African LanguagesFact CheckHausa

Karya ce! Hotunan da aka kirkiro da na’ura mai kwaikwayon dabi’un dan adam ne aka yi amfani da su wajen zargin cewa ‘yan arewa sun kai hari kan Inyamirai

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: wata mai amfani da shafin Facebook  ta wallafa wasu hotuna daban-daban ta na zargin wai Hausawa sun kai hari kan Inyamirai cikin wata kasuwa a yankin arewacin Najeriya dan rama abin da ya faru a jihar Edo

Karya ce! Hotunan da aka kirkiro da na’ura mai kwaikwayon dabi’un dan adam ne aka yi amfani da su wajen zargin cewa ‘yan arewa sun kai hari kan Inyamirai

Hukunci: KARYA CE KAWAI! Wasu hotuna biyu wadanda aka wallafa an kirkiro su ne da AI- wato na’ura mai kwaikwayon dabi’un dan adam, yayin da wasu biyu daga cikinsu kuma tsoffi ne tun a shekarar 2023 aka dauka.

Cikakken bayani

Ranar Juma’a 28 ga watan Maris 2025 ake zargin  mutane 16 sun hallaka a hannun mambobin wata kungiyar ‘yan banga ranar Alhamis a hedikwatar Karamar Hukumar Esan a jihar sakamakon zarginsu da aikata miyagun laifuka.

Bisa rahotannin da aka samu, mutanen na kan hanyarsu ta zuwa jihar Kano ne a cikin wata motar haya sadda masu tsaron suka dakatar da su. Bayan da suka yi musu bincike sun gano bindigogi a hannunsu, abin da ya sa suka kama su suka kuma dauki mataki a kan su. Bayan haka ne Comfort Ikechukwu a shafin All Nigeria Political parties ta,v wallafa wasu hotuna, ta na zargin wai al’ummar arwacin Najeriya ta kai hari kan Inyamurai.

A cikin bayanin wanda ta wallafa ranar 31 ga watan Maris 2025, Comfort ta yi da’awar cewa akalla Inyamirai shida sun hallaka yayin da wasu 10 kuma suka yi rauni bayan da wasu matasa Hausawa suka shiga wata kasuwar Inyamurai a arewa suna kai hari kan duk wadanda suka hadu da su a kan hanya.

Haka nan kuma ta kara da cewa mutane su tuntubi iyalansu domin ba wanda ya ga ‘yan sanda a wurin an neme su ma ba’a gan su ba, sa’anan su kansu maharan na kan hanyarsu ta zuwa wuraren da Inyamiran ke zama da nufin banka musu wuta.

“Shaidun gani da ido na kira da a kai dauki domin ba’a ga ‘yan sanda ba. Wani da aka zanta da shi ta wayar tarho ya ce ya ji karar harbin bindiga da ihun Inyamirai a wasu daga cikin wuraren da aka cinnawa wuta…” ta bayyana

Ana iya gani labarai makamantan wannan a  nan, nan, nan, nan, da nan.

Ganin yadda irin wannan bayanin ka iya haddasa rigima DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiyar lamarin.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da tantance mahimman kalmomi dangane da zargin harin amma ba ta sami labarin a shafin kafofin yada labarai masu nagarta ba.

Daga nan sai muka yi amfani da manhajar tantance hotuna ta image reverse search wanda ya bayyana mana mafarin hotunan da aka yi amfani da su a wannan shafin ranar 8 ga watan Satumban 2023. Hoton an dauko shi ne ainihi daga wani bidiyon da aka wallafa a shafin  ACI Africa kuma ya na nuna gidan fasto ne na cocin Katolika mai suna St. Raphael a Fadan Kamantan can a Dayosis na Kafanchan sadda ya ke cin wuta.

AI-generated old images used to depict attacks on Igbos in the North

Bacin haka, da muka yi amfani da manhajar daukar hoto ta Google Lensa kan daya daga cikin hotunan mun gano cewa tsohon hoto ne wanda aka yi amfani da shi ranar 11 ga watan Maris 2025, sadda wani tankin man fetur ya fashe a Legas.

AI-generated old images used to depict attacks on Igbos in the North

DUBAWA ta yi hasashen cewa sauran hotunan biyu da AI aka kirkiro su, dan haka ne ta yanke shawarar tantance su. Mun yi amfani da  Hive Moderation wanda ke tantance hotunan da aka kirkiro.  Daga nan ne muka tabbatar cewa an kirkiro su ne da AI,  inda sakamakon ya kasance kan  99.3% da 99.7%, cikin 199 bi da bi.

A Karshe

Wannan zargin karya ce kawai. Biyu daga cikin hotunan tsoffi ne a shekarar 2023 aka fara amfani da su yayin da sauran kuma ke dauke da hotunan da aka kirkiro da AI.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »