Donald Trump,Shugaban Amurka. Asalin hoton: Facebook.
Da’awa: Wani bidiyon da ya shuhura a manhajar TikTok na da’awar wai shugaba Trump na Amurka ya kira Gambia kasar da ta tsere wa kowacce a nahiyar Afirka

Hukunci: Karya ce! Bidiyon TikTok na shugaba Trumo inda ya ke kiran Gambia kasar da ta fi kowacce a nahiyar Afirka da AI aka kirkira
Cikakken bayani
Focusonislama, wani mai amfani da shafin TikTok, kwanan nan ya wallafa bidiyon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya na sanar da Gambia a matsayin kasar da fi kowacce a nahiyar Afirka.
A cikin jawabin da ya yi bidiyon, Trump cewa ya yi, “Gambia ce kasar da ta fi kowacce a nahiyar Afirka domin al’ummarta na da kwanciyar hankali, ga kuma filaye masu ban sha’awa,da al’adu masu armashi. Kasa ce karama amma al’ummar na alfahari da kanta, sa’anan ga kyawawan albarkatu kamar rafin Gambia da kuma gabobin ruwan da ta mallaka.”
Daga 16 ga watan Yunin 2026, bayanin (Wanda aka adana a nan) na da alamar like sama da 6,000 tsokaci. Yayin da wadansu suka amince da abin da suka gani a bidiyon a matsayin gaskiya, wadansu sun yi shakkun sahihancin bidiyon suna kiran shi kirkira irin ta AI.
Alal misali, Mgspaklingclean cewa ya yi, “Trump bai ma san sunan Gambia ba.”
Wani shi ma mai amfani da shafin, Mujahidvillain, cewa ya yi, “ ya kan ba ni takaici sosai idan har na ga mutane ba su iya tantance bidiyon da aka yi da AI ba.”
Danni shi ma tsokaci makamancin haka ya yi, “Trump ba zai ce haka ba. Gambia ba ta da wani abin a zo a gani. Ya kamata su karanta abin da ya ke fada da baki.”
Sai dai Ft Tray bayyana amincewarsa ya yi, da cewa, “Ka na da gaskiya Mr President. Mun gode.”
DUBAWA ta gudanar da bincike dan fayyace gaskiya.
Tantancewa
Bayan da muka kalli bidiyon, mun kula cewa yanayin yadda Trump ke magana ya na motsa jikinsa duk ba su zo daidai da yadda baki?lappan sa ke motsi ba. Wannan babbar alama ce ta irin hotunan da aka kirkira da AI.
Dan haka mun yi amfani da manhajojin da ke tantance AI. Sakamakon da muka samu daga manhajar HiveModeration ya ba da tabbacin kashi 99.1bisa 100 na cewa da AI aka kirkiro shafin.
Wata manhajar ita ma wadda ake kira Zero GPT, ita ma ta bayar da tabbacin kashi 81 cikin 100 cewa bidiyon bog ne. Yayin da AI or Not ta nuna cewa kashi 33 AI sa’annan kashi 15 deepfake.

Sakamakon da muka samu daga shafukan tantance ko an yi amfani da AI.
Wadannan sakamakon sun bayyana cewa bidiyon na Trump ne sadda ya ke jawabi a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya kuma an gyara shi ne an dora wadannan maganganun na Gambia.
Bacin haka mun kuma yi amfani da manhajar tantance asalin hotuna na Google Reverse Image Search dan gano mafarin bidiyon. A nan ne muka gano cewa ainihin bidiyon an dauko shi ne daga shafin YouTube na Majalisar dinkin duniya. An nada an dora bidiyon ne sadda Trump ya gabatar da jawabinsa a taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 80 ranar 23 ga watan Satumban 2025 a birnin New York.

Donald Trump ya na jawabi a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya. Asalin hoton: YouTube.
Bidiyon na da tsawon minti 57, kuma inda aka tsakura ya fara ne daga minti 21:30 zuwa 21:50. A daidai wannan lokacin a bidiyon na ainihi, Trump na magana ne a kan niyyarsa na dakatar yake-yaken da ake yi a kasashen duniya, wanda ya hada har da irin “yunkurinsa na dakatar da yaki a kasar Ukraine.”
Ya ce ya kamata a ce an dakatar da yakin cikin ‘yan kwanaki kalilan amma kuma yanzu har ya kai shekaru uku da rabi. Ya ce wannan ya yi sanadin mace-mace a bangarorin biyu. Trump ya kuma yi bayani kan dakatar da yakin da bukatar tallafin masu ruwa da tsaki dan ganin hakan ya faru.
A Karshe
Bidiyon Trump na cewa Gambia ce kasar da ta fi kowacce a Afirka da AI aka kirkira. An kirkiro bidiyon ne ta yin amfani da bidiyon jawabin da Trump ya yi a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya a New York dan haka wannanda’awar karya ce kawai.
An hada wannan rahoton ne a karkashin tallafin horaswa na musammanna na tantance gaskiyar bayanai na Kwame Karikari da OSINT, tare da hadin gwiwar DUBAWA da Cibiyar nazarin fasahar da ke kwaikwayon dabi’un dan adam na AI da bayanan da ba daidai ba (DAIDAC) tare da tallafin Cibiyar Habbakawa da Koyon Sabbin Dabarun Aikin Jarida (CJID)
