PC: www.dataphyte.com
Binciken Zargin NNPCLs
Ranar daya ga watan Satumba, shugaban hukumar kwastam ya zargi NNPC da bayar da alkaluman bogi na yawan man fetir din da ake amfani da shi a kasa kowace rana. Ainihin abin da ya janyo wannan jayayya shi ne alkaluman da aka bayar na yawan man da ake amfani da shi kullun bai zo daidai da karuwar da ake samu a kudin tallafin ba. Watakila an yi ja-in-ja dangane da wanda ya kamata a baiwa laifin satar man da ake fama da shi amma alkaluman yawan man da ake amfani da shi kowace rana shi ne ummul-aba’isin kuma kan gaba a wannan takaddama.
An rawaito shugaban hukumar ta kwastam, Hammed Ali yana cewa “Na tuna a bara mun yi magana kan wannan (tallafi) abin takaici ne a ce a bana ma muna sake batun tallafin mai. Tiriliyan 11 da fiyen da za mu dauka a matsayin bashi na zaman fiye da rabin kudin da za’a bayar a matsayin tallafin man fetir. Matsalar ba fasa kwaurin kayayyakin man fetir din da ake yi ba ne. Na saba gardama da NNPC kan wannan batun, idan har muna mafani da lita miliyan 60 kowace rana, me ya sa za mu fitar da lita miliyan 98 a rana? Idan har kun tabbatar ga yawan da mu ke bukata dan me za ku fitar da adadin da ya gota abin da mu ke bukata?” shugaban na kwastam ya bayyana.
Da ta ke mayar da martani, hukumar ta NNPC ta kare adadin da ta bayar inda ta hakikance lita miliyan 68 ne ake bukata a kasar baki daya a maimakon miliyan 60 din da shugaban kwastam ke zargi, ta ma ce idan har ana ganin kamar karya ne ana iya zuwa a yi bincike a gani a tantance yawan man da ta ke fitar wa da ma yadda ta ke amfani da kudin tallafin da ake ba ta.
Hukumar man ta cigaba da cewa Nera 297 aka kashe a kan kowace lita a matsayin tallafin tsakanin watan Janairu zuwa Agustan 2022 sa’annan ta ce idan da babu tallafin da kowace litar mai za ta kasance Nera 462.
Ba shakka irin wannan labarin zai iya janyo wani yanayi na alhini da fargaba wanda zai iya haddasa hasashe iri-iri tsakanin ‘yan Najeriya wadanda da ma suna fama da hauhawar farashin kayayyakin masarufi. Batun cire tallafi zai kuma kara tsoratar da jama’a.
To amma ina aka kwana idan aka ajiye gardama da hasashe da ma duk wani cece-kuce da ake yi dangane da batun? Shin farashin man fetir zai kai Nera 462 idan har aka cire tallafi?
Yaya gaskiyar zargin da NNPC ta yi dangane da tallafin da ke kan kowace lita guda, kuma nawa zai kama a idan aka sanya tallafi a kan lita 60 ko 68 din da ake zargi ana amfani da shi kullun?
Zargin Farko: NNPC ta biya Nera 297 kan kowace litar mai a kan litoci miliyan 68 kowace rana tsakanin Janairu zuwa Agustan 2022
AMSA: Zargin wai ana sanya tallafin Nera 297 kan kowace litar mai ba gaskiya ba ne
Bisa bayanan kafofin yada labarai da yawa, Garbadeen MUhammad, mai magana da yawun NNPCL ya fitar da wata sanarwar da ta fayyace akalla nawa ake kashewa kan tallaffi kowace rana a kasar, inda ta ce Nera 297 kan kowace lita.
Duk da cewa babu wani bayani takamaimai na yadda NNPC ta kai ga samun wannan kudin da ta bayyana, a rahoton ta na FAAC na watan Agustan 2022, hukumar ta ce ta kashe Nera triliyan 2.458 a matsayin tallafi daga Janaru zuwa Agustan 2022.
Bitar da kamfanin Dataphyte ya yi ya nuna cewa kudin tallafin da aka bayar kan kowani lita ya bambanta amma ya kasance tsakanin Nera 99 zuwa 210 a watanni takwas din da suka yi wa bita, kan litoci miliyan 68 din da suka bayyana. Wanna ya kuma nuna cewa hukumar ba ta biya N297 ko sau daya a wannan lokacin kamar yadda ta ke zargin ta yi ba.
Da aka cigaba da yin bitar, an kuma gano cewa kudin da aka biya cikin wadannan watanni takwas ne ya kasance akalla N149.935 kan kowace lita a maimakon N297 din da suke bayyanawa.
Ko da ma an yi amfani da litoci miliyan 60 din da mahukuntan kwastam ke zargi babu yadda za’a yi a ce sun kashe N297 kan kowace lita. Lallai babu yadda za’a yi a ce sun kashe wannan kudin cikin watanni 8 domin idan har aka ce haka, ke nan Najeriya ta kashe fiye da Nera triliyan 2.485 a cikin wata 8 kadai.
Idan har aka yi lissafin kudin tallafin a kan litoci miliyan 68 din da hukumar NNPCL ta bayar da kuma bayanin da ake da shi na yawan kudaden da aka kashe cikin watanni takwas, ke nan mai yiwuwa Nera triliyan 3.721 ne kadai Najeriya za ta kashe kan tallafi a maimakoon Nera triliyan 6.5 din da NNPCL ke bukatar samu a matsayin kudin tallafin wannan shekarar.
Ko da ma litoci miliyan 60 ne kudin tallafin ba zai wuce Nera triliyan 3.721 ba.
Zargi na Biyu: NNPC na zargin wai idan aka hada duk kudaden da ake amfani da su wajen samar da man fetir dole a sayar da shi a kan Nera 462 kowace lita guda.
AMSA: Wannan zargin ba gaskiya ba ne, bincike ya karyata
Shin a halin da ake ciki yanzu farashin lita daya na mai za ta iya kaiwa Nera 462 idan babu tallafi? Nazarin da aka yi kan farashin man fetir idan babu tallafi ya nuna cewa farashin zai kasance tsakanin N264 da N377 tsakanin watan Janairu da Agustan 2022 da ba zai kai N462 ba.
Bayan haka, farashin zai kai N462 kowace lita kafin karshen shekarar ta 2022? Farashin mai a kasuwannin kasa da kasa ya fadi tun bayan da ya kai $122.7 a watan Yuni, idan har ya cigaba da faduwa haka, farashin ba zai kai N462 kan kowace lita ba a wannan shekarar (2022)
Zargi na Uku: Kasar na amfani da litoci miliyan 68 kowace rana
AMSA: Akwai alamar tambaya kan wannan zargin
NNPCL ta cigaba da kiyasta yawain man da kasa ke amfani da shi kullun a kan litoci miliyan 68 tana amfani da alkalumar da ta samu tsakanin watannin Janairu da Agusta.
Sai dai bitar da ta yi da kanta ta ya nuna cewa akwai abubuwan da dole za’a sanyawa alamar tambaya. Me ya sa? Bisa la’akari da cewa daga farkon wannan shekarar an yi fama da karancin man fetir na tsawon watanni hudu akalla inda aka rika samun dogon layi a gidajen mai, masu sayarwa a waje kuma suka yi riba domin sun saida man kusan Nera 550 kowace lita. Dan haka babu yadda za’a ce wannan bai yi tasiri a kan yawan man da ake zargi kasa na bukata kullun ba.
Karanci da ma alama ce da ke nuna rashin abin da ake nema, ganin cewa yawan tallafin da ake bayar wa ya danganci yawan man fetir din da kasa ke bukata, kamfanin bai bayar da cikakken bayani kan yadda karancin man ya yi tasiri kan yawan man da ake bukata kullun ba a lokacin da aka fiskanci karancin domin mutane ba su ma sami man sun saya ba.
Bisa la’akari da alkaluman da ke bayani kan tallafin man fetir a rahoton wata-wata na NNPC wanda ake kira FAAC report, da ma karin nazarin da Dataphyte ya yi, kasar ta yi amfani da litocin mai tsakanin miliyan 45.263 zuwa 96.554 kowace rana tsakanin watanin Janairu da Agustan 2022.
Litoci miliyan 68 din da aka ce NNPC ta bayar kiyasi ne kawai ba wai dai-dai yawan man da aka rika fitarwa kowace rana ba.
Dan haka, yawan man da Najeriya ke amfani da shi kullun ya danganci yawan da ake bukata ne kawai ba wai akwai wani adadi takamai-mai ba.
Yayin da ake cigaba da takaddama dangane da kudin tallafin man fetir din Najeriyar, ana cigaba da samun damuwa dangane da yiwuwar dorewar matakin, musamman yadda ya shafi yawan kudin da kasa ke samu dan gudanar da ayyukan da za su habaka tattalin arziki su kuma samar da cigaba.
