Shin da gaske ne an daina amfani da harshen turanci ko Ingilishi wajen koyarwa a makarantun Arewacin Najeriya?

Da’awa: Wani shafi da aka tantance a Facebook ya wallafa wani labari (narrative) cewa gwamnoni a arewacin Najeriya sun yi watsi da amfani da harshen Ingilishi wajen koyarwa a makarantu da ke yankin arewacin na Najeriya.

Shin da gaske ne an daina amfani da harshen turanci ko Ingilishi wajen koyarwa a makarantun Arewacin Najeriya?

Hukunci: Karya ce. Duk da cewa daya daga cikin gwamnoni a yankin na arewacin Najeriya ya bukaci ganin a duba yiwuwar koyar da dalibai da harshen uwa na Hausa a matsayin harshen koyar da karatu a makarantu, wannan ra’ayin da ya nuna ba wai umarni ba ne na cewa za a rika koyarwar da harshen na Hausa. 

Cikakken Sakon

Harshe a ko da yaushe na ci gaba da zama muhimmin abu (element) a tsarin Najeriya da ke da yawan al’umma masu al’adu daban-daban tun ma kafin zuwan Turawan mulkin mallaka, akwai harsuna kamar Hhausa da Yoruba da Igbo wadanda sune harsuna da aka fi amfani da su wajen koyarwa a yankunan al’umma da dama a kasar, sai dai bayan zuwan Turawan kasar Birtaniya sai aka rungumi Ingilishi a matsayin harshen da ake amfani da shi a harkoki ya zama harshen da kasa ta tayi tarayya a kansa. Wannan harshe sannu a hankali har ya zama harshen kundin tsarin mulkin kasar wanda kuma ake koyar da karatu ko ilimi da shi.

Bayan tsawon lokaci harshen na Ingilishi shi ya zama abin dogaro a koyarwa inda ya zama matattara da ta hada al’umma da ke da harsuna da dama suka zama suna magana da harshe guda, tubali da ya zama na samun ilimi har zuwa mataki na kwarewa ko ci gaba.

Duk da wannan sai makarantu a Najeriya suka nuna akwai bukatar sanya harsunan uwa cikin tsarin koyarwa musamman a matakin makarantun firamare don tattali na abubuwan al’adu da karafafa ilimi musamman na kananan yara.

”Sabanin abin da aka sani sai wannan mai amfani da shafin na Facebook  @ChukwudiUfondu ya wallafa wani labari da ke cewa: “Gwamnoni a Arewacin Najeriya sun yin watsi da amfani da harshen Ingilishi wajen koyarwa a makarantunsu!”

An wallafa labarin a ranar 23 ga watan Janairu, 2024 da misalin karfe 8:19 na safe. An barke da martani a tsakanin masu amfani da shafin inda da dama suka yi fatali da da’awar.

@Et GoodluckOghenehro, yaki amince da wannan batu a nasa martani: 

“Wannan ba abu ne da za a lamunta da shi ba, a yi biyayya ga wadannan da ke kiran kansu da gwamnoni. Harshen da aka amince ayi amfani da shi shine Ingilishi. Me zai sanya su rungumi wannan mataki da zai zama mai ila har ga doka?”

Wani mai amfani da shafin mai suna, @EbeleOnwuagha, yayi tambaya ne da cewa: “Ta yaya za su rubuta jarrabawar WAEC da JAMB?”

Shi kuwa a nasa martani, @OmeniJem yayi martani ne da cewa: “Amma suna so kowa ya iya magana da harshen Hausa kafin su dauke shi aiki.”

Duk da cewa wannan wallafa ba ta samu martani da yawa ba, DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike kan ta, ganin akwai murdiya a cikinta za kuma ta iya jawo kace-nace.

Tantancewa

DUBAWA ta yi amfani da wasu muhimman kalmomi ta yi amfani da shafin Google wannan ya kaimu ga shafin jaridar Punch da Daily Trust inda Gwamna Bago na jihar Niger yayi kira ga sauran takwarorinsa na Arewacin Najeriya su sake nazari don ci gaba da koyar da dalibai da harshen Hausa a matsayin harshen koyarwa a yankin. Ya bukaci da a rika koyar da harshen na Ingilishi a matakin firamare da sakandare a matsayin wani darasi da ake koyarwa cikin darusan makaranta ba wai harshen da za a rika amfani da shi don koyarwa ba. 

A cewar mai ba da rahoton Bago ya bayyana haka ne a wani taron kwararrun masu ilimi da aka yi a Minna don tuni da zagayowar ranar haihuwar marubuci BM Dzukogi, da ya kafa gidauniyar Hilltop Arts Foundation, a lokacin da ya cika shekaru 60 a duniya.

Yace idan ana koyar da dalibai da harshen na Hausa za a kara samun yawan dalibai da ke zuwa makaranta, zai kuma kara masu fahimta ta karatu. Ya ce gwamnonin arewacin Najeriya su duba wannan bukata ta yadda za a rage yawaitar yara da basa zuwa makaranta.

A cewar jaridar Daily Trust Bago ya bukaci iyaye su samawa yaransu littafai na karatu da sauran kayayyaki ta yadda za a bunkasa tunaninsu, ya kara da cewa dabbaka halayyar karatu a tsakanin matasan ita ce hanya mafi dacewa wajen hana durkushewar al’umma. Ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take wajen samar da ilimin koyon sana’oi a makarantu ta yadda za a samu wadanda suke kammala makarantu da kwarewa ta ilimin ga kuma sana’a.

Bayan wadannan abubuwa da aka gano, babu wasu bayanai ko wani jawabi daga bangaren gwamnoni daga arewaci na Najeriyar da ya nuna a yi watsi da harshen Ingilishi wajen koyarwa.

A Karshe

Yayin da rahoton ya nuna bukatar Gwamna Bago na Niger ta ganin ana amfani da harshen Hausa wajen koyar da dalibai a makarantu da ke arewacin Najeriya , babu wata sheda da ta nuna cewa gwamnoni na arewacin Najeriya sun yi baki guda wajen yin watsi da harshen Ingilishi a matsayin harshen koyarwa a makarantu da ke Najeriya.

Exit mobile version