Manoma a jihar Kaduna na ci gaba da dakon aikin samar da gidajen gona da manufar samar da madara da aka yi watsi da shi; gwamnati ta gaza ba da amsa

A can baya watan Nuwamba, 2023 watanni kadan bayan da Gwamna Uba Sani na Kaduna ya hau karagar mulki, manyan jami’an gwamnati sun yi tururuwa (streamed) zuwa Arla Farms da ke kauyen Damau don ganin yadda aka kaddamar da bude katafaren aikin samar da madarar shanun da ya kafa tarihi. 

Shekara guda daga bisani wannan katafaren aikin gidajen gona ya bude kofarsa (threw its gates open) ga masu ruwa da tsaki kan samar da madarar shanun da suka hadar da manoma na cikin gida da kwararru a fannin ayyukan gona da dalibai masu nazari kan likitancin dabbobi da manyan jami’an gwamnati wadanda ke da sha’awa kan sha’anin da ya shafi kula da dabbobi da harkokin abincin dabbobi da yadda ake samar da madarar shanu a zamanance.

 Sai dai kuma a lokacin da DUBAWA ta kai ziyarar ganin wannan aiki mai fadin hekta 400 a watan Fabrairu,2025, wannan aiki ya sauka daga manufar da aka dora shi a kai, hanya daya tilo da za ta kai ga inda aka tanado wajen samar da madarar tana wani hali babu kwalta shuka baje ko’ina sai kukan shanu.

Kaduna farmers wait endlessly as N10bn dairy project abandoned; govt unable to provide answers

Hanya da za ta kaika gonar ta Arla dairy farm, wanda ya dauki hoto: Cole Praise/DUBAWA. 

“An gama da kudade, ina fada maka,” a cewar Abdulkareem Yahaya mazaunin garin na Damau yayin da yake bayani ga DUBAWA inda ya nunar da cewa da dama ayyukan ba a kammala su ba, saboda babu kudade, kamfanoni da dama da ya kamata su yi aikin gyaran hanya da magudanan ruwa sun kauracewa wuraren ayyukansu.

Yahaya ma na kara nuna damuwa ga abin da Happy Ustaaz (@Ussyy), ke fadi ne inda yace duk da makuden kudade da gwamnatin jihar Kaduna ta ranta miliyan dubu N10.5 gidajen gona 2o ne kawai aka samar daga cikin gidajen gona 1000 da aka yi alkawari.

DUBAWA ta kudiri aniya ta gudanar da bincike kan wannan da’awa a dangane da halin da wannan katafaren aikin samar da gidajen ayyukan gona yake ciki.

Katafaren aikin samar da madarar shanu na Damau da zai lashe miliyan dubu N10.5 

Har yanzu dai matsalar na nan yadda za ka ga makiyaya na lalata gonakin manoma ana asarar miliyoyin naira(millions of naira), abin da ke kara ta’azzara matsalar samar da isasshen abinci a Najeriya.

 A ranar 17 ga watan Janairu,2020 a lokacin Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, (inaugurated) ya kaddanmar da aikin kamfanin samar da madarar shanu na Damau da ke karamar hukumar Kubau jihar Kaduna, wannan kokari ne na gwamnati na rage radadi saboda irin matsalar da ake samu tsakanin makiyaya da manoma wanda yayi sanadi na rasa rayukan dubban mutane ( left tens of thousands dead) wasu daruruwan dubbai kuma suka kauracewa muhallansu a arewacin na Najeriya (hundreds of thousands displaced). Har yanzu dai ana jika inda ake ci gaba da samun makiyayan na ratsa gonakin manoma, abin da ke jawo masu asara ta miliyoyin dubbai na naira.

Aikin samar da gidajen gonar 1,000 a Damau, a kauyen da ke can nesa dabara ce ta gwamnatin jihar Kaduna a kokari na kawo karshen rikicin da ake samu tsakanin manoma da makiyaya, aikin da ya samun tallafi kamfanin samar da madara na Arla daga kasar Denmark da kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN).

A lokacin kaddamar da aikin (inauguration,) El Rufai ya bayyana cewa wannan aiki zai taimaka a kokari da ake yi na dakile matsaloli da ake samu masu alaka da matsalar ta makiyaya da ke kiwon dabbobi.

Haka shima kamfanin na Arla adopted ya karbi wannan tsari da ya kalla a matsayin wanda zai taimaka wa makiyaya su kara samun riba a harkokin da suke yi na samar da madarar shanu a Najeriya.

Manajan daraktan kamfanin na Arla Foods Nigeria, Peder Pederson, (described)  ya bayyana hadin gwiwar da suka yi a matsayin kasuwanci da zai samar da riba a kuma samu dorewar alaka da kamfanin na duniya.

Kaduna farmers wait endlessly as N10bn dairy project abandoned; govt unable to provide answers

Babbar kofar shiga kamfanin na Arla dairy farm wanda ake aikin ginawa tun a shekarar 2022, wanda ya dauki hoto: Cole Praise/DUBAWA

Tsohuwar manajar darakta a kamfanin da ke lura da harkokin kasuwanci a Kaduna (KMDMC), Tamar Nandul, a wata tattaunawa (interview) da jaridar Leadership ta taba fadawa jaridar yadda suke fatan ganin wannan kamfani ya zamo a nan gaba.   

Ta bayyana cewa za a raba katafaren kamfanin da ke zama katafaren gidan gona gida uku hekta 1,800 kowanne, inda kowanne za a samu rukunai 8 zuwa 9 kimanin hekta 200. Kowane lardi zai samu gonaki kanana 320 zuwa 360, akwai kuma karin hekta 600 da aka ware don noman rani.

Kimanin manoma 40 za a sama masu lardunansu, manomi da iyalansa a ware masa hekta 5 inda zai samu gidan gona da rumfar shanu da wajen rainon marakai, za a bashi rabin hekta na filin da zai gina gida da lambuna, raguwar hudu da rabin kuwa domin dan kiwon na dabbobi kowane manomi kuma za a bashi shanu na musamman na kasashen ketare da zai samar da madara da kiwon shanun.

Duk da cewa an dasa wannan aiki a can nesa da gari wanda babu ababen more rayuwa, gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa (said) za ta gina hanya mai tsawon kilomita 130 da fadin mita 10  da kwalbati 37 da gadoji guda biyu. Gwamnatin ta kuma yi alkawari na gina rumfuna da ake ajiye shanu 400 da wajen ajiye marakai da cibiyoyi biyu na koyon sana’a da cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko guda biyu da ginin azuzuwa biyu na makaranta da ginin rumfar kasuwa biyu da bandakuna shida da ofishin jami’an tsaro guda hudu.

Har ila yau a kashin farko na aikin, manoman yankin za su iya samun horo kan yadda ake samar da madarar shanu a zamanance. Kamfanin na Arla (constructed) ya samar da gonar gwaji mai fadin hekta 400 a filin gonar da aka samar. A wannan katafaren yanki na gidajen gona da ke zama kamfani za a samar da gidaje da zaa zuba shanun wanda za a sanya masu na’ura da ke kula da yanayin zafi ko sanyi da gidaje da aka samawa ma’aiakatan gonar da wajen samar da abincin dabbobin da rumbun ajiyar kayan abincinsu da tsarin noman rani da wajen tatsar madarar shanu. 

Da fari Arla ya zuba jarin kimanin miliyan $14 na dalar Amurka a wannan katafariyar gona inda anan gaba yake fatan zuba jarin dala miliyan $25 wanda za a yi amfani da su wajen samar da sashin sarrafa madarar da kafa cibiyar karbar madarar shanun.

Manoma sun shiga rudani yayin da gwamnati taki mayar da hankali a aikin samar da madarar shanun.

A wata rana a watan Fabrairu,2025, samaniya cike da hadari a garin da a tsawon sama da shekaru 20 basu da hasken lantarki, idan ka ga hasken wuta wasu tsirarun gidaje ne da suke samun wutarsu daga hasken rana. 

Yanayin garin da ka kalla za ka ga tsofaffi na yawo a kekuna da ke zama abin sufuri a gare su haka za ka ga yara dauke da bokiti suna dauko ruwa daga babbar rijiya zuwa gidajensu.

Wani mazaunin yankin Danladi Bello (wanda ba shine asaklin sunansa ba, ya yi haka ne don gudun tozartawa), ya fadawa DUBAWA cewa gwamnatin El Rufai taso al’ummar da ke yankin na Damau su fara amfana da wannan aikin katafaren gidan gona kasancewar an kafa shi a garinsu.

Nandul ta fada wa Leadership cewa manoma 1000 za su amfana da wannan aiki wadanda za a zakulo su daga garuruwa 10 daga jihar Kaduna wadanda suka hadar da Anchau da Ikara da Makarfi da Hunkuyi da Soba da  Zaria da Sabon Gari da Lere da Kauru da Damau.  

Mutanen Damau akasari Fulani ne makiyaya da kaddamar da wannan aiki ya sanya dole su tafi kiwo kasancewar wurin kiwon nasu yayi kadan su ciyar da shanunsu. Wasu iyalan ya zame masu dole su rika fita kiwo da dabbobinsu daga wuri zuwa wuri don ciyar da su.Wasu kuma na tafiya da dabbobin nasu saboda matsalar fashin daji inda ake masu satar shanu matsalar da ta dauki shekaru masu yawa na addabar makiyayan a arewacin Najeriya.

Kaduna farmers wait endlessly as N10bn dairy project abandoned; govt unable to provide answers

Kauyen Damau. Wanda ya dauki hoto: Cole Praise/DUBAWA

.

Danladi ya fada wa DUBAWA  cewa da shugabannin aikin suka zo Damau, sun nemi bayanai ne a wajen al’umma suka tattara, sannan suka tambaya ko mutane na da sha’awa na kiwon shanu don samun madara, wannan shine abu na farko da aka fara yi da al’ummar garin. A lokacin da suka dawo kuma sai suka zo da jerin sunaye 400. Wannan shine jerin sunaye na mutane da aka ware za su shiga tsarin, daga nan aka rarraba su zuwa rukunai 10, kowane rukuni na da mambobi 40. Da fari babu tsari na shugabanci a cewar Danladi.

Kowane rukuni ba da wani bata lokaci ba sai ya zama kungiyar taimakon juna wacce ke da bukatar shugabanci, kungiyar taimakon juna ta Kaduna State Cooperative Society ita ta sanya idanu a tsarin zaben, wanda ke da sha’awar shugabanci sai ya bada sunansa ko sunanta, yayin da sauran mambobi suka zabe su.

Idan wata matsala ta taso a kowace kungiya kowacce sai ta tura shugabanta su tattauna a matakin koli na “Apex body.” Wannan kungiya ce ke tattaunawa da masu aikin samar da wannan katafaren gidan gona ko kamfaniwanda su kuma suke mayar da bayanan da suka samu zuwa mambobin kungiyar.

Ko da yake ba duka mambobin kungiyoyin taimakon junan ke zama masu kiwon dabbobi ba kasancewar wasu daga cikinsu manoma ne amma duka an basu horo kan kiwo don samun madara a zamanance. A cewar Danladi har kawo wannan lokaci basa amfani da ilimin da suka koya a yayin taron karawa juna sanin, ya kara da cewa kamfanin na Arla da ke dan asalin kasar Denmark shi ya samar da horo ga makiyayan kan yadda ake tatsar nonon shanu da yadda ake alkinta shi dama yadda ake siyarwa.

Haka kuma wadanda suka samu horon basu sami shanun na kasashen waje ba, da za su yi amfani da su wajen samar da madarar, Danladi ya kara da cewa shanu da ake da su na cikin gida abin da suke iya samarwa a rana shine lita daya a duk rana sabanin shanun kasar ta Denmark da za su iya samar da madara tsakanin lita 20 zuwa lita 25 a duk rana.” 

“Shanun ba a kawo su ba har yanzu,su na zamani ne saniya tamu ta nan gida tana iya samar da lita daya ne na madara a duk rana . Wadanda aka bamu horo a kai kuwa za su iya samar da lita ta madara daga lita 20 zuwa lita 25 ko sama da haka a duk rana.”Kamar yadda Danladi ya bayyanawa DUBAWA.

Kaduna farmers wait endlessly as N10bn dairy project abandoned; govt unable to provide answers

 A wata gona a Damau. Wanda ya dauki hoto: Cole Praise/DUBAWA.

Yana mai ra’ayin cewa sauyin gwamnati da aka samu daga El-Rufa’i da Gwamnan Kaduna na yanzu Uba Sani shi ya jawo tsaikon a aikin. Yace gwamnatin yanzu ta so ta ci gaba da wannan aiki duk da matsalar da aka samu da gwamnatin da ta gabata.

Kaduna farmers wait endlessly as N10bn dairy project abandoned; govt unable to provide answers

Gada da ta hada hanyar zuwa garin. Wanda ya dauki hoto: Cole Praise/DUBAWA.

Gwamnatin jihar Kaduna mai ci ta nada Ibrahim Lazuru a matsayin sabon shugaban kamfanin da ke lura da harkokin kasuwanni (KMDMC), sai dai wadanda suka ci moriyar shirin ba su da kyakkyawar alaka da sabon shugaban, ya bayyana a lokacin da ya gana da su cewa zai karasa aikin, amma abin ya tsaya ga alkawari, ko da yake manajan daraktan yayi alkawari zai sama masu da shanu da rumfunan shanun da gonaki Danladi ya fada wa DUBAWA bai san dalili ba wadannan alkawura na ci gaba da samun tsaiko.

Yana bukatar bayani me ya sanya gwamnati ta gaza cika alkawuran, amma yafi damuwa kasancewar shi ko wani mai kiwo sun gaza fahimtar mai yasa gwamnatin ke tafiyar hawainiya, wannan zai iya shafar alakarmu ko ma makiyayan su gaza samun cika alkawarin da aka yi masu na samar da wannan katafaren kamfani da ke zama gidan gona wanda shi suke bukata.

Don haka shi ko waninsa babu abin da ya rage masu face su zama masu hakuri. Ya fada wa DUBAWA cewa mazauna kauyikan sun ga irin wadannan nakasu da ya sanya basu iya komai sai mika wuya ga gwamnati, babu abin da za su iya. Wannan ya nuna cewa gwamnati ta fitar da tsare-tsaren, a lokaci guda kuma taki aiwatarwa ba tare da ba da wani dalili ba. 

“ Yanzu mun zama kamar almajirai , shi almajiri ba shi da zabi, ba za mu iya yi ba (aikin samar da madarar na zamani) da kanmu. Ba zamu iya daukar nauyin aikin da kanmu ba. Gwamnati ce ke da iko na iya tafiyar da lamura.” kamar yadda Danladi ya nunar.

Dan asalin kauyen na Damau bai boye tunaninsa ba ga aikin, ba shi da tacewa kan wannan aiki da ya tsaya cak, ya gaza fahimta matsalar daga gwamnati ce ko daga kamfani ko dankwangila  ko kamfanin na KMDMC.  

Kaduna farmers wait endlessly as N10bn dairy project abandoned; govt unable to provide answers

Gidaje da aka yi wa wadanda suka samu horo alkawari sun kasance ba kammalallu ba, Wanda ya dauki hoto: Cole Praise/DUBAWA.

Yace abin da ya ragewa al’ummar wannan kauye suke rayuwa da shi shine noman da suke don samun abinci a kusan kowane gida da ke kauyen.

Duk da cewa abu ne sananne kowane mutum a kauyen a iyalansa za ka ga suna da gona da suke noma don samun abincin da suke amfani da shi amma ba wani babban noma bane da zai iya rike gidajen su ci abinci sau uku a kowace rana ko su yi amfani da shi don samun kudade da za su yi wani aiki, kawai taimako ne don ci gaba da rayuwa.

Amma a fadar Danladi idan gwamnati za ta yi masu abubuwan da ta yi alkawari za su iya kawar da mtsalolinsu na rayuwa. Mazauna kauyen za su iya samun kudade da za su sayi abin da suke so daga ribar madarar da za su rika fitarwa.

Wani da shi ma ya samu horon Sabiu Damau, ya fada wa DUBAWA cewa an dauki tsawon shekaru hudu inda anan kamar sauran wadanda suka amfana da wannan aiki ya samu horo a fannin noma don samawa shanun abinci. 

“Sun koya mana yadda ake ciyar da shanu da yadda ake samar da abincinsu da yadda ake lura da su. ” A cewar Sabiu. 

Sabiu, wanda sakatare ne na kungiyar taimakon juna tasu ya fada wa DUBAWA cewa duk wadanda suka samu horon sun samu ilimi na dabarun yadda ake kiwon shanu don samun madara da yadda ake tatsa da tafasawa, ya kara da cewa wannan shiri yayi mana alkawari na samar da gidaje da dabbobi da makarantu don yaranmu da kasuwa don dorewar harkokin kasuwancinmu.

Har yanzu Sabiu da sauran mambobi 40 na kungiyar taimakon junansu basu samu cika alkawari na gidajen da aka ce an sama masu ba, 

Sakataren kungiyar taimakon junan ya fada wa DUBAWA cewa duk da yake gwamnati ta fara aikin gina wadannan gidaje 200 an barsu ba tare da karasawa ba, babu wani manomi da zai rayu a cikin gini wanda ba a karasa ba, sun gwammace su ci gaba da rayuwa a yankin nasu da bashi da ci gaba.

Kaduna farmers wait endlessly as N10bn dairy project abandoned; govt unable to provide answers

Gida da ba a kammala ba. Wanda ya dauki hoto: Cole Praise/DUBAWA.

“Mun ga gidaje amma gidajen ba a kammala su ba, tuni suka fara gina gidajen 200 amma ba a kammala su ba.” kamar yadda Sabiu ya fada wa DUBAWA.

Lokacin da DUBAWA ta ziyarci rukunin gidajen da ake tanadi akwai gidaje kimanin 30 wadanda ba a kammala su ba , babu asibitin dabbobi, babu makaranta, babu rumfar ajiyar shanu, babu ofishin jami’an tsaro, babu makewayi. Ba kawai gidajen kwana suke dakon jira ba ballantana ayi maganar lokacin da za a mika masu makulli na shagunan da aka yi masu alkawari. Duk da haka mazauna kauyen sun yi rumfuna  irin na mazauna karkara inda suke siyar da abubuwan da suka samar.

Kaduna farmers wait endlessly as N10bn dairy project abandoned; govt unable to provide answers

Tun shekarar 2022, gwamnati ke ci gaba da ba wa mazauna kauyan tabbaci cewa za su samar masu da hektoci na fadin kasa da wutar lantarki da asibitoci da makarantu da cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko da ginin kasuwa da sauransu. 

Yayin da wadanda suka samu horon ke jira a basu abubuwan da aka yi masu alkawari karkashin wannan shiri na samar da gidajen gonakin sai kawai a ka bige da basu kudaden kalilan a lokacin da ake ba su horon kiwon shanun don samar da madara. 

“Shekaru uku kenan kullum sai fada mana ake suna hanya za su zo su bamu kaza, amma har yanzu babu abin da yazo hannunmu, sai kawai su gayyace mu wurin ba da horo in an kammala a bamu kayan marmari, ina tunani sau daya ne kawai aka bamu  N10,000, a cewar Sabiu a bayaninsa ga DUBAWA.

Tsawon wannan lokaci jagororin shirin sun shirya taron bita sau biyar ne, sau tari suna tattaunawa ne da wakilan kungiyoyin taimakon juna, Sabiu ya kara da cewa duk abinda bangaren kamfanin daga Denmark ke son tattaunawa da wadanda suka samu horon ya kan kira su su je Legas ne anan suke tattaunawa.

Babban abin da ake tattaunawa a yayin taron shine, yadda mutanen kauyan za su amfana da abubuwan da aka tanadar masu amma har kawo yanzu babu wani abun azo a gani,  Abin da jagororin kungiyar taimakon junan suke fadawa mazauna kauyen ko mambobinsu shine babu shakka za a ci gaba da wannan aiki. 

Amma wannan aiki ya tsaya ne a wani kadami lokacin da aka samu sauyin gwamnati a 2023. Lokacin da Gwamna El-Rufa’i ya kammala gwamnatinsa ya mika ga magajinsa Gwamna Uba Sani wanda takaddamar siyasa tsakaninsu taki karewa har kawo wannan lokaci. 

A farkon 2025 El-Rufa’i ya zargi Gwamna Sani da karkatar da kudaden kananan hukumomi zuwa Birtaniya (siphoning local government funds to the United Kingdom (UK).Sabiu yace an fada masu cewa kada su damu lokacin da shirin ya tsaya, kasancewar matakin da ake ba zai jima ba, kuma ba zai shafe su ba, an ce masu tsayawar da ta zo ba tsammani na da alaka da jihar ne, sai dai babu wani cikakken bayani kan me ke faruwa.

Kaduna farmers wait endlessly as N10bn dairy project abandoned; govt unable to provide answers

 Aikin gada da aka yi watsi da shi, hanyar da ke samar da ruwa zuwa gidajen gonakin. Me hoto: Cole Praise/DUBAWA.

“Aikin ya tsaya. Sun fada mana cewar mu kwantar da hankulanmu, kada mu damu, aikin zai ci gaba, amma akwai wasu abubuwa da ya kamata a warware da jihar.,” kamar yadda Sabiu ya bayyana.

Kazalika baya ga cewa wadanda za su amfana da wannan tsarin a Damau basu samu abin da ya dace ba, yanayin aikin da aka dauki shekaru uku bai yi saurin da ya dace ba, DUBAWA ta lura cewa tawagar masu kula da aikin ta mayar da hankali ne kan al’ummar kauyen na Damau, duk mutane da aka jawo a cikin sshirin na da alaka da Damau ba tare da wani daga cikin sauran larduna tara ba.Daga cikin mutane 1000 da gwamnati ta tsara za su shiga cikin ba da horon, 400  ne kawai aka shigar da su a tsarin.

Martanin Arla, kamfanin bai fara aiki ba saboda shigar gwamnati 

DUBAWA ta tuntubi Arla ta hanyar ta hanyar manajojin shirin, Funmi Oduntan. ta fada wa DUBAWA cewa alaka tsakanin kamfanin na Arla da manoma a yankin na Damau alaka ce ta cudeni in cude-ka. Sai dai kuma gwamnatin jihar Kaduna ta riga ta ajiye manoman a wadannan gonaki kafin ma Arla ta fara hulda da su don koya masu yadda ake aikin samar da madarar shanu a zamanance. 

Mun samu bayanai cewa da zarar an daidaita da manoman, za a  basu dama su shiga su samu sani kan yadda ake kiwon na zamani, za a koya masu yadda ake amfani da abubuwan da ake samu daga shanu, su san yadda za su rike kansu ta hanyar madarar shanun, su san yadda za a samu madara mai yawa da ribar da za a iya samu, Arla shine kamfanin da zai sayi madarar da sukan samar. Wannan na nufin wadanda suka samu horon za su kulla yarjejeniya da kamfanin kan yadda za su siyar masa abin da suka samar a wani farashi da suka amince.

Duk da cewa an samu nakasu daga bangaren gwamnati wajen samar da gidajen ga makiyayan Oduntan ta fadawa DUBAWA cewa yanzu haka kamfanin na Arla na samar da horo ga makiyayan. Ta hanyar aiki da wasu kungiyoyi na cikin gida da suka hadar da Milk Valued Chain Association, Arla na amfani da ma’aikata da ke shiga daji wadanda ke samar da ilimi kan yadda ake samar da madarar shanu a zamanance.

Duk da cewa manoman basu cika samu n dama ba ta ganin yadda Arla ke tatsar madarar daga shanu samfurin (Holstein cows) kafin a mayar da ita yadda mutane za su iya amfani da ita, ana zuwa gonar a wasu ranaku, a irin wadannan ranaku ne da bakasafai  aka cika samu ba suke koya masu ganin yadda kamfanin dan asalin Denmark ke iya tatsar nonon shanun da yadda ake gyara shi.

Haka kuma kasancewar makiyayan basu sami shanu na kasashen waje da za su yi amfani da su ba, kamar yadda gwamnatin jihar ta yi masu alkawari a farkon fara wannan aiki, abin  da ya rage masu shine amfani da shanun da suke da su na gida su gwada irin ilimin dabarun samar da madarar na zamani da suka koya.

“Don haka ba abu ba ne na samun ilimi a takarda kawai za a kuma ga ilimin a aikace. Yayin da suke koya suna gwadawa a aikace ta hanyar amfani da shanun da sike da su a kasa” ta fada wa DUBAWA.

Ka duba su kansu makiyayan ko manoman basa iya siyar da madarar don ci gaba da rayuwarsu, saboda aikin kamfanin bai fara ba, sannan idan gwamnati ta basu mazauni a gidajen da aka samar da aikin samar da madarar za su rika siyarwa ne kawai ga Arla. 

Yarjejeniyar da aka kulla ita ce yayin da Arla za ta dauki nauyin samar da abubuwan da ake bukata da ma samar masu da horo, su kuma manoma a nasu bangare manoman za su siyar da madarar ga kamfanin ne na Arla. DUBAWA ta fahimci cewa wasu manoman sun kulla yarjejeniya da Arla yayin da wasu kuma za su yi a nan gaba da zarar an samar masu mazauni a katafaren aikin samar da gidan gonar.  

Oduntan ta bayyana cewa sai an kammala gina ginin gidajen da dasa ciyawar da dabbobinsu za su ci sannan ne za a nemi su koma gidajen.

“Saboda gwamnatin Kaduna ita za ta ba da mazaunin ga manoman da iyalansu sai an samar da gidajen , an dasa ciyawar da suke bukata , aikin ne da ke tafiya, ba a kammala ba har kawo yanzu.” kamar yadda ta fadawa DUBAWA.

Gwamnatin Kaduna ba ta ce komai ba a dangane da dakatar da aikin 

DUBAWA ta tuntubi mai magana da yawun gwamnatin jihar Kaduna Ibrahim Musa kan batun samar da rumfunan da za a ajiye shanun, babban jami’in gwamnatin wanda ya fada mana da fari cewa ba a dade da bashi mukami ba, bai san komai ba a game da wannan aiki , ya yi alkawari cewa zai tuntubi jami’an da ya dace don karin bayani a dangane da batun.

“Kamar yadda na fada maka, ni sabo ne anan, zan tuntubi wani a gwamnatin da ta gabata da za ku iya tambaya saboda wannan aiki na karkashin kamfani ne da ke lura da harkokin kasuwanni, zan nemi bayani kan abin da ake ciki zan kuma yi maku bayani,” kamar yadda Ibrahim ya fada wa DUBAWA. Bai dai yi bayanin ba har lokacin wallafa wannan labari.

DUBAWA ta tuntubi mashawarci na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa a tsohuwar gwamnatin ta Kaduna Olumuyiwa Adekeye, a dangane da aikin, amma babu wata amsa da ya bayar bayan mika masa tambayoyi a dangane da aikin.

Har ila yau DUBAWA  ta bukaci karin bayani daga ma’aikatar harkokin kudade don jin bayani kan kudade da aka ware da wanda aka kashe a wannan aiki na samar da madarar shanun, nan ma babu wata cikakkiyar amsa daga ma’aikatar duk da cewa an nemi bayanin watanni biyu da suka gabata. 

Rashin katabus daga gwamnati ya hana manoma amfana daga aikin na Damau

A lokacin da DUBAWA ta kai ziyara a karamar hukumar Lere a yankun kudancin Kaduna, daya daga cikin kananan hukumomi da aka tsara za ta amfana da wannan aiki, mun tunkari Adamu Maigari mai kiwon dabbobi, ya fada mana cewa ya fara kiwon dabbobi tun a shekarar 2019 sai ya siyar da su idan sun girma. Ga Adamu da wasu irinsa bude irin wannan kamfani ko katafaren gidan gona dama ce a gare su da za su samu hanyar ciyar da dabbobinsu a hanya mai dorewa.

“A bangaren shanun da muke tatsar nononsu muna daukarsu mu shiga daji da safe da yamma mu koma gida,” a bayaninsa ga DUBAWA.

Adamu ya kara da cewa gwamnatin karamar hukuma ta amince mu fita kiwo, kuma masu gonaki ma basa kyararmu musamman idan an kammala kwashe amfanin gona, suna bari shanun su ci ciyawa da karmami, sai dai a cewar Adamu duk da fahimta da ke tsakanin manoman da makiyaya a wasu lokutan ana samun tashin hankali kamar yadda Adamu ya fadawa DUBAWA.

Da DUBAWA ta tambayi mai kiwon dabbobin a Lere ko yana da masaniya kan aikin katafaren gidan gonar ko kamfanin samar da masarar shanun na Damau sai yace bai sani ba, 

“Na fada maku cewa ni bani da masaniya kan aikin gidan gonar tatsar madarar shanun na Damau akwai masu kiwon shanu da dama wadanda basu san da wannan aiki ba.A cewar Adamu.

Haka lamarin yake a karamar hukumar Sabon Gari  a jihar ta Kaduna inda makiyayan da aka tsara su amfana da wannan tsari ba su ma san da zamansa ba.

Exit mobile version