African LanguagesHausa

A WhatsApp ana sake yada wani tsohon bidiyo da da’awar cewa ‘yan bindiga na barazana ga cocuna a Najeriya 

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da dandalin sakonni na WhatsApp na  wallafa wani bidiyon da ke cewa kwananan ‘yan bindiga sun tura wasu wasiku zuwa cocuna a Najeriya suna da barazanar cewa su rufe su su tashi.

A WhatsApp ana sake yada wani tsohon bidiyo da da’awar cewa ‘yan bindiga na barazana ga cocuna a Najeriya 

Hukunci: Yaudara. Bayanan da muka samu sun nuna mana cewa wannan bidiyon mai tsawon mintoci uku da dakiku bakwai na nuna kwamishinan ‘yan sandan Zamfara ne ya na bayani dangane da wata wasikar da wasu suka ajiye cikin wani cocin da ke jihar, kuma wannan ya faru ne tun a shekarar 2022, shekaru biyu da suka gabata.

Cikakken bayani

Daya daga cikin manyan kalubalen da yankin arewa maso yammacin Najeriya ke fuskanta ita ce rashin tsaro daga ‘yan bindiga wadanda ke kai haro kan cocuna, masallatai, tashoshin mota, al’ummomi da makarantu.

Wata mai amfani da WhatsApp ta wallafa wani  bidiyo ranar 14 ga watan Mayun 2024, tare da taken “‘Yan bindiga sun tura wasiku zuwa ga cocunan Najeriya suna musu gargadin cewa su rufe su tashi, sun ce Najeriya mallakar su ce kuma suna so su karbi kasarsu. Mu yi hattara mu kuma rika la’akari da tsaro a duk inda mu ke.”

A cikin bidiyon tsohon kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Ayuba Elkanah ya tabbatar da cewa sun ga wasikar da ake zargi ya fito daga wurin ‘yan bindigan wanda ke umurtar kiristoci da su rufe cocuna na tsawon watanni uku a jihar Zamfara.

A cikin bidiyon, Mr Elkanah ya ce an kawo wasikar hedikwatarsu kuma shi da kansa ya bude sakon.

Old video about bandits threatening Nigerian churches recirculated on WhatsApp

Labarin na WhatsApp

Yaduwar da wannan labarin ya yi a kungiyoyin WhatsApp da ma sarkakiyar da batun ke da shi ya sa DUBAWA daukar nauyin tantance batun.

Tantancewa

Mun gudanar da bincike ta hanyar sanya bidiyon cikin manhajar tantance hotuna ta Google Reverse Image Search daga nan ne muka gano cewa tun a shekarar 2021 ake yayata bidiyon.

Sa’annan mun gano bidiyon na ainihi wanda aka wallafa a shafin YouTube, inda kwamishinan ya yi bayani dangane da wasikar da ya samu.

A jihar Zamfara aka nadi bidiyon sadda Mr Elkanah ya gana da manema labarai ranar 30 ga watan Nuwamban 2021. Lokacin hirar ta sa da ‘yan jarida, a Gusau, babban birin jihar, Mr Elkanah ya tabbatar cewa ya sami wasikar da ke daukwe da barazanar ‘yan bindiga wadanda kuma suka bukaci cocuna a Zamfara su daina aiki na tsawon shekaru uku domin idan ba haka ba akwai hadarin cewa za’a kai mu su hari.

“Wadansu wadanda ba’a san ko su wane ne ba suka ajiye wasikar a gaban ofishin ‘yan sanda,” kwamishinan ‘yan sandan ya bayyana.

Yayin da suke samr da matakan dakile matsalolin tsaro, shugaban ‘yan sandan ya fayyace cewa wasikar ta bayyana sunayen wadansu cicuna wadanda ke daga wajen babban birnin ta ce za ta kai musu hari a karshen shekarar 2021.

Jaridar Vanguard newspaper ta dauki wannan labarin ranar daya ga watan Disemban, 2021.

A Karshe

Bincikenmu ya nuna mana cewa bidiyo kan wasikar da ‘yan bindiga suka bayar a Zamfara ba kwanan nan suka yi ba, tun shekarar 2021 labarin ya bulla yanar gizo-gizo. Dan haka labarin da ake yayatawa yaudara ce.

Wannan rahoton aikin bincike an yi shine karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 karkashin shirin kwararru na Kwame KariKari Fellowship da hadin gwiwar Olufisoye Adenitan, FRCN positive fm Akure Ondo t a kokari na fito da “gaskiya” a aikin jarida da inganta ilimin aikin jarida a fadin Najeriya.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button