Wutar lantarki. Asalin hoton: MET Group
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wata da’awa da aka tura wa sashin matambayi baya bata na DUBAWA chatbot an yi tambaya ne ko shin an siyar da kafatanin fannin samar da lantarki a Najeriya.

Hukunci: KARYA CE! An siyar da wani bangare ne na fanin samar da kantarki a Najeriya yayin da aka siyar da fannin samo lantarkin da rarraba shi gwamnatinb Najeriya na rike da fannin yadda ake yada lantarkin wanda ke zama muhimmi a sanya farashi da sanya dokoki.
Cikakken Bayani
Samar da lantarki ya fara ne a shekarar 1886, tsawon shekaru wannan fannin ya ci gaba da bunkasa inda aka samar da hukumar samar da lantarki a Najeriya Electricity Corporation of Nigeria (ECN) a 1951 daga nan aka samar da hukumar Niger Dams Authority (NDA) a 1962 wadannan hukumomi biyu sai aka hade su aka samar da National Electric Power Authority (NEPA) a shekarar 1972, wannan ce ta koma kamfanin samar da lanatrki na PHCN a 2005.
A baya bayan nan miniustan samar da lantarki a Najeriya Adebayo Adelabu, ya ba da haske (hinted) cewa wadanda ke samun wutar lantarki a layin Band B basa biyan kudin wuta yadda ya kamata don haka nan ba da dadewa ba za a kara masu kudi. Ya zuwa yanzu wadanda ke a Band A sun cancanci a basu wuta ta tsawon awanni 20 a duk rana yayin da wadanda ke a ajin Band B za a basu wutav ta tsawon awowi 16 haka nan masu ajin Band C ana basu wuta tatsawon awanni 12.
A baya-bayan nan an tura wa DUBAWA chatbot tambaya inda ke neman sani game da cefanar da fannin lantarki a Najeriya.
Wannan tambaya na ci gaba da tasowa daga lokaci zuwa lokaci abin da mke nuna yadda al’umma ke son sani game da batun na samar da lantarki a Najeriya, don haka DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike don ba da bayanai masu inganci.
Tantancewa
Kafar yada labaran Africa Business ta ba da rahoto (reported) a ranar 30 ga watan Satumba 2013 cewa a hukumance gwamnatin Najeriya ta mika (certificates) da duk wasu takardun sheda ga sabbin kamfanoni wadanda suka mallaki kamfanoni 15 na samar da lantarki da rarraba shi. Karkashin shirin cefanar da kadarorin gwamnati, abin da suka bayyana da zama bude sabon babi a harkokin samar da lantarki a kasar.
Kasar ta mallaki kamfanoni na samar da lantarki 6 (GenCos) da kuma kamfanoni na rarraba lantarkin (DisCos) guda 11 wadanda suke rarraba lantarkin. Kamar yadda rahoto (report) na hukumar da ke sa ido kan harkokin lantarki Nigerian Electricity Regulatory Commission (NERC), wacce ke da alhaki na sanya dokoki kan yadda ake siyar da lantarki da harajinsa ya nunar da cewa wannan kamfanoni sun koma karkashin masu zaman kansu amma bisa sa’ido da sanya dokoki ko ka’idoji na hukumar ta NERC.
Duk da cewa an cefanar da kamfanonin sam,ar da lantarkin yadda ake yada shi yana karkashin kulawar gwamnati karkashin kamfanin sadarda lantarki na Transmission Company of Nigeria (TCN). Kamfanin na TCN shike da alhaki na lura da turakun da ake yada lantarkin na kasa wanda hakan ke nufin duk da cewa masu zaman kansu ke samar da lantarki da rarraba shi suna dogara ne da turakun lantarki na kasa mallakar gwamnati.
Har yanzu gwamnati na sa ido kan harkokin lantarki inda hukumar ta NERC ke sa ido kan farashin lantarki da al’umma ke amfani da shi da tabbatar da ganin ana samar masu da lantarkin da kare hakkin masu siya. Jawabi na baya-bayan nan na ministan makamashi Adebayo Adelabu, kan batun kara farashin lantarki ga wadanda suke rukunin B wannan ya kara fito da irin karfin fada aji da gwamnati ke da shi kan kayyade farashin makamashi a kasar.
Gwamnatin Najeriyar na kuma shiga harkokin da suka shafi sanya tallafi da tsare-tsare kan yadda za a rarraba ko kayyade farashi na lantarkin.
A Karshe
Binciken da muka gabatar ya gano cewa fannin sa,mar da lantarki a Najeriya ba baki dayansa aka cefanar ba, yayin da samar da shi da rarraba shi ke karkashin kulawar kamfanoni masu zaman kansu, gwamnati ke da iko kan abin da ya shafi sanya dokoki da ma fitar da farashi.
