Getting your Trinity Audio player ready...
|
Dubban ‘yan Najeriya ne suka shiga wani yanayi na ha’ula’i bayan da suka fada hannun mazambata.
Mutane da dama a kan kafofin sadarwa daban-daban suka rika kidayar yawan rashin da suka yi, yayin da kamfanin CBEX, sanannen dandalin hada-hadar kaddarori suka lakume fiye da triliyan daya da digo uku na Naira daga asusun masu zuba jari. Dandalin ya ma rushe bayan da kudaden suka bata, aka kuma dakatar da cire kudi sa’annan kuma aka toshe duk wasu hanyoyin sadarwa,
Taiwo Owolabi, wani mai nazarin harkokin tsaro kwanan na ya yi wani nazarin da ke nuna yadda aka zare kudaden masu zuba jari aka sa a cikin wani babban asusun shafin wanda a yanzu haka ke dauke da dalar Amurka miliyan 857.
Mai nazarin harkokin tsaron ya kammala da cewa CBEX wata hanya ce kawai ta cin kudi da zamba cikin aminci.
Hoton wani bangare nanazarin Owolabi. Asalin hoton: Trending Explained.
Sadda CBEX ya yi alkawarin bai wa jama’a ribar dari bisa dari a kan yawan kudin da suka sa a matsayin ajiya na Crypto cikin kwanaki 30, ‘yan Najeriya da yawa suka je suka sa kudadensu kamar dai yadda suka yi sadda aka damfari mutane a wancan shirin na zuba jari wanda ya bi ruwa na MMM. To sai dai banda rushewar da CBEX ya yi, ya bukaci wasu daga cikin wadanda suka zuba jarin da su biya dalar Amurka 100 zuwa 200 dan a sako mu su wani adadi na kudin.
Yanzu da komai ya rikice haka, sai mu yi tambayar da ya kamata a ce an yi tun farko: “Yaya aka yi aka shammace mu haka ba tare da mun ga wasu alamu ba?”
Ga wasu daga cikin alamun da muke ganin ya kamata a ce da an yi la’akari da su kafin a zuba jarin.
- Kamfanin bai yi rajista da hukumomin da ya kamata a ce ya yi ba
CBEX ya yi aiki ne ba tare da aminciewar Hukumar da ke Kula da masu zuba jari da harkokin hada-hadar kasuwannin kudi wato SEC ko kuma ma na Babban Bankin Najeroyar. Amma duk da haka, ‘yan Najeriya suka je suka kai kadudadensu, da imanin cewa shafin ya halatta saboda yadda aka alkinta shi. Bisa dukkan alamu dai wannan ya zama wani sabon salo ke nan domin ko a baya sadda aka zalunci ‘yan Najeriya su ma shafukan ba su yi rajista ba.
Tun da dadewa SEC ta gargadi ‘yan Najeriya kan hadarin da ke tattare da zuba jari a kamfanonin yanar gizo-gizon da ba su yi rajista ba, har ma ta ce an haramta yin hulda da irin wadannan kamfanoni a karkashin sabuwar dokar tabbatar da tsawo a harkokin zuda jari ko kuma dokar ISA.
Darasi: A tabbatar an tantance sahihancin dandalolin zuba jari a kan yanar gizo kafin a sa kudi.
- Ba’a san wadanda suka kirkiro kamfaniaan ba
Shafin CBEX da ma takardun cikawa ba su bayyana wadanda suka mallaki kamfanin ba kuma babu sunayen manyan kamfanin. Domin batar da kama su nuna kamar suna da nagarta, sun kera shafin CBEX din ya yi kama da shafin hada-hadar kudi na crypto, su na ma magana a kan blockchain, wanda ke nuna shiga da fitan kudade, da ma sauran nau’o’in hada-hadar kudin irin su “Trading bots” da tsare-tsaren da ke amfani da basirar AI. To sai dai duk da haka ba shi da makalun da za’a iya tantancewa, ko kuma ma wadanda ke da alaka da shafukan crypton da aka sani. Dan haka sun yi amfani da kalaman fasaha ne kawai suka rudi jama’a.
Darasi: Idan har ba’a sana wadanda ke bayan shafi ba a guji yin ma’amala da shafin.
- Alkawarin samun riba dari bisa dari, da samun matsala wajen cire kudi daga asusun
Duk da cewa babu wani yawan kudin da aka kayyade a sunan yawan kudi ko kuma ribar da ya kamata a ce an samu a kan jarin da aka zuba, idan har aka yi alkawarin riba mai yawa ko ma dai ko wani irin dogon buri ya kamata ayi hattara domin irin wannan ba mamaki yaudara ce.
CBEX ya yi wa masu zuba jari alkawarin samun ribar 100 bisa 100 a kan kudinsu cikin kwanaki 30. Wannan shi kan shi ya nuna cewa yaudara ce. Kamar yadda aka gani a baya, yawancin irin wadannan alkawuran da kyar ake cikawa, amma kuma har yanzu ana amfani da irin matakan wajen jan hankalin jama’a.
Da farko, CBEX ya yi aiki. Masu amfani da shafin sun rika samun kudi amma kamar yadda Owolabi ya bayyana sun rika amfani da kudin wani ne suna biyan wani har zuwa lokacin da suka ga ba su iyawa.
Dab da rushewar kamfanin, masu amfani da shafin da dama sun yi korafin cewa ba su iya cire kudadensu kamar yadda suka saba. CBEX cewa ta yi ba wani abu ba ne illa matsalar da ake samu sakamakon guyaran da ake yi a shafin da kuma matsalolin da ke da kasaba da layi ko kuma network. Wanda yawanci dabara ce kawai ta masu yin zamba cikin aminci.
Darasi: Alkawarin samun riba mai yawan gaske yawancin lokuta alama ce ta yaudara. Rashin iya cire kudi shi ma alama ne cewa kudin na karwa, kuma hakan na nuna cewa sun fara shirin yin awon gaba da kudaden ke nan.
- Biye wa infuluwensas da ma matsin lamba daga takwarori
Fargabar “kada a yi ba ni” ko kuma The Fear Of Missing Out (FOMO)kamar yadda ake cewa da turanci abu ne da yanzu ya ke shafar kowa, babu babba babu yaro, musamman idan har infuluwensas, abokai, da iyalai suka sanya baki. To sai dai cin amana ta hanyar yada bayanan da ba daudau ba ya na yawan faruwa a irin wannan lamarin.
Babban abin da ya budewa CBEX kasuwa shi ne soshiyal mediya da kuma bayanan fatar baka. Sun yi dogaro sosai da bayanan jama’a musamman wadanda suka fi kusa da su.
Daga bayanan shafukan WhatsApp zuwa shafukan Facebook da bidiyoyin TikTok, CBEX ya kuma sake samun karbuwa ne sakamakon bayanan shaidu. Mutanen da suka yi bayani dangane da kudaden da suka samu, (wasu bayanan karya ne ma) sun dauki hotunan kudaden da suke zargin sun samu suna yadawa tare da bayanai masu sosa rai.
Sadda abokai da iyalan wasu suka gaskata da shafin , da yawa sun mance da mahimmancin tantance shafin kafin suka jari.
Darasi: Ji daga bakin wanikawai ba zai isa ba idan har ana si a tantance sahihancin batutuwa irin wannan. A tabbata a ko da yaushe an sake samun wata majiya mai zaman kanta wajen tantancewa, ko da kuwa ‘yan uwa da abokan arziki na daga cikin wadanda suka gaskata da lamarin.
A karshe
Rushewar kamfanoni irin su CBEX ba sabon abu ba ne, sai dai abun takaicin shi ne wata kila ba shi ne zai zama karshe ba. DUBAWA na kira ga masu zuba jari da dauki dabi’ar tantance abubuwa da zarar aka tuntube su da harkokin da suka shafi kudi. Irin wadannan abubuwan zamban sukan sami karfi ne idan har akwai rashin sani. Garkuwar kowa a nan ita ce tantancewa, ba fatan abubuwa za su yi kyau nan gaba ba.