewa asalin bidiyon ya fito ne daga Sudan ta Kudu
Kuma abubuwan da aka nuna na daidaikun mutane ne a da ke da alaka da masu fafutukar ‘yantar da Sudan na (Sudan People’s Liberation Army-In Opposition (SPLA-IO).
