|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Mai amfani da shafin Facebook na da’awar wai Iran ta ce nan ba da dadewa ba kasashen Kenya da Najeriya za su shiga rikicinta da Amurka.

Hukunci: Yaudara ce. Wannan da’awar ba ta fito daga shafin gwamnatin Iran ba. Hujjojin da muka sa mu sun kai mu ga wata majiyar da aka goge wadda hira ce da aka yi a gidan rediyon kasar da wani masanin harkokin kasa da kasa da ba’a tantance ko shi wane ne ba ne.
Cikakken bayani
Takaddama tsakanin da Iran da Amurka na cigaba da ta’azzara tun bayan hare-haren soji da rigingimu na diflomasiyya da matakan ramakon da suka dauka.
Wannan rikicin ya dauki hankalin kasa da kasa, inda kasashe da dama suke nuna goyon bayansu ga bangaren da suka zaba ta hanyar fitar da sakonnin diflomasiyya, bayar da hadin kai a fannin sojoji da tsaro, da bayannan sirri da ma ayyukan jinkai.
Bisa la’akari da wannan ne, da’awowin da ake dangantawa da wasu karin kasashe a rikicin ke cigaba da yawo musamman a shafukan sada zumunta.
Ranar 10 ga watan Yulin 2026, wani shafin Facebook, Civic Media News (wanda ake iya gani a nan), ya wallafa labarin da ke zargin wai Iran na da’awar cewa Najeriya da Kenya za su shiga yakin.
Labarin na cewa, “Labarai da dumi-duminsu: Iran na da’awar wai mai yiwuwa nan ba da dadewa ba Kenya da Najeriya za su shiga rikicinta da Amurka.
Daga 13 ga watan Yulin 2026, labarin ya sami alamar like sama da 521, akwai kwament 168 sa’anann an sake rabawa sau 21.
Wannan batu dai ya haddasa husumi tsakanin masu amfani da shafukan sada zumunta musamman ‘yan Najeriya.
Wani mai amfani da shafin Mudassir Muhammed, cewa ya yi, “Wace Najeriyar? Yau ga wani tashin hankalin.”
Wani shi kuma, Ola Gold, ya rubuta, “Me zai faru da ni yanzu tunda ba da dadewa ba mata ta haihu?”
Wani shi ma Johnson Bruce, tambaya ya yi dangane da sahihancin wannan da’awar inda ya ce “wace Najeriyar ku ke magana a kai idan kun yarda?”
questioned the claim, asking, “Which Nigeria are you talking about, please?”
Mun kuma sake ganin batun a nan da nan.
Ganin yadda batun ya tayar wa jama’a da hankali kamar yadda muka gani a cikin tsokacin da suka yi da ma yiyuwar haddasa tashin hankalin da labarin ke da shi ya sa DUBAWA tantance gaskiyar lamarin.
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da binciken mahimman kalmomi dan tabbatar da ko akwai kafofin yada labarai masu nagarta da suka yi rahoto dangane da wannan da’awar da ake zargin ya fito daga gwamnatin Iran.
Binciken ya kai mu ga wani rahoton da aka wallafa a Kenyans.co.ke, wanda ya yi bayanin cewa labarin ya yi mafari ne daga wani shafin X na wata tashar yada labaran Iran wato IRIB wadda mallakar gwamnati ce, amma ba daga shafin gwamnatin kasar ko ma wani jami’i mai magana da yawun gwamnati ba.
Yayin da IRIB ke zaman mallakar gwamnati, labaranta da wallafe-wallafenta a shafukan sada zumunta ba lallai ne su wakilci matsayar da gwamnatin Iran din ta dauka a hukumance ba.
Haka nan kuma rahoton ya kara da cewa ita wannan hirar da aka gani a shafin tashar, an danganta ta ne da wani masanin kasa da kasa ba ma’aikaci ko jami’in gwamnatin Iran din ba.
Labarin ya ce, “Masanin harkokin kasa da kasa ya fadawa IRIB cewa: Kenya da Najeriya su ma suna da dakarun sojoji a ajiye wadanda za su iya shiga filin daaga a lokacin da ya dace.”

Screenshot of the Tweet by IRIB
To sai dai wanda aka wallafa a Facebook bai fadi ainihin abin da labarin ya fada ba a maimakon haka ya bayyana batun a matsatin sanarwar da ta fito daga gwamnatin Iran a ahukumance.
Daga ita tashar ta IRIB da masanin wanda ba’a tantance ko shi wane ne ba babu wanda ya ambato wani jami’in Iran a batun.
DUBAWA ta kuma yi kokarin tantance shafin rashar na X amma ba ta ga komai makamancin haka ba duk kuwa da cewa ta duba har da shekarun baya. KO da shi ke a wani shafin YouTube, mai suna Make Afrika Again, an yi amfani da hoton da aka sa cikin labarin aka sa sauti a cikin wani bidiyon da aka wallafa ranar 10 ga watan Yulin 2026.
Tashar ta kaucewa yin bayani kan dalilan da suka sa aka ambato wadannan kasashen, kuma ba ta fayyace abin da ya sa aka goge hirar ba. Wannan rashin hujjojin da ma yadda aka goge bayanin duk sun rage sahihancin batun.
Domin samun karin haske, DUBAWA ra tuntubi IRIB dan ji ko goge hirar da a yi ya nuna matsayar da dauka ko ta gwamnati, sa’annan ta kara da bukatar hujjojin da suka godi bayan wannan da’awar.
Sai dai har zuwa 14 ga watan Yulin 2026 sadda muka kammala wannan labarin ba su sami wani martani daga IRIB ba.
A Karshe
Da’awar wai Iran ta ce kasashen Kenya da Najeriya za su shiga yakinta da Amurka yaudara ce. Duk hujjojin da muka samu an danganta su ne da wani bidiyon da aka wallafa a tashar watsa labaran IRIB kuma yanzu sun cire batun daga shafinsu.
