Me ya sa mata ba su cin naman ‘yan gwailon dabbobi, kuma shin ya na hana haihuwa?

A kwanan nan ne al’ummar musulmi a fadin duniya suka gudanar da ibadar sallar layya, wadda ake yanka dabbobin ni’ima irinsu rago, bunsuru, tunkiya, shanu, da dai sauransu domin sadaukarwa da neman kusanci ga Allah.

‘Ya ‘yan maraina ko kuma gwailo, wani bangare ne na jikin dabbobi da ke da muhimmancin wajen haihuwa ga namiji. Wadannan halittun masu siffar koko, aikinsu shine samar da maniyyi wanda haɓaka halayen namiji da aikin haihuwa. 

Duk da cewa wasu mutanen ba sa cin wannan naman saboda ra’ayin kansu, da yawa na cin wannan naman.

Ba sabon abu bane cewa, a mafi yawan gidajen Hausawa ana bai wa maza wannan naman yayin da mata ke kaurace masa.

Sai dai wasu bayanai da ba na gaskiya ba sun yi ta karade shafukan sada zumunta dangane da amfani da kuma illar cin wani bangare na naman dabbobin yake da shi. Misalin wannan shine wani ikirari da wani mai amfani da shafin Facebook ya wallafa cea cin naman ‘ya’yan gwailo yana hana mace gamsuwa a yayin mu’amalar aure.

Wasu labaran kuma da ke yawo a cikin gari kuwa na cewa wannan naman yana hana mata daukar ciki ya hana su haihuwa.

Labaran shaci-fadi ke sauya tunanin mutane har su yarda da duk abin suka ga an jima an yinsa, hakan ne ya sa DUBAWA yin bincike domin gano gaskiyar wadannan labaran da ake yadawa.

Hana mace gamsuwa yayin saduwa?

A wannan lokacin da mafi yawan batutuwan da suka shafi jima’i da haihuwa suke daukar hankalin al’umma, duk wani bayani kan abinci da zai iya hana gamsuwa zai dauki hankalin al’umma da dama.

To sai dai bincike DUBAWA bai samu wani bincike na kimiyya ko da ke nuna cewa cin naman ‘ya’yan gwailo yana hana mace gamsuwa.

Wannan ne ya sa muka tuntubi kwararriya kuma likita kan lafiyar mata a asibitin koyarwa ta jami’ar Usman Danfodio Sokoto, Aisha Ibrahim, ta ce wannan ba gaskiya ba ne, “don mace ta ci naman gwailo na rago, bunsuru ko maraki, ba zai hanata jin dadi ba a lokacin saduwa, sai dai idan wata matsalar ce daban”.

Shin cin naman ‘ya’yan gwailo na hana mace haihuwa?

Kwararriya Aisha Ibrahim ta ce babu wani binciken kimiyya da ya nuna cewa idan mace ta ci naman yana hanata haihuwa, kuma har yanzu ba a ji irin wannan ta faru ba ko a kasashen waje.

“Wadannan ‘ya’yan gwailo ba magani ba ne, ko tsirrai da za a ce idan an ci zai haifar da wani abu a cikin mahaifar mace, nama ne dai kamar sauran naman dabba, saboda haka labarin karya ne ba gaskiya ba” a cewarta.

Aisha Ibrahim ta kara da cewa “kowa ya san haduwar kwai na mace da maniyyin namiji ke sanadiyar samun ciki, saboda haka mutane su daina yarda da irin wadannan bayanan da ke yawo a kafafen sada zumunta.”

Dalilin da ya sa mata ba sa cin naman gwailo

DUBAWA ta yi irin wannan tambayar ga malama a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, Dr Safiya Sambo Gidadawa, wadda ta ce wannan bai rasa nasaba da dabi’ar kunya da aka san malam bahaushe da ita.

Ta bayyana cewa ba mata ba kawai, har da maza akwai wadanda ba sa cin wannan naman sai dai a bai wa yara su ci.

“Tun asali an san al’ummar kasar Hausa/Fulani da kunya, kuma ‘yan gwailo al’aura ce ta dabbobi wadda abokan zamanmu maza suke da irinsa, akwai nauyi sosai ga mace a ganta tana cin wannan naman a bayyane ko a boye” In ji Dr Safiyya.

Exit mobile version