Rudolph Bropleh. Asalin hoton: Rudolph Bropleh
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Daya daga cikin masu sharhi a kan shirin na mai suna Spoon Talk na da’awar wai al’ummar Najeriya ta kai biliyan daya.

Hukunci: Karya ce. Shafin da ke kididdigar yawan al’ummar duniya na The World Population da wasu da dama masu nagarta na sa yawan al’ummar Najeriya a kan mutane miliyan 242.
Cikakken bayani
Wani malamin addinin Najeriya, Babatunde Ayodele, na cocin da aka fi sani da Inri Evangelical Spiritual Church, kwanan nan ya sanar da wani wahayin da ya yi dangane da Laberiya.
A bayanin da ya yi Primate Ayodele ya ce ukuba na jiran Laberiya domin gwamnatin ba ta shirya canjawa ba.
A cewarsa tattalin arzikin Laberiya na cikin wani yanayi na rudani kamar dai irin rudanin da shi kan sa shugaban kasar ke ciki. Wannan wahayin da ya ke da’awar yayi ta janyo cece-kuce daga ‘yan Laberiya da dama wadanda suka yi kira ga malamin addinin da ya mayar da hankali kan abubuwan da suka shafi kasarsa Najeriya.
Daya daga cikin wadanda suka ja hanlalin Ayodele kan wannan batun shi ma ya kasance a cikin wadanda suka yi tsokaci a shirin, mai suna Spoon Talk, inda ya ce ma sa tattalin arzikin Labreriya bai kai girman naNajeriya ba saboda al’ummar kasar ba ta da yawa. Daga nan neDr Rudolph Bropleh, ya ce al’ummar Najeriya ta kai kusan biliyan daya.
Bropleh ya tsinci alkaluman ne a tskanin wadannan mintocin wato daga 1:52:01 zuwa 1:52:08 na shirin, wanda mutane sama da dubu 58.1 suka kalla, wasu 3.7 suka yi tsokaci , sa’anan aka sami wasu 784 da suka yi ma’amala da labarin wasu 131 suka sake rabawa da jama’a.
Domin tabbacar da sahihancin bayanaia al’umma DUBAWA ta tantance wannan da’awar
Tantancewa
Rabon da Najeriya ta kididdiga al’ummarta tun shekara ta 2006. To sai dai bacin haka, kungiyoyi daban- daban wadanda suka hada da Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Lafiya ta Duniya duk sun bayyana alkaluman a matsayin kasa da abin da Dr Rudolph Bropleh ke da’awa.
Hukumar kididdiga ta Majalisar Dinkin Duniya na sa alkaluman a kan miliyan 237 a shekarar 2025.
Daga daya ga watan Janairun 2026 kasidar da ke bitar yawan al’ummar duniya ta sa adadin a kan miliyan 242, wanda shi kansa ya saba wa da’awar Dr Bropleh na biliyan daya.
Haka nan kuma ofishin kididdiga ta sa adadin a kan miliyan 250 daga bayanan da take samu na yawan al’ummar. Wannan bayanin na daga daya ga watan Yuli ne
A Karshe
Da’awar Rudolph Bropleh na cewa al’ummar Najeriya ta kai biliyan daya ba gasakiya ba ne
