Mark Zuckerberg. Asalin hoton: David Paul Morris/Bloomberg.
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Ranar Talata bakwai ga watan Janairu, shugaban kamfanin Meta Mark Zuckerberg ya sanar da hukuncin da kamfaninsa ya yanke na katse hulda da kungiyoyin da suke aiki da su wajen tantance sahihancin bayanan da ake wallafa a kan shafukansu, wanda kuma za su fara da Amurka. Kafin wannan sanarwar, Meta na amfani da kwararrun masu bincike ne masu zaman kansu wajen sanya ido kan batutuwan da ake wallafawa a shafukanta na Facebook, Instagram da Threads.
A karkashin wannan shirin, Meta ta kulla kawance da kungiyoyi irin su DUBAWA dan tantance bayanan da ake sanya alamar tambaya kan sahihancinsu a kan duka dandalolin, da kuma kai kararsu saboda a cire su ko kuma dai a dauki irin matakan da suka dace. Wannan ne ma ya taimakawa Meta wajen gano bayanan da ke yaudarar jama’a.
Meta ta sanar cewa za ta maye gurbin wadannan kungiyoyi da abun da ta kira community notes a turance ko kuma sharhin al’umma. Wannan sabon matakin zai taimaka wa duk wadanda ke amfani da shafin su yi karin bayani dangane da sakon da suka wallafa inda za su iya fadan ko akwai batutuwan da ke zaman karya ko kuma dai suna dauke da bayanan da ka iya yaudarar jama’a. Wannan ne za’a iya amfani da shi wajen tantance bayanan da ke zaman karya ko gaskiya.
Duk da cewa wannan ba sabon abu ba ne ga masu amfani da shafin X, sabo ne ga wadanda ke amfani da shafukan da ke karkashin kamfanin Meta. Dan haka ga mahimman tambayoyi shida wadanda za su taimaka mu ku wajen fahimtar wannan karin da aka yi.
1. Mene ne makasudin community notes?
Bisa bayanan shafukan X, Reddit, da Wikipedia, wadanda suka riga suka fara amfani da wannan salon, babban dalilin samar da shi, shi ne yaki da bayanan da ba daidai ba. A shafin X, ya kan bukaci masu amfani da shafin su yi karin bayani dangane da batun da ka iya yaudarar mutane ko kuma dai ba gaskiya ba.
Idan alal misali ka ga labarin wani tauraro ko tauraruwarka da ba gaskiya kuma babu kwakwarar hujja. Da community notes kana iya zuwa inda aka sanya bayanin ga fayyace da na ka hujjojin ko kuma dai ka yi karin bayanin da zai yi karin haske. Idan aka yi haka mutane suna iya yanke shawarar da ta dace da su ba tare da sun fiskanci wata matsala ba.
To sai dai amfani da community notes din a shafin X bai hana mutane wallafa bayanan karya ba.
2. Se wane ne za su iya yin wannan sharhin na al’umma ko kuma community notes?
Ko da wanda bai saba amfani da shafin ba ne ko kuma kwararre, Notes na ita taimakawa jama’a wajen shiga a dama da su wajen tattaunawa. Ke nan duk wanda ya ga batu kuma ya na da sha’awar shiga tattaunawar, ya na iya shiga ya bayar da gudunmawa ko ma dai ya fayyace abun da ya ga kamar zai jefa mutane cikin duhu. Wannan dai kamar shiri ne al’umma baki daya wanda kowa zai iya tallafawa wajen ganin an samar da maslaha mai kwari daga karshe. Ta yin haka, sai a sami ra’ayoyi mabanbanta, da mahawara irin wadda za ta amfani jama’a.
Bacin kasancewarsu kwararru, masu bincike sukan yi hira da mutane su kuma yi amfai da manhajojin zamani wajen tantance duka bayanan da suka gani. Koma bayan Notes dai shi ne har da masu karamin sani ma na iya sharhi kan batun dan haka ba lallai ne a sami irin fayyacewar da ua fi dacewa ba tamkar ba’a rabu da bukar ba an haifi habu ne.
3. Ta yaya ake tantance bayanan da aka yi?
Hanya guda da X ke bi wajen tantance bayanan shi ne barin jama’a su nuna alamar ko labarin ya amfane su ko bai amfane su ba. Yin hakan ya kan bayyana labarin da ya fi daraja ko kuma ya fi amfanan mutane. Ta haka ne ake iya tantance bayanin da ya fi sahihanci. Batun ko wannan na da irin mahimmancin da ake bukata kuma wani abu ne daman
4. Ta yaya za’a iya samun Notes?
A shafin X, idan har note ya sami kuri’u da dama a al’ummar shafin, ana iya ganin shi a karkashin ainihin labarin da aka fara wallafawa. Wannan na nufin idan har wani abun da mutun ke shakkar sahihancin shi ya bulla a shafin shi, zai iya duba notes din da sauri dan samun karin bayani.
5. Mene ne alfanun Notes?
Bisa bayanan wadanda suka kirkiro shi, burin community notes shi ne samar da hadin kai da yadda a tsakanin masu amfani da shafin ta yadda za su zurfafa tunaninsu dangane da abubuwan da suke karantawa a shafukansu. To sai dai bacin kasancewar wannan matakin na da nasaba da siyasa, Zuckerberg na ganin cewa hakan zai tabbatar da ‘yancin fadan albarkacin baki.
6. Shin Community Notes na da iyaka?
Mutane da dama sun ce community notes na da iyaka ba komai ne zai iya yi ba idan aka zo batun tantance bauanan da ba daidai ba. Bisa bayanan Alex Mahadevan, darektan MediaWise a cibiyar Poynter, daa daga cikin manyan batutuwan shi ne kusan kashi 60 cikin 100 na notes din ba a cika ganinsu cikin manyan kanun labaran ba. Ma’ana da yawa daga cikin abubuwan da akan fayyace ma ba’a ganinsu.Bugu da kari, kafin a bayyana note cikin manyan batutuwan da ake tattaunawa dole sai an amince da shi a duka dandalolin siyasar da ke kan shafin kuma wannan babban kalubale ne tunda yawancin alkiblolin mutanen da ke amfani da shafin da kyar ne zai zo daya. Wannan ne ya kan janyo tsaiko ya kuma hana mutane mayar da martani kan abubuwan da ke kai ga yaduwar rahotannin da ba daidai ba wanda kuma ya ke rage tasirin manhajar.
