|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: wani mai amfani da shafin Facebook na da’awar wai wasu mutane masu dammarar makaman da aka nuna cikin wani bidiyo ne ke da alhakin rashin tsaron da ake fama da shi a Najeriya.

Hukunci: Karya ce. Bidiyon na da alaka da rikicin Sudan ne. Ba mu sami wata hujjar da ta danganta rikicin da Najeriya ba bare harkokin ‘yan bindigan da ake fama da shi a yankin arewacin kasar.
Cikakken bayani
Bidiyoyin da ake zargin wai sun nuna ‘yan bindiga da sauran kungiyoyin maharan da ke tayar da zaune tsaye sun zama abin da ake gani kusan ko da yaushe a shafukan sada zumunta. Yawancin lokuta a kan ga wasu maza dauke da makamai, da wasu kuma wadanda ake ganin su ne abin ya shafa, yayin da wasu kuma sukan bayyana a sansanonin ajiye wadanda ake garkuwa da su kafin a sami kudin fansa da ma sakonnin da ake tura wa al’umma. Yayin da wadannan bidiyoyin ke cigaba da yaduwa, masu amfani da shafukan su kan yada su da da’awowi daban-daban dangane taken (yawancin lokuta hasashe) abin da suke nufi ba tare da sun fayyace gaskiyar abin da labari ko batun ke nufi ba, however, such posts can easily mislead the public.
Kwanan nan wani mai amfani da shafin Facebook, @Mc Ese Jomo, ya wallafa wani bidiyon da ya ke da’awar wai ya na nuna wadanda su ka addabi Najeriya.
Bidiyon mai tsawon dalilu 35 (wanda za ku iya gani a nan) ya rabu gida biyu. A gefen hagun wasu maza masu dammara suna daukar kansu hoto suna raira kasidu, yayin da gefen daman kuma ya nuna wani mutumi ya na bayani.
Mutumin da ke bayanin cewa ya yi, “‘Yan Najeriya, na fada mu ku cewa zan kawo fuskokinsu. Ku kalle su idan har ba ku san su ba. Su ne suka hana mu sakewa a Najeriya.”
Daga 21 ga watan Yulin, 2026, mutane sama da 647 sun sa alamar like, wasu 418 sun yi tsokaci, 126 sun raba, sa’anan 52 sun adana shi ta bookmark.
Mun duba wasu daga cikin tsokace-tsokacen da aka yi dan jin ra’ayoyin wadanda suka yi ma’amala da labarin
@Njabulo Mosia, alal misali cewa ya yi, “Mutane 12 kacal din da suka hana mutane sukuni a kasar baki daya.”
@Kgothatso Subzet ya amsa da cewa, “Abu daya da ya kamata a tambaya shi ne wane ne ke ba su kudin sayen irin wadannan kayyayakin aikin?”
@Ricardo Trevor, wanda tsokacinsa ya nuna ya na goyon bayan da’awar ya yi martani kamar haka, “‘yan bindigan na gudanar da aiki mai kyau.”
Wani mai amfani da shafin, @Nkanyeni Maenetja, wanda ya ce shi dan Afirka ta Kudu ne ya ce, “Abin da ya kamata ‘yan Najeriya su rika yaka ke nan ba ‘yan Afirka ta Kudu ba. Ku tsaya a gida ku yi yaki, Ubangiji zai taimake ku.
Duk da cewa mutumin da ya wallafa da’awar dan Najeriya ne, DUBAWA ta lura da cewa yawancin wadanda suka mayar da martani kan batun a matsayin ‘yan Afirka ta Kudu sun bukaci ‘yan Najeriya da su matar da hankali kan rashin tsaro a Najeriya a maimaikon cece-kuce kan ‘yan Najeriyan da ke barin Afirka ta Kudu.
Mun kuma sake ganin wani mai amfani da Facebook ya wallafa labarin a nan.
DUBAWA ta dauki nauyin tantance batun ganin yadda zai iya yaudarar al’umma.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da sa bidiyon cikin manhajar INVID na tantance bidiyoyi wadda ke taimakawa wajen cire mahimman hotunan da za’a iya amfani da su wajen gano asalin bidiyon. Bayan nan mun sa hotunan cikin google reverse image search, wanda ya kai mu ga ainihin bidiyon, wanda ma ya fi haske a shafin X. An wallafa labarin a shafin X ranar 3 ga watan Yulin 2026 kwana biyu kafin a sake wallafa bidiyon a Facebook wato ranar 5 gawatan Yulin 2026.
Labarin na X na dauke da taken, “Sudan: Mayakan da ke da alaka da dakarun sojojin Sudan (#SAF) sun wallafa sabon bidiyo daga filin daaga. Wannan rukunin na SAF da ma an san su da amfani da makami kirar #Iran -wato rokokin atilari na 107mm Fadjr-1 ( wadanda kamar ba da dadewan nan ba aka tura musu) da bindigogin yaki na AZ-7,62 wadanda ake kerawa a #Azerbaijan.”
DUBAWA ta gudanar da binciken mahimman kalmomi ta na amfani da taken dan ganin ko akwai kafafen yada labarai masu nagarta wadanda suka dauki labarin ko kuma ma dai akwai wata majiya ta musamman wadda ta dauki labarin a hukumance. Yayin da mu ka ga labarin a wasu shafukan sada zumunta (nan, nan, da nan), ba mu ga wani rahoto mai zaman kan shi wanda ya yi labarin batun ko ma ya bayar da wani nazari kan bidiyon ba.
To sai dai mun ga wani rahoto a shafin Middle East 24 wanda ke labarin sabon hadin kan sojoji tsakanin Sudan da Iran da kasashen biyu suka gyara dangantakarsu ta diflomasiyya a shekarar 2023. Rahoton ya nuna cewa makaman da Iran ke kerawa sun bayyana a hannun dakarun sojojin SUdan. Duk da cewa rahoton bai yi nazarin bidiyon da ake magana a kai ba, ya goyi bayan yanayin da aka wallafa bidiyon.
DUBAWA tta kwatanta rigunan da sojojin cikin bidiyon Facebook din suka sa da wanda dakarun sojojin SUdan suka sa. Wannan kwatancen ya nuna cewa salo da launin kayan iri daya ne abin da ke kara tabbatar mana da cewa wannan bidiyon ya fito Sudan ne ba Najeriya ba kamar yadda ake hasashe.

Kayan sojoji cikin bidiyon Facebook (hagu) Hotunan kayan sojojin ‘yan Sudan (dama).
Yayin da muke tantance batun DUBAWA ba ta sami hujjojin da suka danganta bidiyon da maharan da ke aikata ta’asa a Najeriya ba. Iyakaci dai hujjojin da suke nuna cewa batun ya faru a ne a Sudan.
A Karshe
DUBAWA ba ta sami wata sahihiyar hujjar da ke danganta bidiyon da harkokin ’yan bindiga ko rashin tsaro a Najeriya ba. Hujjojin da muka samu sun tabbatar cewa bidiyon na bayani ne kan rikicin Sudan kusan shekaru takwas da suka gabata. Dan haka wannan da’awar yaudara ce kawai.
