Zargi: Wani bidiyon da ke yawo na zargin Atiku na da babban gida a Hadaddiyar Daular Larabawa

Wannan zargin ba gaskiya ba ne. Binciken DUBAWA ya bayyana cewa ginin mallakar Tiger Group ne, wani kamfanin saye da sayar da gidaje da ke da mazaunin shi a Daular Larabawan. Ginin ba shi da wata alaka da dan takarar jam’iyyar PDP
Cikakken bayani
Kwanan nan wani bidiyon da aka yada a soshiyal mediya ya ke zarhin wau wani zaftareren ginin da aka gano a Hadaddiyar Daular Laraba ta dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar adawa ta PDP wato Atiku Abubakar ne ya mallaki ginin
Gajeren bidiyon ya nuna wani gini mai bisa sa’annan akwai muryar wata mace a cikin bidiyon tana wasu karin zarge-zargen kamar haka:
“Wannan ginin da ku ke gani a nan Dubai na Atiku Abubakar ne kuma abin takaicin shi ne babu dan Najeriyar da ake aiki a ciki. Babu shakka idan mu ka yi la’akari da wannan zamu fahimcin abin da Obasanjo ke nufi sadda ya ce kudin da Atiku ya sata lokacin suna gwamnati zai iya ciyar da ‘yan Najeriya sama da milliyan 400 na tsawon shekaru 400. Babu wanda zai iya mana rufa ido kuma. ‘Yan Najeriya mu zama masu hikima.
Wannan bidiyo dai ya yi yawo kuma mutane da yawa suna daukar shi a matsayin gaskiya shi ya sa muka dauki nauyin tantance gaskiyar wannan batun.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da yin bincike cikin google dan ganin ko Atiku na da kasaitaccen gini kamar yadda ake zargi a Dubai, sai dai babu wani bayanai takamaimai dangane da batun. Daga nan sai muka yi kokarin yin binciken kwa-kwaf kan hoton, amma nan ma ba mu yi nasara ba.
Sai muka yi binciken wani bangaren hoton da Google Lense wanda wata manhaja ce da ke baiwa mutun hikimar duba hoto ta yadda zai iya gano ko an dora wadansu hotunan ne na daban a kan wani hoton. Wannan ya gwada mana dai-dai wurin da aka dauki hoton, wato 898M+QW5-Al Majaz Al-Nahdha-Sharjah- United Arab Emirates(Hadaddiyar Daular Larabawa). Ginin yana kusa da wani shago mai suna Kitcherama Group wanda ke sayar da kayayyakin girke-girke da na sanyawa a Kitchen ko kuma dakin girke-girken.
Wajen kwatanta ginin, shafin google ya bayyana cewa ginin mallakar Tiger Group ne, wato wani kamfanin masu sana’ar saye da sayar da gidaje wadanda suka shahara a UAE suna kuma da ayyuka wajen sama da 200 da suka kammala a kasar. Kamfanin na karkashin jagorancin wani mai suna Injiniya Waleed Mohammad AlZoubi.
Baya ga haka, binciken mu ya nuna mana cewa ginin yana Sahrjah ne ba Dubai ba kamar yadda muryar da ke bayani a bidiyon ta yi zargi. Ita dai Sharjah tana zaman daya daga cikin dauloli bakwan da suka hadu suka zama Hadaddiyar Daular Larabawar.
A Karshe
Muna tabbatar da cewa wannan zargin karya ce domin binciken mu ya nuna mana cewa ginin mallakar kamfanin Tiger Group ce kuma ba ta da wata alaka ko dangantaka da Atiku Abubakar.