|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Duk shekara ranar 4 ga Fabrairu rana ce ta cutar Kansa ta duniya: Ana Fadakar da al’ummar duniya karkashin Kungiyar kasa da kasa mai yaki da cutar Kansa (UICC) don karfafa matakan kariya da gano cutar Kansa da wuri da tallafa wa mutane da ke fama da cutar Kansa. A wannan rana, ana jaddada mahimmancin fahimtar cutar Kansa da kuma yaki da jita-jita da ke yawo a cikin al’umma. Wannan yana mai da hankali ga cutar Kansa.
Taken ranar cutar a tsakanin 2025–2027 shine “Haduwa don abu na musamman” kira kan al’umma ba kawai cuta ba, a cibiyar lura da cutar Kansa. Ta ba da haske cewa cutar Kansa kalubale ne na duniya. Ya daidaikun mutane da ke fama da cutar Kansa, suna fuskantar maganin cutar tare da la’akari da yanayi na zamantakewa da tattalin arziki.
Cutar Kansa ta zama babban batu a tsakanin al’ummomi da hukumomi.
Cutar Kansa na daya daga cikin manyan kalubale a duniya, tare da tasirin da ke shafar miliyoyin mutane.
Wannan na nufin cewa kulawa da ilimi game da cutar Kansa yana da matukar muhimmanci.
Wannan yana nuna cewa cutar Kansa na da mahimmanci a cikin al’umma, kuma yana bukatar kulawa ta musamman.
Cutar Kansa na bukatar hadin kai daga kowa don inganta fahimtar cutar Kansa da kuma magance jita-jita da ke yawo a cikin al’umma. Wannan hadin kai na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da cewa mutane suna samun ingantacciyar kulawa da jinya, musamman masu fama da cutar Kansa. A gaskiya, cutar Kansa na bukatar kulawa ta musamman a kowane mataki.
A Najeriya, wadannan abubuwa da ke a zahiri an cukurkuda su da jita-jita da labaran karya a dangane da cutar Kansa, tun daga sakonnin shafukan WhatsApp zuwa labaran da ake yadawa a kan titi da labaran shafukan sada zumunta. Labaran karya na sauya tunanin al’umma a dangane da cutuka, suna hana mutane suje a yi masu gwaji da wuri da yin maganin cutar Kansa da wuri.
A wannan makala, DUBAWA ta fayyace wasu rade-radi a dangane da cutar ta kansa ta yadda mutane za su dauki mataki na rayuwarsu.
- Kansa jifa ne ko yin azaba
Kansa a wasu lokutan ana bayyanata a matsiyin tsinuwa ko maita ko yin azaba saboda wani abu da aka aikata, musamman idan tana cin jikin mutum cikin sauri ko ta rika dawowa bayan an yi magani ko kuma taki jin magani.
A cikin al’umma da dama, cutittika da ba a iya maganinsu ana bayyanasu da cewa jifa ne ko asiri musamman idan mutum da fari ana ganinsa kalau kafin ya fara cutar.
Cutar kansa yayin da kwayoyim halitta ke girma da hayayyafa ba tsayawa wannan na faruwa ne saboda kwayoyin halita na samun sauyi a kwayoyin halittar gado na DNA abin da ke shafar yadda suke girma, su gyara kansu ko su mutu. Irin wannan sauyin halitta ba yana faruwa ba ne dalilin jifa ko asiri ba ne, wannan na faru ne dalilin wasu abubuwa da suka shafi lafiya da dalilai na muhalli.
Kansa ta yiwu aga ta faru “ba zato ba tsammani” saboda sau tari tana girma ne sannu a hankali tsawon shekaru kafin alamun su fara bayyana, A lokacin da aka fara ganin alamu tana yiwuwa abin ya riga yayi nisa, lamarin da ke sanyawa a rika ganin cewa cutar ta gagara ayi mata maganin dalilin da yake sawa mutane su ce asiri ne ko jifa.
Sai dai dalilai na kiwon lafiya sun ba da sheda cewa gano cutar da wuri da daukar matakai akan lokaci wannan na taimakawa a kokari na magance cutar.
- Yanke wurin da ke da cutar kansa na jawo yaduwarta
Wasu mutanen sun yi amanna cewa yanke wurin da ke da cutar kansa a jikin mutum na jawo yaduwar cutar a wasu sassa na jiki, wannan fargaba kan sanya marasa lafiya su rika jan kafa wajen zuwa neman magani ko su bari a duba ciwon da ke damunsu, abin da ke haifar da matsala babba.
Cutar kansa na bazuwa idan kwayar halittar da ke da matsala ta balle daga inda matsalar take sai ta bi jini ta tafi wani bangare na jiki, wannan tsari shi ake kira da suna metastasis a kimiyance, abin da ke faruwa a tsarin halitta lokacin da cutar ke ci gaba da girmama. Ba wata hanyar kula da lafiya ke kawo shi ba.
A kwai wani tsari mai suna biopsy wannan hanya ce da jami’an lafiya ke yankar wani bangare na jiki don aiwatar da gwaje-gwaje a gano ko akwai cutar kansa a tabbatar.Fida kuwa ta hadar da cire inda ake ganin cutar baki daya ko wani bangare, dukkanin wadannan kwararren likita ne ke yi ta hanyar amfani da kayan aiki masu tsafta don kaucewa yada kwayoyin cutar ta kansa.
Kai tsaye fida a yanke wurin ciwon ita ce hanyar magance cutar musamman idan aka gano ta da wuri, wannan kuma na ba da karfin gwiwa na kaiwa ga gaci.
- Maganin gargajiya da azumi na maganin cutar kansa
A Najeriya abu ne sananne za ka ga kayayyaki na gargajiya kamar ganyan shayi ko a ce shayi na maganin cutar kansa “a gargajiyance”, wani lokacin abin na jawo tsaiko ko ayi watsi da asibitoci don neman magani baki daya.
Babu wata sheda a kimiyance cewa maganin gargajiya ko yin azumi na maganin cutar kansa. Kansa na faruwa saboda yadda kwayoyin halitta ke hayyayafa da girma ba tsayawa, tana faruwa kuma dalilin sauyin kwayoyin halitta da harbuwa da cuta da dalilai na muhalli ko tsarin rayuwar mutum, Idan ana so ayi nasarar magance cutar kansa akwai bukatar kulawar lafiya da ta hadar da yin fida a yanke wurin da cutar take ko a kone cutar ko a dora mutum kan magani.
Yayin da wasu magungunan na gargajiya ke karfafa jiki wannan baya nufin suna iya kawar da kwayoyin cutar kansa, shan maganin gargajiya na haifar da cutittika masu hadari kamar cutar hanta ko lalata koda, suna haduwa mai hadari da wasu magunguna da ake gashi ko lalata baki dayan lafiya. Yin azumi ba kakkautawa ko a ki cin wani nau’i na abinci na haifar da rauni abin da ke karya garkuwar jiki ta mara lafiya, hakan kuma na sanyawa ya gaza idan ana bashi kulawa ta mara lafiya me cutar ta kansa.
- Mata ne kawai ke kamuwa da cutar kansar nono
Kansar nono cuta ce da sau tari ake gani a matsayin “cutar mata” saboda wayar da kan jama’a da ake yi da tattaunawa kan cutar an fi mayar da hankali ne kan mata, saboda haka maza da dama basa kallon kansu a matsayin wadanda ke ganin wannan barazana ko ma su yi watsi da duba alamu na farko ko su jinkirta zuwa neman lafiya.
Babu shakka maza ma na iya fuskantar cutar kansar nono. Ko da yake ba kasafai ake ganin hakan ba a maza kamar yadda ake gani a mata, tabbas ana ganin wannan cuta ma a tsakanin mazaje. Su ma maza ai suna da nono, kuma ana iya samun kwayoyin cutar su kama nononsu kamar na mata.
Alamun cutar ta kansa a maza iri daya ne da na mata wannan ya hadar da iya ganin kullutu a bangaren kirji a kan nonon ko ruwa ya rika fita ko yanayin fatar ya sauya a kewayen nonon. Kasancewar maza basa zuwa a duba lafiyarsu sau tari sai an makara ake gane an kamu da cutar, idan hanyoyin magance cuta suka takaita kuma sai lamarin ya kazanta.
- Gano cutar kansa hanya ce ta mutuwa
Da dama mutane a Najeriya sun amince cewa muddin aka gano cewa mutum na da cutar kansa to shi kenan sai jiran mutuwa. Wannan shi ke haifar da sanya tsoro da kin aminta ko boye cutar wasu mutanen ma su kauracewa asibiti saboda basu da karfin gwiwa za su iya samun waraka.
Gano cutar a jikin dan Adam baya nufin shike nan ba makawa sai mutuwa, da dama nau’ikan cutar kansa ana iya magance su, musamman idan aka gano su da wuri. Cigaba a fannin lafiya kamar inganta harkar fida ko tiyata da yin gashi na chemotherapy da radiotherapy da shan magani ana samun waraka idan aka rungume su , kamar yadda aka ga ci gaba a fadin duniya.
Sakamakon da ake samu ya danganta da wasu abubuwa wanda ya hadar da nau’in cutar ta kansa da matakin da take da yanayin lafiya na mai dauke da cutar da damar da yake da ita wajen neman magani, alal misali cutar kansa irin ta nono da kansar mahaifa da ta mafitsara wadannan ana iya magance su da zarar an gano su a lokacin da suke a matakin farko.
Kallon cutar kansa a matsayin wacce take kisa hakan na jawo rashin zuwa a duba lafiyar mai cutar da tsaiko wajen duba mara lafiyar abin da ke jawo salwantar rai. Gano cutar da wuri da yin magani a kan lokaci na kawo waraka daga wannan cuta kamar yadda aka gani a lokuta da dama a Najeriya da wajen kasar.
A Karshe
A daidai lokacin da duniya ta yi bikin ranar cutar kansa ta duniya, wannan yaki bai tsaya ga ba da maganin cutar da bin hanyoyin fasaha ba, har sai an yi yaki da canfi da bayanan karya wadanda ke sa mutane na daukar makoma. A Najeriya labaran karya kan cutar kansa na jawo tsaiko wajen zuwa neman magani su hana mutane su je ayi masu gwaji da sanya marasa lafiya gujewa hanyoyin magani na hakika.
