Motocin kwatanu. Asalin hoton Peoples Gazette
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
A ranar 1 ga watan Afrilu, 2026 ministan kudi a tarayyar Najeriya Wale Edun ya rattaba hannu a tsarin haraji da hada-hadar kudaden gwamnati wato Fiscal Policy Measures (FPM) na shekarar 2026.
Wannan tsari ya rage kudaden haraji kan motocin daukar fasinjoji hada da motoci masu kofa hudu da masu doro da ake kira (station wagons), harajin da aka rage masu wanda ya kai kaso 70 cikin dari.
Bayan fitar da wannan sanarwa an shiga yanayi na farin ciki da jin dadi a shafukan sada zumunta inda da dama ‘yan Najeriya suka rika hasashen cewa farashin motoci zai yi kasa, amma shin hakan abu ne mai yiwuwa?
A wannan bayani DUBAWA ta duba adadin da ake fadi inda ta kwatanta da’awar da abun da ke a kasa na zahiri.
Me gwamnati tace ne
Abu mai muhimmanci shine ya kamata a sani cewa gwamnati ta rage haraji ne ba kudin fito na motoci ba, duk da cewa mutane basu cika banbance wadannan abubuwa guda biyu ba, wato kudin fito da na haraji , abubuwa ne daban-daban. Kudin fito da ake kira (import duty) kudade ne da ake biya idan za a shigo da kayayyaki cikin kasa. shi kuwa kudin harajin na Tariff daya ne daga cikin jerin kudaden da ake biya.
Wannan sabon ragin kudade zai maye gurbin manyan kudade da aka gabatar a tsarin haraji da hada-hadar kudaden gwamnati na shekarar 2015. Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa “ta fito da wannan tsari ne “don bunkasa wasu muhimman fannoni na tattalin arziki.”
Wannan lokaci da aka ba da damar kwanaki 90 ne ga masu shigo da kayayyaki da dama tuni sun bude fom da ake kira fom ‘M’ kafin ranar 1 ga watan Afrilu, 2026. Wannan na nufin motocin da ke kan hanya da wadanda suke jibge a tashar gabar teku za su biya kudadensu a kan tsohon tsarin wanda ke zama kaso 70 cikin dari.
Don haka ganin sauyi na farashin motocin a hannun diloli zai iya daukar watanni kafin a gani a kasa.
Nawa ake bukata idan ana so a shigo da mota Najeriya?
A nan ne jin dadin da ake yi a kan wannan tsari ta yiwu aji abin da ba haka ake tsammani ba, aji gaskiyar lamarin duk daci kuwa.
Ga mai siyan kayayyaki wani abu da bai sani ba shine, shi wannan haraji daya ne daga cikin tarin harajin da ake biyawa mota kafin a kawota wajen siyar da motoci.
Wasu sanannun kudade da ake biya kafin shigo da mota. Tushen hoton: Nigeria Customs Service.
Sauran kamar inshorar mota da harajin hukumar da ke kula da harkokin samar da motoci ta (NAC) da harajin VAT da kudaden da ake warewa abin da ka je ka dawo da kudin dakon kaya duk ana tattara su. Da zarar aka tattara wadannan kudade da kudin masu aikin fito ko dan kamasho sai a wayi gari kudaden sun yi sama.
Shin farashin kudin mota zai sauka?
A kan takarda kudin harajin mota ya kasance kaso 70 cikin dari, a zahirance kuwa da dama diloli na mota basa biyan kudaden baki daya saboda hanyoyin da ake bi na neman alfarma da samun sauyi a tsari, da dakatarwa da aka yiwa tsarin shekaru sama da 10.
Wani mutum da yayi magana da DUBAWA ya bayyana cewa yana biyan daga kaso 30 zuwa kaso 35 cikin dari maimakon wancan adadi.
A takaice dai a farkon shekarar 2026 Hukumar Kwastam na amfani da tsarin kwamfuta inda ake karbar harajin motocin kaso 20 cikin dari hadi da harajin gwamnati kaso 15 cikin dari. Wannan ya sanya harajin ya kai kaso 35 cikin dari, wanda wannan adadi ya kasance kasa da abin da gwamnati ta ce ta rage na kaso 70 cikin dari.
Yayin da aiwatar da wannan ke nufin sabon “haraji ya zama kaso 40 cikin dari” a takarda ya nuna kamar an rage kudaden, amma a zahiri a wajen dilolin mota kari ne kasancewar dama can basa biyan kaso 70 cikin dari din kafin wannan lokaci.
Duba da wadannan hujjoji sanin yadda sauyin zai shafi mai siyan mota ya dogara ne da wasu tarin abubuwa.
Na farko ya danganta da sauyin farashin kudaden waje, abu na gaskiya shine naira na sauyawa ba kakkautawa tun daga shekarar 2023, domin haka idan naira za ta yi kasa nan da lokacin da dilolin motar za su sake dauko wasu jiragen motocin, yadda ake samun sauyi a canjin kudin zai iya shafar kudaden harajin.
Dilolin motar na kuma iya kin amincewa su sadar da saukin da suka samu zuwa ga masu siyan motar sai dai idan akwai matsin lamba ko masu sa ido don tabbatar da ganin an aiwatar da ragin har ya kai ga mai siya.Suna iya ganin wannan dama a matsayin abin samun riba da zasu sanya a aljihunsu.
Har ila yau kungiyar dillalan motoci a Najeriya ta bayyana cewa sabon tsarin ragin harajin ba zai sa masu siyan motoci su samu sauki ba.
A wata tattaunawa da jaridar The Sun, shugaban kungiyar Ajibola Adedoyin, yace ko da yake tsarin zai shafi ragin farashin amma ragin ba wani mai girma ba ne.
”Ga misali, idan motar kudinta miliyan biyar ne, kudin harajin kuma kimanin N400,000, idan aka rage kudin harajin zai koma N150,000. ”Wannan adadi ba lallai ya gamsar da mai siyan motar ba, tabbas Idan gwamnati za ta rage kudin fito na shigo da motoci to tabbas za a iya ganin tasiri ga mai siyan motar kasancewar wannan kudi na da yawa sosai idan aka kalli kudaden da ake biya baki dayansu” kamar yadda ya fadawa kafar yada labaran.