Mitar lantarki. Mallakar hoto: Guardian Nigeria.
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da Facebook ya yi ikirarin cewa masu shan wutar lantarki a Arewacin Najeriya suna biyan kuɗin lantarki fiye da na Kudancin ƙasar.

Hukunci: Yaudara ce. Binciken DUBAWA ya gano cewa ana ƙayyade kuɗin lantarki a Najeriya bisa tsarin rukuni da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta amince da shi, ba saboda yankin da mutum yake zaune ba.
Cikakken Bayani
Wani mai amfani da Facebook ya wallafa wani bidiyo (ajiye a nan) a ranar 28 ga Mayu, 2026, yana ikirarin cewa masu amfani da lantarki a Arewacin Najeriya suna biyan kuɗi mai yawa idan aka kwatanta da mutanen Kudancin ƙasar.
A cikin bidiyon, mutumin wanda ke magana da harshen Hausa tare da nuna hotunan da ke kwatanta sayen lantarki a Bauchi da Ibadan, ya bayyana cewa ana zaluntar mazauna Arewa ta hanyar kakaba musu tsadar lantarki.
Bisa lissafin da ya gabatar, ya ce a Bauchi, Naira 1,000 na samar da unit na lantarki guda huɗu kacal, wanda ke nufin ana sayar da kowane unit a kan Naira 250. Sai kuma ya ce a Ibadan, Naira 90 na samar da unit na lantarki 8.5, wanda ya kai kusan Naira 10.59 kan kowane unit.
Daga nan ya kafa hujjar cewa idan aka yi amfani da wannan lissafi na Ibadan, Naira 1,000 za ta iya sayen kusan unit na lantarki 94.4.
Bidiyon ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda wasu suka fassara lamarin a matsayin nuna wariya tsakanin yankunan ƙasar wajen farashin lantarki.
Wani mai amfani da Facebook mai suna Ibrahim Umar Mesago ya bayyana goyon bayansa ga ikirarin.
“Gaskiya Nigeria a rarrabe take a fakaice, saura a rubuce ne ya rage kawai” in ji shi.
Sai dai wani mai suna Saddam Ibn Sulaiman ya bayyana sabanin ra’ayin, yana mai nuni da bambancin rukuni na lantarki.
“Ya kamata ka san akwai bambanci tsakanin kowane rukuni. Ko a nan Bauchi ma akwai bambancin kuɗin wuta. Wanda yake Band A daban yake da na Band C.”
Zuwa ranar 3 ga Yuni, 2026, bidiyon ya samu kallon mutane 462,000, an yi sharhi sama da 1,100 da kuma yaɗawa 9,600.
Saboda yadda ikirarin ke iya haifar da rashin fahimta da kuma tayar da hankulan jama’a game da tsarin kuɗin lantarki a Najeriya, DUBAWA ta binciki gaskiyarsa.
Tantancewa
DUBAWA ta duba tsarin farashin lantarki a Najeriya kuma ta gano cewa Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ce ke tsara farashin lantarki a faɗin ƙasar.
A karkashin tsarin da ake kira Service-Based Tariff (SBT), an raba masu amfani da lantarki zuwa rukuni biyar: Band A, B, C, D da E, gwargwadon matsakaicin sa’o’in wutar lantarki da suke samu a kullum.
Masu shan lantarki da ke cikin manyan rukuni suna samun wuta na tsawon lokaci kuma suna biyan kuɗi mafi yawa, yayin da waɗanda ke ƙananan rukuni ke samun wuta na ɗan lokaci kuma suna biyan kuɗi ƙasa da haka.
Misali, masu amfani da ke Band A ya kamata su samu aƙalla sa’o’i 20 na wuta a rana, kuma suna biyan kuɗin da ya dace da ainihin farashin samar da wutar. A gefe guda, masu amfani da ke Band D da Band E suna samun ƙarancin sa’o’in wuta kuma suna biyan kuɗi mafi sauƙi.
Domin tantance ikirarin da mai amfani da Facebook ya yi, DUBAWA ta duba jadawalin kuɗin lantarki da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ibadan (IBEDC) ya wallafa.
Jadawalin ya nuna cewa masu amfani da Band A suna biyan Naira 209.50 kan kowace kilowatt, masu Band B suna biyan tsakanin Naira 67.25 zuwa Naira 70.41, yayin da masu Band D ke biyan Naira 32.44, kuma masu Band E ke biyan Naira 32.26 gwargwadon nau’in mitarsu.
Domin tabbatar da bayanan, DUBAWA ta duba takardar biyan lantarki daga Jihar Oyo.
Takardar, wadda IBEDC ta bayar ga wani kwastoma a yankin Apata Business Hub na Ibadan, ta nuna cewa ana cajar sa ne Naira 32.44 kan kowace unit, wanda ya yi daidai da Band D Non-MD da hukumar NERC ta amince da shi.

Takardar lissafin lantarki da DUBAWA ta samu.
Ƙarin bincike ya nuna cewa lissafin da mai ikirarin ya gabatar bai bayyana muhimman bayanai ba, ciki har da rukuni (Band) na kwastomin da kuma ko akwai wasu gyare-gyare ko karin kuɗin lantarki da aka sanya.
DUBAWA ta kuma duba tsarin farashin lantarki da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Jos (JED) ke amfani da shi, wanda ke samar da lantarki ga Bauchi da wasu jihohin Arewa.
Tsarin farashin na JED ma yana bin tsarin rukuni da NERC ta amince da shi.

Hoton jadawalin farashin lantarki na JED.
Wannan tsarin ya nuna cewa mutane biyu da ke zaune a gari ɗaya za su iya biyan kuɗin lantarki daban-daban idan suna cikin rukuni daban.
Haka kuma, mutane da ke zaune a yankuna daban-daban na ƙasar za su iya biyan kuɗi iri ɗaya idan suna cikin rukuni ɗaya. Saboda haka, bambancin kuɗin ba daga yankin da mutum yake zaune ba ne, sai dai daga rukunin da NERC ta sanya shi.
A Karshe
Ikirarin cewa lantarki ta fi tsada a Arewacin Najeriya fiye da Kudancin ƙasar yaudara ce.
