Labaran karya kan zaben 2027, harin ‘yan bindiga a Katsina, da sauran manyan da’awar da aka tantance a wannan makon

2027 election disinformation, Katsina bandit attacks, other top claims fact-checked this week
Getting your Trinity Audio player ready...

A wannan makon, fannin yada labarai ya fuskanci labarai na yaudara, da suka hada da amfani da fasahar kirkira ta AI domin rage ko karin gishiri kan labarin hare-hare, da kuma sake amfani da tsofaffin bidiyon zanga-zanga domin karkatar da ra’ayin al’umma.

Yayin da yakin neman zabe ke kara zafi gabanin babban zaben 2027, da’awa masu yaudarar mutane na ci gaba da yaduwa a kafafen sada zumunta.

Ga kadan daga cikin labaran da DUBAWA ta tantance a cikin makon da ya gabata:

  1. Masu amfani da kafafen sada zumunta na yada shafukan jaridu na bogi da aka ƙirƙira da fasahar AI gabanin zaben 2027

Gabanin babban zaben 2027, wasu shafukan magoya bayan jam’iyyu a X da Facebook sun yada shafukan farko na jaridu na jabu da ke kunshe da kalaman bogi da alkawurran manufofi da aka jingina wa ‘yan siyasa, ciki har da Shugaba Bola Tinubu da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar.

Wadannan labaran karya sun jingina kalaman ban mamaki da alkawurra ga manyan masu neman tsayawa takara. 

Binciken diddigin fasaha na DUBAWA ya gano cewa an ƙirƙiri shafukan ne ta hanyar amfani da manhajojin fasahar AI, tare da alamomin jam’iyyun siyasa da ba su dace ba da kuma sunayen wasu kafafe na jaridu da aka sani. Duba karin bayani a nan.

  1. Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya yi ikirarin cewa babu ‘yan bindiga a Jihar Sokoto

A yayin wani taro, Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya yi ikirarin cewa rahotannin ayyukan ‘yan bindiga a Jihar Sokoto ba gaskiya ba ne. Ya ce duk wanda ke ba da rahoton ayyukan ‘yan bindiga a jihar karya yake yi saboda ya yi tafiya lafiya kalau daga Sokoto zuwa Silame.

DUBAWA ta binciki bayanan tsaro kuma ta tabbatar da cewa ikirarin gwamnan yaudara ce. Yin tafiya lafiya a kan babbar hanya tare da rakiyar jami’an tsaro masu tsaron VIP dauke da manyan makamai ba ya nuna ainihin yanayin tsaro a fadin jihar gaba daya.

Karanta cikakken bincikenmu a nan.

  1. Wani mai amfani da Facebook ya yi ikirarin cewa sama da ‘yan bindiga 100 sun kai hari a wata al’umma a Katsina

Wani rubutu a Facebook daga wata kafar yanar gizo, Spy Nigeria, ya yi ikirarin cewa an ga ayarin babura sama da 100 dauke da ‘yan bindiga suna kai hari a Karamar Hukumar Funtua da ke Jihar Katsina.

DUBAWA ta gudanar da bincike ta hanyar ziyartar Funtua, inda ta zanta da shaidun gani da ido, da jami’an tsaron al’umma na Katsina Community Watch Corps, da kuma shugabancin ‘yan sanda na yankin. 

Binciken ya nuna cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan sandan kwantar da tarzoma suka kama wani mutum da ake zargi dan bindiga ne, lamarin da ya sa yan uwansa shida da suka zo a mota kirar Volkswagen Golf suka bude wuta a kokarin kubutar da shi.

Ga karin bayani a nan.

  1. Bidiyon da aka ƙirƙira da fasahar AI da aka gabatar a matsayin ‘yan ta’adda na shigowa Najeriya

Wani bidiyo a Facebook da ya yaɗu ya yi ikirarin nuna yadda ‘yan ta’adda na kasashen waje ke kutsa kai ta iyakokin Najeriya.

Binciken hotuna na intanet da tantance hotuna ta hanyar amfani da InVID sun bayyana cewa bidiyon ba na gaskiya ba ne. Maimakon haka, wani hadin hotuna ne da aka mai da bidiyo ta hanyar amfani da AI. Kafafen yada labarai sun wallafa hotunan tun a watan Maris na 2023 domin bayyana rahotannin tsaro na cikin gida.

Manhajojin gano kirkirar fasahar AI sun tabbatar da cewa bidiyon AI ne da aka kirkira daga tsofaffin hotuna.

  1. Ikirarin bidiyon wani yaro Bafulatani yana karɓar horo zai kashe Kiristocin Najeriya

Wani mai amfani da shafin X @VOLTOXf ya yada wani bidiyo yana zargin cewa ya nuna wani karamin yaron Bafulatani yana samun horon yadda zai kashe Kiristoci a Najeriya. Hoton ya nuna wani karamin yaro a zaune yana harbin bindiga a wani abin da aka kafa a kan bishiya.

Binciken sauti da hoto na DUBAWA ya gano cewa ikirarin yaudara ne. Binciken sautin ya nuna cewa manyan mutanen da ke ba yaron umarni suna magana ne da yaren Larabcin kasar Sudan (Sudanese Arabic) ba Fulfulde, Hausa, ko wani yaren da ake amfani da shi a Najeriya ba.

Duba sakamakon binciken a nan.

  1. Tsohon bidiyon 2024 da aka sake yadawa a matsayin mazauna Sokoto na neman Peter Obi ya maye gurbin Tinubu

Wani bidiyo da aka yada a Facebook ya yi ikirarin cewa mazauna Sokoto kwanan nan sun yi dandazo zuwa fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi suna neman Shugaba Bola Tinubu ya yi murabus sannan Peter Obi ya karbi mulki nan take.

DUBAWA ta gano cewa faifan bidiyon na zanga-zangar #EndBadGovernance ce da aka gudanar a fadin kasar a watan Agustan 2024, inda masu zanga-zangar suka kutsa fadar saboda tsadar rayuwa da yunwa, ba tare da wata alaka da Peter Obi ba.