Shin gaskiya ne gwamnatin Sokoto ta haramta kyaututtuka a aure da taruka tsakanin maza da mata Musulmi da Kirista?

Does Sokoto ban wedding gifts and mixed gatherings for Muslims and Christians?
Sultanate Palace, Sokoto.
Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani bidiyon da ya dauki hankali na da’awar wai gwamnatin jihar Sokoto da hukumar Hisbah sun haramta kyaututtukan aure da tarurrukan da suka hada mata da maza daga addinan Musulunci na Kirista a cikin jihar.

Shin gaskiya ne gwamnatin Sokoto ta haramta kyaututtuka a aure da taruka tsakanin maza da mata Musulmi da Kirista?

Hukunci: Yaudara ce. Duk da cewa hukumar Hisbah na Sokoto ta sanar da sabbin dokokin da suka shafi wasu harkoki da al’adun aure, DUBAWA ta gano cewa wadannan dokokin ba su shafi kiristoci ba.

Cikakken bayani

Ranar 13 ga watan Agustan 2026 wani mai amfani da shafin X ya wallafa bidiyo ya na kira ga ‘yan Najeriya da su kalla, ya na da’awar cewa hujjoji ne da suka tabbatar da wadansu daga cikin fargabar da ya bayyana cikin wani bidiyo dangane da makomar addinin Kirista a Najeriya.

Bidiyon (wanda ake iya gano a nan) ya nuna wani mutumi wanda bai bayyana ko shi wane ne ba ya na bayyana abin da ya kwatanta a matsayin matakan da hukumar Hisbah ke dauka a jihar Sokoto.

A cikin bidiyon, ya yi da’awar cewa yanzu babu r kyaututtukan aure, da masu sanya sautin da aka fi sani da DJ  da ma dai tarurruka kamar yadda aka sani tsakanin maza da mata a jihar SOkoto. Haka nan kuma yayi da’awar wai wadannan dokokin sun shafi kirista da musulmi, inda ya ce yanzu kiristoci maza da mata ba za su iya taro tare ba bare ma zuwa coci dan yo sujada tare.

Mutumin ya kuma cigaba da gabatar da wannan da’awar sabbin dokokin a matsayin wani bangare na abun da ya kwatanta da ajandar musuluntarwa, inda ya ce wanzar da dokokin shari’a a jihar Sokoto shi ne matakin farko na yunkurin da ake yi na yada addinin musulunci a wasu yankunan arewacin Najeriya kafin a fadada zuwa wasu yankunan kudancin kasar.

Bidiyon ya fusata mutane da dama musamman wadanda suka yi tsokaci a kan labarin inda wasu suka soki dokokin da ma irin tasirin da ya ke da shi kan ‘yancin walwalar addini

Wani mai amfani da shafin X, (@kaderkingpin91), wanda ya ce shi musulmi ne ya rubuta cewa, “Hisba ta keta dokokin Islama. Babu inda a cikin Alkurani mai girma aka ce dole ne kowa ya bi dokokin Islama. Hasali ma cikin sura na biyu, Alkuranin ya ce babu dole a addinin Islama.”

Shi ma mai amfani da shafin, Dapsie (@Dapsijaiye), ya bayyana fargabansa kan abin da suka kwatanta a matsayin ajandar musuluntar da Najeriya. Ya ce: Matsalar kiristocin Najeriya shi ne tunaninsu ya fi mayar da hankali ne kan abubuwan da za su yi tasiri cikin gajeren lokaci. Musuluntar da Najeriya ajanda ce ta wani tsawon lokaci, kuma abin da wannan mutumin ke bayyanawa ha zai faru nan da shekaru biyar  kadai.”

Daniel (@Sir_Willoh) Shi ma ya bayyana fushinsa dangane da wannan da’awar, inda ya yi tambayar ko me ya sa shugabanni suka yi shiru

“Wannan ya na matukar ba ni haushi. Me ya sa shugabanni suka yi shiru? Me ya sa muke da dokokin ketare a kasar? Ko wadanda su ke yankin Gabas Ta Tsakiya ba su yin haka. Su waye ke daukar nauyin wadannan dokokin?” ya tambaya.

Daga 21 ga watan Agustan 2026 mutane sama da 101,400 sun ma’amala da labarin wasu 1,700 sun sake wallafawa yayin da wasu 202 suka yi tsokaci kan labarin.

Ganin yadda irin wannan batun ka iya yin tasiri a bangaren addini da siyasar kasar da ma yadda batun ya dauki hankali ne ya sa DUBAWA tantancewa.

Tantancewa

DUBAWA  ta yi bitar wadannan da’awowin da aka yi cikin bidiyon sa’anan ta gudanar da bincike a rahotanni da ire-iren sanarwar da hukumar Hisbah da ma sauran hukumomi da majiyoyin  jihar masu mahimmanci suka yi.

Binciken ya gano cewa an dauki bidiyon ne sakamakon wani umurnin da hukumar Hisbah a jihar Sokoton ta bayar, amma sun gabatar da dokokin a fadade ne ba tare isassun hujjojin da suka goyi bayan dokokin ba.

Sokoto ba ta haramta kyaututtukan aure ba.

Hukumar Hisbah ta jihar Sokoto ta sanar da dokoki kan wadansu harkokin da suka shafi aure da kashe kudi ba kima.

Ranar 27 ga watan Yulin 2026, kwamandan Hisbah Usman Abdullahi ya sanar da dokokin wadanda suka shafi wasu daga cikin al’adun da akan yi gabannin buki irin su “Na Gani Ina So” wadda al’ada ce ta ganawa da surukai wadda ta kunshi kawo kyaututtuka irinsu lemun kwalba, biskiti, alawa da goro.

Haka nan kuma hukumar ta yi gargadi kan yawan kayan da ake kaiwa amarya wanda aka fi sani da lefe.

Cikin bidiyon da mai kula da harkokin labaran kwamandan Hisban Isha Rufa’i ya wallafa a Facebook, Kwamandan ya ce wani wani mataki ne a yunkurin da ake yi na rage yawan kudin da ake kashewa lokacin gudanar da bukukuwan aure.

Sai dai bai ce wai duka kyaututtukan aure ne aka hana ba.

Dan haka wannan da’awar na cewa Sokoto ta hana kyaututtukan aure ba gaskiya ba ne yaudara ce.

Shin an haramta tarurruka na jinsin maza da mata a waje guda?

Hukumar Hisbah ta kuma sanar da dokokin da suka takaita haduwa tsakanin maza da mata a wasu wurare musamman wadanda suka hada da aure da wadansu taruka na zamantakewa.

Rahotanni na umurnin watan Yulin ya bayyana haduwa tsakanin maza da mata a lokutan bukukuwa na nishadi a cikin abubuwan da hukumar ta haramta.

Sai dai wannan dokar ba kowani irin taro tsakanin maza da mata ta shafa ba.

Dokokin da Hisbah ta fitar sun shafi wadansu taruka ne wadanda ke karkashin dokokin addinin da hukumar ke da hurumin aiwatarwa.

Dokokin ba su shafi kiristoci ba

Wannan da’awar cewa dokokin sun shafi kiristoci da musulmi karya ce.

Kwamandan Hisbah Usman Abdullahi ya fadawa DUBAWA cewa wadannan dokokin sun shafi musulmi ne kadai.

“Mun yi wadannan dokokin ne dan Musulmi kadai ba dan wani addini ba,” ya fayyace.

Da muka tuntubi shugaban Kungiyar Kiristoci na Najeriya (CAN) a Sokoto, Kayode James, shi ma ya ce dokokin ba su shafi kiristocin jihar ba.

Ya kara da cewa shi kansa mutane da yawa sun tuntube shi dan samun karin bayani dangane da batun.

A Karshe

Da’awar wai gwamnatin jihar Sokoto da Hukumar HIsbah sun haramta taruka da musayar kyaututtukan aure tsakanin maza da mata na addinan kiristoci da musulmin jihar yaudara ce kawai.

Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) da OSINT  tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.