|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi ikirarin cewa Jihar Sokoto tana da tsaro kuma duk wanda ke ikirarin cewa akwai ‘yan bindiga jihar karya ne, yana mai kafa hujja da yadda ya yi tafiya ba tare da wata matsala ba zuwa Silame.

Hukunci: Yaudara ce. Rahotanni sun nuna cewa ikirarin gwamnan bai yi daidai da ainihin hakikanin abin da ke faruwa a zahiri ba.
Cikakken Bayani
A yayin wata ziyarar aiki da ya kai Jihar Sokoto a ranar 2 ga Satumba, 2026, Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi wata magana a kan rahotannin da jama’a da kafafen yada labarai ke bayarwa game da rashin tsaro a jihar.
Da yake jawabi yayin kaddamar da gadar Silame da ayyukan hanyoyin karkara, Gwamna Sule ya bayyana cewa ya zabi tafiya nesa ne zuwa Karamar Hukumar Silame domin ganin abin da ya kira ƙarai-rayi na kafafen yada labarai da nufin tsoratar da masu son zuba jari.
Ya tabbatar da cewa duk da gargadin da aka yi masa na cewa ba zai iya bin hanyar ba tare da haduwa da ‘yan bindiga ba, ya yi tafiyar ba tare da wata matsala ba. Sule ya bayar da hujjar cewa rahotannin da ke nuna yaduwar ayyukan ‘yan bindiga a jihar ba gaskiya ba ne.
“Irin wadannan jita-jita marasa amfani da labaran ne ke tsoratar da masu son zuba jari daga kawo jarin su domin bunkasa jihohinmu da kasarmu, saboda ‘yan jarida sun yada karairayi a kanmu,” in ji Gwamna Sule.
Sai dai kuma, ya amince da cewa babu wata jiha a Najeriya da ta tsira daga kalubalen tsaro, yana mai jaddada bukatar shugabanni da ‘yan kasa su rika yada labarai masu kyau domin jawo bunkasar tattalin arziki.
Kalaman sun haifar da muhawara a tsakanin al’umma nan take, inda mazauna yankin suka nuna shakku kan kimantawar da gwamnan ya yi la’akari da hare-haren da aka kai kwanan nan a yankunan karkara.
Wani mai suna Bashir Jelani ya bukaci gwamnonin Nasarawa da Sokoto da su nemi afuwar al’ummar Sokoto saboda wannan kalami.
“Har yanzu na kasa fahimtar dalilin da zai sa gwamna ya yi amfani da tafiya guda daya a kan wata hanya domin ya ƙaryata irin halin da al’ummar Sokoto suka shiga na ta’addancin ‘yan bindiga. Abin da ya fi ba ni takaici ma shi ne martanin da Gwamnan Jihar Sokoto ya yi lokacin da yake jawabi,” in ji shi.
Dan takarar gwamnan Jihar Sokoto a karkashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Manir Muhammad Dan’iya, ya kalubalanci kalaman da aka danganta ga Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, kan halin tsaro a Jihar Sokoto.
Ya ce ya kamata a auna ingancin tsaro ne ta hanyar duba yadda mazauna yankin ke yin rayuwa cikin kwanciyar hankali, da zuwa gonakinsu, da kuma gudanar da ayyukansu na neman na halak.
Kasancewar kalaman jami’an gwamnati a kan harkar tsaro na da tasiri a kan ra’ayin jama’a da matakan da gwamnati ke dauka, DUBAWA ta binciki ikirarin Gwamna Sule idan aka kwatanta shi da bayanan tsaro da aka rubuta a Jihar Sokoto.
Tantancewa
Binciken faifan bidiyon da aka nada ya tabbatar da cewa Gwamna Sule ya yi wadannan kalaman.
A jawabinsa, ya bayyana cewa an gaya masa cewa matafiya ba za su iya tuka mota daga Sokoto zuwa Silame ba tare da sun fuskanci hare-haren ‘yan bindiga masu dauke da makamai ba. Ya dage cewa tun da ayarinsa ya bi hanyar lafiya kalau, ikirarin cewa akwai ‘yan bindiga a jihar ba gaskiya ba ne kuma ƙarya ce kawai.
Sai dai kuma, DUBAWA ta binciki rahotannin tsaro a fadin Jihar Sokoto domin tabbatar da ko rashin samun harin kwanton-bauna a kan hanya guda daya da aka bi tare da jami’an tsaro masu tsaron mutane na musamman (VIP) ya tabbatar da cewa babu ayyukan ‘yan bindiga a jihar.
Abin da hujjoji suka nuna
Bayanan tsaro da rahotannin kafafen yada labarai sun saba wa ikirarin cewa babu ‘yan bindiga a Jihar Sokoto.
A ranar 26 ga Agusta, 2026, ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a yankin Gorau da ke Karamar Hukumar Goronyo, harin da jaridar Vanguard ta ruwaito, inda aka kashe mazauna yankin hudu, wasu bakwai suka samu raunukan harbin bindiga, sannan aka yi garkuwa da wasu hudu ‘yan kwanaki kadan bayan wani mummunan hatsarin jirgin ruwa a wannan yankin.
A wannan rana, kamar yadda The Whistler da The Star suka ruwaito, sojoji sun fafata da ‘yan bindiga da suka yi yunkurin kutsa kai cikin garin Sifawa a Karamar Hukumar Bodinga—kimanin kilomita 25 daga birnin jihar—a wata musayar wuta da ta yi sanadiyyar raunata sojoji biyu kafin a fatattaki maharan.
Tashin hankalin ya ci gaba bayan ‘yan kwanaki a Karamar Hukumar Rabah, inda ‘yan bindiga suka yi wa manoma kwanton-bauna a gundumar Ghandi a ranar 31 ga Agusta, 2026.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa maharan sun bude wa ma’aikatan gona wuta, inda suka kashe manoma takwas tare da barin wasu biyar cikin mawuyacin hali a wani hari da Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sokoto ta tabbatar.
Bayan kai hare-hare kai tsaye, ‘yan bindiga sun ci gaba da sanya harajin kudi a kan al’ummomi; a ranar 2 ga Satumba, 2026, rahotanni sun bayyana yadda ake zargin ‘yan bindiga sun kakaba haraji naira miliyan 40 a kan mazauna garin Kebbe, abin da kakakin rundunar ‘yan sandan ya tabbatar wa DUBAWA.
Shin tafiya tare da rakiyar jami’an tsaro hujja ce Sokoto ba ta da rashin tsaro?
Tafiyar Gwamna Sule ta gudana ne a kan babbar hanya, kuma ya yi tafiyar ne a cikin ayarin motocin gwamna a hukumance tare da rakiyar jami’an tsaro masu dauke da makamai.
Yin tafiya lafiya da jami’an tsaro kan hanya guda daya ba zai zama hujjar cewa babu ‘yan bindiga a fadin jihar ba. Hare-haren da aka ruwaito, da neman kudin fansa, da kuma asarar rayuka a Goronyo, da Rabah, da Bodinga, da Kebbe na nuna cewa akwai ayyukan ‘yan bindiga a wasu sassan Jihar Sokoto.
A Ƙarshe
Yaudara ce, ikirarin Gwamna Abdullahi Sule na cewa rahotannin ayyukan ‘yan bindiga a Jihar Sokoto ƙarya ne. Duk da cewa gwamnan ya yi tafiya cikin kwanciyar hankali daga Sokoto zuwa Silame, rahotannin ‘yan sanda da dama da aka tantance, da alkaluman wadanda abin ya shafa, da bayanan sirri na jami’an tsaro sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga na ci gaba da gudanar da ayyukansu da kai hare-hare a yankuna da dama a Jihar Sokoto.
An gudanar da wannan aikin ne a karkashin kungiyar Centre for Journalism Innovation and Development (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai (EU).
