|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani shafi a dandalin Facebook mai suna Hausawa ya yi ikirarin cewa mutane da dama da ake zargi da zama ‘yan bindiga sun fito daga daji domin halartar nadin sarautar Alhaji Sani Tukur a matsayin sabon Sarkin Ruman Katsina kuma Uban Ƙasa a Ƙaramar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.

Hukunci: Yaudara ce. Wani rahoto da Katsina Times ta wallafa ya tabbatar da cewa wasu daga cikin mutanen da ke cikin hotunan tubabbun ‘yan bindiga ne da suka zo bikin nadin sarautar tare da taya sabon basaraken murna, a matsayin alamar tabbatar da dorewar zaman lafiya a Batsari.
Cikakken Bayani
A ranar 30 ga Agusta, 2026, wani shafi a Facebook mai suna Hausawa ya yada wasu hotuna guda uku (wadanda aka adana a nan) yana mai ikirarin cewa mutane da dama da ake zargi da zama ‘yan bindiga sun fito daga daji domin halartar nadin sarautar Alhaji Sani Tukur a matsayin sabon Sarkin Ruman Katsina kuma Uban Ƙasa a Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina.
Ya zuwa ranar 7 ga Satumba, rubutun ya samu martani 165, sharhi 67 da sake yadawa sau 16.
Rubutun ya janyo ra’ayoyi mabanbanta a tsakanin masu amfani da dandalin, inda wasu suka nuna shakku kan gaskiyarsa yayin da wasu kuma suka gaskata shi.
Muammar Gaddafi ya yi sharhi inda ya tambayi ina ‘yan bindigar suke a cikin hoton, yana mai cewa, “Ni dan Batsari ne.”
Wani mai amfani da dandalin, Oluranti Olujitan, ya nuna mamakin dalilin da zai sa a bar wadanda ake zargi da laifi su halarci taron jama’a su kuma fice ba tare da an kama su ba.
“Yanzu duk wanda bai kai shekara 40 ba dan bindiga ne muddin shi Musulmi ne?” Adedayo Julius ya tambaya.
Ikirarin ya fito ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kokarin samar da zaman lafiya da sulhu tsakanin tubabbun ‘yan bindiga da al’ummomin Batsari, biyo bayan kwashe shekaru da dama ana fama da rashin tsaro da hare-haren kungiyoyi masu dauke da makamai. Saboda haka DUBAWA ta binciki ikirarin.
Tantancewa
DUBAWA ta binciki hotunan da suka nuna mutane da dama suna halartar bikin al’adar. Tambarin Katsina Times yana bayyane a jikin hotunan.
Binciken amfani da muhimman kalmomi ya kai DUBAWA zuwa ga bidiyon da aka yaɗa kai tsaye na bikin nadin sarautar Alhaji Sani Tukur, wanda ya gudana a Batsari a ranar 29 ga Agusta, 2026.
Mun kuma gano wani rahoto da Katsina Times ta wallafa a ranar 30 ga Agusta, wanda ya bayyana cewa tubabbun ‘yan bindiga da tsofaffin shugabannin kungiyoyi masu dauke da makamai sun halarci bikin.
Rahoton ya bayyana sunayen shugabanni guda biyu, ‘Tukur da Bala Musa,’ wadanda suka gabatar da kyaututtukan ban girma kamar shanu, fura, da nono ga sabon basaraken.
Rahoton ya ce tubabbun ‘yan bindigar sun bayyana goyon bayansu a bainar jama’a ga sabon basaraken tare da tabbatar da aniyarsu ta wanzar da zaman lafiya a Batsari.
Shugaban Kwamitin Sulhu da Zaman Lafiya na Karamar Hukumar Batsari, Mamman Mannir Murtala, ya bayyana halartar tubabbun ‘yan bindigar a matsayin wani gagarumin ci gaba a tattaunawar da ake yi domin kawo karshen shekaru da dama na ayyukan ‘yan bindiga a karkara a Batsari.

Hoto daga wajen nadin sarauta. Mallaka: Katsina Times
Kafar yada labarai ta Blueprint Hausa ita ma ta yi labari game da taron, inda ta ruwaito cewa tubabbun ‘yan bindiga da dama sun halarci bikin, suka sake jaddada goyon bayansu ga sabon Hakimin, kuma suka yi alkawarin ci gaba da zaman lafiya a yankin.
DUBAWA ta kuma tuntubi Zaharaddeen Ishaq, dan jaridar Katsina Times da ya dauki rahoton bikin kuma ya dauki hotunan.
“Tubabbun ‘yan bindiga ne kamar yadda aka ruwaito. Sun zo nadin sarautar kuma sun taya mutane murna domin nuna ci gaba da sadaukarwarsu ga zaman lafiya a Batsari,” ya kara da cewa.
Saboda haka, kwararan hujjoji sun nuna cewa tubabbun ‘yan bindiga ne da suka fito daga daji suka halarci nadin sarautar, ba ‘yan bindiga masu tayar da kayar baya ba.
A Ƙarshe
Ikirarin yaudara ce. Wasu daga cikin mutanen da ke cikin hotunan tubabbun ‘yan bindiga ne da suka zo domin halarta tare da taya murna a wajen nadin sarautar a matsayin alamar dorewar zaman lafiya a Batsari.
Wannan bincike an gudanar da shi ne a karkashin shirin Cibiyar Bunkasa Aikin Jarida da Kirkire-kirkire (CJID) tare da tallafin Tarayyar Turai (European Union).
