|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da dandalin Facebook, Spy Nigeria, ya yi ikirarin cewa sama da baburan ‘yan bindiga 100 ne suka mamaye Karamar Hukumar Funtua da ke Jihar Katsina.

Hukunci: Yaudara ce. Ko da yake an yi artabu a garin Funtua a ranar 4 ga Satumba, 2026, Rundunar Tsaron Al’umma ta Jihar Katsina (KSCWC) da rundunar ‘yan sanda sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga bakwai ne, ba gungun ‘yan bindiga a kan babura sama da 100 ba.
Cikakken Bayani
A daidai lokacin da fargabar ayyukan ‘yan bindiga ke ci gaba da addabar Jihar Katsina, mazauna Karamar Hukumar Funtua sun ci gaba da zama cikin shirin ko-ta-kwana sakamakon hare-haren da ake kaiwa a kauyukan noma da ke kewayen garin.
Halin da ake ciki ya kara jefa jama’a cikin fargaba a ranar 4 ga Satumba, 2026, lokacin da wasu mahara dauke da makamai suka shiga yankin da ake kasuwanci a garin Funtua.
Yayin wannan zaman dar-dar, wani shafi a dandalin Facebook mai suna Spy Nigeria ya wallafa wani rubutu yana cewa, “An hango baburan ‘yan bindiga sama da 100 yayin da a halin yanzu ‘yan bindiga ke kai hari a Karamar Hukumar Funtua a Jihar Katsina”.
Rubutun da aka adana ya janyo martani daban-daban daga masu amfani da dandalin Facebook.
Ahmed Lawal, Faruku Umar, tare da Shafiu Ahmad Ciroma, sun yi addu’ar neman kariya ga mutanen yankin.
Wani Ismaila Ayoola, tambaya ya yi, “Daga wace kabila ne ‘yan bindigar suka fito?”
Masu amfani da dandalin da dama sun nuna shakku kan adadin baburan da aka ambata.
Wani mai suna Isah Halidu ya ce, “Jami’an ‘yan sanda da masu tsaron al’umma ne suka kore su. Don haka ina shakkar adadin ababen hawan da suka zo da su.”
Ya zuwa ranar 8 ga Satumba, 2026, ikirarin ya samu martani 112, sharhi 28, da kuma sake yadawa sau 25.
Ruruta alkaluman jami’an tsaro ko mahara a lokacin da ake cikin rikici na iya haifar da firgici tare da karkatar da ainihin gaskiyar abin da ke faruwa. Saboda haka, DUBAWA ta gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin.
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da bincike a garin Funtua inda ta tattauna da shaidun gani da ido da suka kasance a wurin da lamarin ya auku.
Muhuyiddeen Mansur, wani dan kasuwa da ya shaida lamarin, ya bayyana cewa maharan sun zo ne a cikin mota kirar Volkswagen Golf guda daya, ba a cikin ayarin babura ba.
Ya kara da cewa daya daga cikin maharan ya sauka domin sayen takalmi a wani shago da ke kusa, amma yadda yake tafiya da dabi’unsa sun jawo hankalin mazauna yankin har suka sanar da ‘yan sandan kwantar da tarzoma (MOPOL) da ke sintiri a kusa.
Mansur ya ce bayan sun kama shi, sauran ‘yan bindiga shida da ke dauke da makamai suka bude wuta nan take a kan motar ‘yan sandan domin ceto shi.
Salisu Maikankan, mai magana da yawun Rundunar Tsaron Al’umma ta Jihar Katsina (KSCWC), ya tabbatar da wannan bayani.
Maikankan, wanda ya shiga aikin kai daukin, ya tabbatar da cewa ‘yan bindiga bakwai ne kacal suka haddasa lamarin, inda ya bayyana cewa jami’ai sun kama mutum daya a take a wurin, sannan suka sake cafke wani a yankin Mahuta, yayin da sauran maharan suka tsere.
DUBAWA ta kuma tuntubi ofishin ‘yan sanda na yankin Funtua. Wani Sufeto a ofishin, Adamu Sambo, ya karyata labarin da aka yada a dandalin sada zumunta.
“Ƴan bindigar mutum bakwai ne kacal, ba jita-jitar da ake yadawa ta cewa sun haura mutum 100 a kan babura ba”, in ji shi.
Jami’in ya bukaci al’umma da su daina yada labaran da ba a tabbatar da su ba wadanda ke iya jefa mutane cikin fargaba da hargitsi a lokacin da ake gudanar da aikin tsaro.
A Karshe
Ikirarin da ke cewa sama da ‘yan bindiga 100 a kan babura sun kai hari a Karamar Hukumar Funtua da ke Jihar Katsina yaudara ce. Ko da yake an yi musayar wuta bayan da jami’an tsaro suka cafke wadanda ake zargin a cikin garin, kwararan hujjojin da aka samu sun tabbatar da cewa ‘yan bindiga bakwai ne kacal da ke tafiya a cikin mota suka kai harin.
Wannan bincike an gudanar da shi ne a karkashin shirin Cibiyar Bunkasa Aikin Jarida da Kirkire-kirkire (CJID) tare da tallafin Tarayyar Turai (European Union).
