|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook mai suna @Daily Updates ya fitar da wata wallafa cewa dafin kudan zuma na magance cutar kansa ko cutar daji cikin mintuna 60.

Hukunci: Yaudara ce. Da’awar ta nuna kambama binciken farko na dakin gwaji sannan an gabatar da wasu abubuwa wadanda ba a fayyace ba aka ce yana magani.
Cikakken Sako
Cutar kansa cuta ce da ke zama barazana ga rayuwar al’umma da dama. Akwai nau’ika da dama na cutar kansa, a kowane mataki tana da nata siradi, da girman matsaloli da ke tattare da cutar. Bincike ya gano cewa akwai wasu na’uika na hanyoyi da ake bi don magance cutar ta hanyar abin da aTurance ake kira chemotherapy da sauran wasu hanyoyi da ake bi. Irin wannan hanyar lura da cutar da ake bi ta taimakawa mutane da dama sun samu waraka yayin da wasu kuma basu kaiwa ga gaci suna rasa rayukansu saboda cutukan da ke tattare da cutar.
Wani shafin Facebook mai suna @Daily Updates, yayi da’awa cewa dafin zuma na maganace cutar kansar mama ko nono da ta gagara cikin mintuna 60.
”Wannan da’awa na tafe da taken labari da ke cewa “a wani abu da ke nuna cewa an cimma gagarumar nasara a fagen aikin kimiya inda masanan suka gano yadda dafin kudan zuma ke raga-raga da kwayoyin cutar kansa ta nono kamar yadda aka gano a dakin binciken kimiya an kuma tabbatar da cewa yana kawar da kwaoyoyin cutar da kaso 100% cikin minuta 60.”
Mai da’awar yace sirrin shine an gano yadda melittine da ake samunsa a cikin dafin zuma ke katse hanyar da ke haifar da samuwar rarrabuwar kwayoyin halittar da ke cikin cutar kansar nono ta yadda za su dena girma da dema yaduwa.
A wallafar ta ci gaba da cewa shi sinadarin na mellitin na lalata kwayoyin halittar ta kansa da ake kira (triple-negative da HER2-positive ) wadanda su wannan biyun suna da hadari sosai. Ta kara da cewa lafiyayyun kwayoyin halittar sukan zama ma ba a iya taba su, abin da ke nuna cewa shi dafin kudan zuman na iya zama dama mai kyau ta maganin wannan cuta ko ma a ce yana da ingancin ma da ya sha gaban amfanin gashin da masu cutar ke yi wanda ake kira chemotherapy a Turance.
A wannan wallafa dai har ila yau ta kammala da cewa dafin zuma babbar hanya ce ta magance kwayoyin cutar kansar mama ko nono.
Ya zuwa ranar 19 ga watan Nuwamba,2025 wannan wallafa ta samu masu nuna sha’awa wato likes 37,000 da masu tsokaci comments 1,900 da wadanda suka yada sama da dubu biyar.
Mun nazarci tsokacin da ake yi don fahimtar irin tunanin mutanen da suke yin martani.
@ Kayden Gilbeaux, ga misali tace, “Duk abin da muke nema wata kila gashi nan ma , kawai ba a gano ba ne, idan har kana tunani akansa.”
@Abdul Garcia ya rybuta cewa, “ Ba zato ba tsammi kusan za a iya cewa dukkanin kudan zuma da muke da su suna neman bacewa.”
@Benjamin Kelly ya kara da cewa, “Da alamu abubuwan da Allah ya halitta da muke kashewa ba ma basu kariya sune za su yi mana maganin cutuka da suke damunmu.”
@Jess Paschen ta bayyana nata ra’ayin, “ wannan ya nuna cewa tunatarwa ce cewa ba kowane abu ne da ka gani a intanet zai zama gaskiya ba.”
Sakonnin da aka wallafa a sashin tsokaci ya nuna cewa wasu daga cikin masu amfani da shafin sun amince da da’awar, yayin da wasu kuma suka yi watsi da ita har ma suke neman mai da’awa ya ba da hujja.
Wannan wallafa ta samu martani da dama kuma sanin cewa duk abin da ya shafi lafiyar dan’Adam abune da ke jan hankali mun ga dacewar gudanar da bincike kanta.
Tantancewa
DUBAWA ya fara gudanar da bincikensa ta hanyar farawa da sanin hanyoyi da ake bi na magance cutar kansa don ganin cewa ko dafin kudan zuma na daga cikin hanyoyin. A cewar mujallar Medical News Today daya daga cikin hanyoyi da ake bi don magance cutar sun hadar da yin fida ko tiyata , akwai gashi da ake yi ta hanyar abin da ake kira radiation therapy a Turance karkshinsa akwai Chemotheraphy wanda ya hadar da na’uka daban-daban kamar yadda suke a zayyane haka: (gashi da daukar hoto da gashi mai amfani da haske, da gashi mai karfafa garkuwa, da gashi da ake nufar wani bangare na cutar, da gashi da ya shafi kwayoyin halitta), dukkanin wadannan na farwa cutar ta kansa ta hanya ta musamman, ko dai a nufi wani bangare ko kuma a karfafa garkuwa, duk jerin wadannan hanyoyi babu inda aka bayyana dafin zuma cikin hanyoyi da ake bi wajen magance cutar dajin ko kansa.
DUBAWA ta kuma duba wasu kafofin ciki har da dafin na zuma a matsayin maganin cutar dajin amma babu wata kafa da ta tabbatar da hakan, wasu ayyukan binciken da tushensu da aka yi kan maganin cutar zaa iya ganinsu kamar a wadannan wurare
Tun da wannan batun an mayar da hankali kan batun kansar mama, mun duba yadda ake jinya ko lura da cutar ta kansar nono, domin ji a ina ne ake maganar amfanmi da dafin kudan zuma a cewar Cibiyar yaki da Cutar Kansa ta Kasa (NCI) cikakkun hanyoyin kula da wannan cuta sune yanke inda ciwon ya lalata da yin gashi abin da ake kira Chemotheraphy a Turance da gashi ta hanyar amfani da haske da gashin kwayoyin halittar da gashi na wani bangare da ke fama da cutar da gashi na kara karfin garkuwar jiki.
Asibitin Mayo Clinic yayi bayani ya bayyana cewa idan ana maganar cutar kansar mama, likitoci sau tari bayan yanke bangaren da cutar ta shafa suna amfani da haske wajen gashi suna amfani da Chemotheraphy da bunkasa garkuwar jiki da yin gashi na wani bangare na jiki, ya danganta da bangaren da ke ci gaba da girma , idan aka hada irin wadannan matakai ana cire cutar a kuma dakile yiwuwar dawowarta.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar da rahoto da ya nuna cewa mutane 670,000 sun mutu a duniya ta dalilin cutar sankara ko daji a shekarar 2022 da kimanin miliyan biyu da dubu dari uku wadanda suka zama sabbin ciwo ne.
Kiyasi daga Cibiyar kasa da kasa mai kula da bincike kan cutar kansa (IARC) ya nunar da cewa za a samu mutane miliyan 3.2 sabbin kamuwa da cutar, da mutane miliyan 1.1 da za su mutu duk shekara nan da 2050, muddin aka ci gaba da samun irin wannan yanayi da ake ciki.
Duba da wadannan bayanai da zarar aka ce ga wata hanyar magance cutar kansar mama, kamar yadda wannan mai amfani da Facebook yayi ikirari da hasashen da ake ya hadar da kawai samun mafita.
Me ake cewa game da dafin na kudan zuma?
Baya ga rashin hujja na cewa dafin kudan zuma na maganin cutar kansar nono, DUBAWA ta kuma gano cewa wannan dafi an gudanar da aiki a kansa a dakin bincike, binciken da aka gano kuma ya nuna cewa shi sinadarin na melittin da wasu abubuwa da ya kunsa an gano yana kashe wani kwayar halittar da ta shafi cutar ta kansa, kana yana hana girma na kwayar halittar, masanan na kimiya sun kuma bayyana wasu hanyoyi da ake bi a kai shi ba tare da wata matsala ba, ko ta hanyar gashin da ake kira chemotheraphy ko ta abin da ake kira (nanomaterials), har ila yau wannan hanyar fa ba a yi amfani da shi ba ba a gwada ba a jikin dan Adam, wannan sakamakon gwaji da aka samu a dakin bincike na nuni da cewa wannan ba hanyar samar da waraka bace kai tsaye har sai an dauki shekaru na gudanar da gwaje-gwaje.
Ra’ayin Kwararru
Amina Bello, malama a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa kuma wacce ke karatun digiri na uku a fannin yaki da cutar kansa da ake kira oncology ta bayyana cewa shi bincike kan kansa abune da ake yi sannu a hankali ba a sauri a hanyar, kuma babu abin da ake cewa maganin cutar kai tsaye. A cewarta duk wata hanyar da aka tabbatar to ta dauki tsawon lokaci idan kuwa aka dauki mara lafiya abin kan dauki lokaci ma mafi tsayi.
“A dakin gwaji aikin na farawa ne da tsayawa a kalli yadda kwayoyin halittar kansar ke sauyawa idan an sami sauyi a muhallin da suke rayuwa, za a dauki lokaci da bincike da gwaji da samun kuskure har sai masana kimiya sun tabbatar da cewa wannan sakamako haka yake.” a cewarta.
Ta kara da cewa ko da kuwa a ce dafin kudan zuma na da sinadaran da za su yi maganin cutar ta kansa a yanzu kuskure ne a yanke hukunci cewa yana magani “binciken da ba a kammala ba a ce yana maganin cuta cikin mintuna,” ta kara jaddadawa.
Yunusa Ayuba, masanin harkar lafiya a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano Teaching Hospital, shi ma ya ba da tasa fahimtar ga DUBAWA.
Yace nauyin da ke kan batun cutar kansa yana da yawa a duniya, a duniyar kimiya babu wani abu da zai buya ga masana musannan a fagen da kowa ke fafutuka. Yace lura da cutar kansa na da tarin kalubale a Najeriya, don haka mutane su guji irin wadannan labarai, wadanda ke iya zama na yaudara ga al’umma da dama.
”Lura da cutar kansa abune mai wahala a Najeriya kuma abu da mutane za su yi na karshe shine su kirkiri wani abu suce yana maganin cutar wanda kuma ba haka ba ne, dafin kudan zuma baya maganin cutar kansar nono ko wani abu mai kama da haka, idan da ace yana maganin cutar kamar haka yadda masu fadi ke cewa da tuni masu ruwa da tsaki sun gano, ya fadawa DUBAWA cewa ko da a kasashe da suka ci gaba inda ake lura da cutar da ma hanyoyin da abi na ci gaba, wannan dai ba hanya ce ta maganin cutar ba kamar yadda ake yadawa.”
Yunusa yace abu mafi kyau shine ayi watsi da irin wannan bayanai irin na wannan da’awa.
“Abu mafi kyau da za a yi da wannan bayani shine a yi watsi da shi, idan mutane za su yada wani abu sabo na binciken kimiya kamata yayi su rika ba da misali, dama inda aka yi amfani da maganin aka samu waraka ko wani bincike da ya tabbatar da shi.” a cewarsa.
A Karshe
Binciken DUBAWA ya gano cewa dafin kudan zuma baya maganin cutar kansar nono, binciken da ake da shi a dakin gwajin kimiya kawo yanzu shine akwai tasirinsa amma ba a jikin dan Adam ba, don haka da’awar yaudara ce.
