Wani bidiyo da ke nuna yadda ake ajiyar wake ta hanyar amfani da siminta yaudara ce

Da’awa: Wani bidiyo da ya yadu a shafin WhatsApp ya nuna yadda wasu mutane a arewacin Najeriya ke zuba “siminti” cikin busasshen wake don tattalinsa ko ajiya.

Wani bidiyo da ke nuna yadda ake ajiyar wake ta hanyar amfani da siminta yaudara ce

Hukunci: YAUDARA CE. Bincike da DUBAWA ta gudanar ya gano cewa wannan farin abun da ake gani sinadarin (calcium carbonate) ne ba siminti ba kamar yadda mai da’awar ya nunar. Kuma abin da aka nunar a bidiyon na da illa idan za a ci.

Cikakken Sako

Farashin wake ya rika tashi (surged) ba kakkautawa a shekarar 2024, abin da ya sanya abincin da a baya kowa ke iya siya ya gagari da dama ‘yan Najeriya. Duk da cewa farashin ya fadi (recent drop) a baya-bayan nan, har yanzu siyan wake ya gagari kimanin ‘yan Najeriya miliyan (129 million) wadanda ke rayuwa a cikin talauci. Bayanai da Bankin Duniya ya fitar a 2024 ya nunar (revealed) cewa ‘yan Najeriya kaso 65 cikin 100 na rayuwa cikin talauci inda basa iya kashe Dala $2.15 a rana. Akwai dalilai da dama da suka zama sune silar hakan, abin da ke nuna irin kalubalen da kasar ke ciki ta fuskar wadata kasa da abinci.  Kungiyar masu samar da wake a Najeriya  Cowpeas Farmers Association of Nigeria (CFAN) (said) ta bayyana cewa raguwar samar da wake da rikicin manoma da makiyaya da fitar da waken zuwa kasashen ketare da rage darajar Naira sune dalilai da suka shafi farashin na wake da sauran kayan masarufi.

A wannan bidiyo mai tsawon dakika 58 a shafin na WhatsApp da DUBAWA ta samu an masa take da cewa “Manoma a arewa na amfani da siminta don ajiyar wake tsawon lokaci, da Allah idan za ku yi amfani da wake ku tafashi sau biyu kafin a fara dafawa.” Shafin na WhatsApp ya nunar da cewa wannan bidiyon an yada shi sau da yawa.

Wani bidiyo da ke nuna yadda ake ajiyar wake ta hanyar amfani da siminta yaudara ce

Wannan bidiyo ya yadu a shafin Facebook, wani shafi mai suna Admin TV, a Facebook ya yada wannan bidiyo wanda ya tattara (gathered) masu martani 22, mutane 11 suka yi tsokaci (comments) da 127 suka sake yadawa (reshares). Ya zuwa ranar 11 ga Satumba,2025.

Ogbonnaya Sebastine, wani mai amfani da Facebook ya samu (had) martani 15 da tsokaci 30 bayan wallafa wannan bidiyo a ranar 8 ga Satumba,2025. Ga ma wasu wurare da wannan wallafa ta bayyana (here da here, da here).

Duba da yadda wannan bidiyo ya yadu dama matsalar abinci da ke a kasar, wannan ya sanya DUBAWA ganin dacewar gudanar da bincike kan wannan batu.

Tantancewa

Ta hanyar amfani da manhajar Vid WeVerify, DUBAWA ta duba asalin bidiyon don gano asalin wannan buhu dauke da farin garin hodar da aka bayyana da zama siminti, sai kuwa binciken ya kaimu ga shafin Facebook Calcium Carbonate Freedom Group Eastern Region wanda ke siyar da sinadaran  calcium carbonate a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya. 

Wannan shafi na aikin rarraba sinadaran na Kaolin da Cacite da calcium carbonate da kamfanin Freedom Group ke samarwa.

Mun lura cewa shi wannan buhu a bidiyon da ya yadu  yana kama da wanda kamfanin na Freedom Group  ke samarwa.

Yadda bidiyon yake a bincike

Duk da cewa ba cikin sauki ake iya saurin ganewa ba, a jikin buhun an rubuta lamba 55, a jikin tambarin an rubuta ‘Calco.’ a gefen buhun kuma an rubuta ‘Freedom’, DUBAWA ta lura da cewa duka wadannan abubuwa ko rubutu an sanya su a wannan buhu na  “calcium carbonate” da ke shafin na Facebook page

Hotunan buhunhunan, Hoto: Phillip Anjorin

Mun lura cewa abin da aka barbada a kan waken fari ne. 

Hoton da ke nuna yadda mutum ke barbada farin abun a bidiyon. 

Kalar Calcium Carbonate ita ma fara ce.

Manoma da fari suna amfani da calcium carbonate, wanda kuma ake kiransa “agricultural lime,” don inganta kasar noma abin da ke inganta amfanin gona, ana amfani da shi don gyara kasa idan sinadarin Acid yayi yawa, yana da muhimmanci wajen samun sinadaran kamar nitrogen da phosphorus don amfanin tsirrai. Ta hanyar daidaita kasa akwai bukatar samar da sinadaran na calcium carbonate ta yadda tsirrai za su samu karfin jijiyu su girma.

Haka kuma shi sinadarin na calcium muhimmi ne wajen samun karfin bishiya ko tsirrai, samar da shi har ila yau na kara inganta kasar noma da yadda take rike ruwa da fitar da shi.

Wannan inganta yanayin na kara samar da karfin jijiyar da lafiyar shuka. Ana kuma amfani da calcium carbonate a wani lokacin a samar da abincin dabbobi su samu karfin kashi da kwarin bawo na kwai.

Har ila yau abin da aka yi amfani da shi da aka nunar a bidiyon calcium carbonate ne kamar yadda aka nunar a jikin buhun, duk da cewa ana amfani da calcium carbonate a ayyukan gona ana kuma amfani da ita a masana’antu ta wata fuskar kuma.

Akwai fila da ake amfani da ita (intended) a lokacin yin fenti da dangoginsa, ba ana amfani da ita don ajiyar wake ba kamar yadda aka bayyana a bidiyon. 

A jikin buhun abin da aka nunar irin abin da ake amfani da shi a masana’anta ne, abin da ke ciki ba irin na ayyukan gona bane. Irin wannan na kunshe da wasu sinadarai da ke zama masu hadari wanda ba su dace da abin da dan Adam zai ci ba.

Ita fila ta masana’anta ko ta fenti na dauke da wasu sinadarai wadanda ba na ci bane, ana hada wannan ce don aiki na daban ba abin da ya saba da sharuda na cin abinci (food safety).

Cin wake da ke dauke da waccan hoda da aka gani a bidiyon na da hadari sosai kasancewar yana da wasu sinadarai masu hadari (heavy metal poisoning)  da zai iya kawo matsala a ciki ko ya shafi kwakwalwa ko lalata wata gaba ta jikin dan Adam.

Karshe

Abin da aka yi amfani da shi don ajiyar wake kamar yadda aka gani a bidiyon fila ce ta  calcium carbonate, ba siminta ba kamar yadda aka yi ikirari. Duk da cewa  calcium carbonate bashi da illa amma amfani da nau’insa da ake amfani da shi na masana’antu kamar wanda ake yin fenti da dangoginsa, yana da hadari wajen amfani da shi wajen cin abinci.

The content used to preserve beans in the video is calcium carbonate filler, not cement as claimed. Although calcium carbonate is not harmful, the industrial-grade filler in the video is used in paints and coatings, which is hazardous for human consumption.

Exit mobile version