|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Shafin Facebook mai suna, Hausaland Magazine, (mujallar Hausaland) ta yi da’awar wai mazaunan karamar hukumar Kebbe da ke jihar sokoto sun hako gawawwakin wasu mata 37 wadanda ake zargi ‘yan bindigan Fulani suka hallaka.

Hukunci: Yaudara ce. Yayin da kafofin yada labarai masu nagarta suka yi labarin cewa an hallaka da dama a karamar hukumar Kebbe, ba su nuna cewa an hako gawawwakin wasu matan Hausawa 37 ba. Haka nan kuma rahotannin ba su ce wadanda aka hallakan mata ne ko Hausawa ba bare ma wai “‘yan bindigan Fulani” ne suka kashe su.
Cikakken bayani
Ranar Litinin 17 ga watan Agustan 2026, wani shafin Facebook mai suna Hausaland Magazine, ya yi da’awar cewa mazauna karamar hukumar Kebbe da ke jihar Sokoto sun hako gawawwakin wasu mata Hausawa su 37 wadanda ake kyautata zaton cewa “yan bindigan Fulani ne suka kashe su.
Shafin ya yi wannan da’awar ne a cikin wani labarin(da za ku iya gani a nan), da taken: “Abu mai ban tsoro a Sokoto: Mazauna sun hako gawawwakin matan Hausawa 37 wadanda mayakan Fulani suka kashe a karamar hukumar Kebbe. A cewar Iyalansu.”
Daga Laraba 19 ga watan Agusta mutane sama da 216 sun dannan alamar like, wasu 118 sun yi tsokaci yayin da wasu 192 kuma suka sake raba labarin.
Wannan da’awa dai ta dauki hankalin masu yawan tsokaci a shafin Facebook, inda wasu daga cikinsu ma suka rika fassara labarin a matsayin wata hujja ta kisar kabilanci har ma suka rika kira da a kai wani harin na ramako.
Kabiru Hamza cewa ya yi, “Hausawa, ya kamata mu hada kai kafin wadannan ‘yan bindigan su kashe mu duka, tilas ne kowannenmu ya bayar da gudunmawa wajen kare kai.”
Wani shi ma mai amfani da shafin, Ikechukwu Onyenacho, ya yi tambayar da ke neman sanin ko shin dokokin shari’a za su iya shawo kan rahsin tsawo a yankina Arewacin Najeriya, yayin da shi kuma Moses Eze ya ce, “ku yi dammara kawai Hausa, ku daina jiran majirata.”
Ganin yadda wannan da’awar ke da sarkakiya ta yadda za ta iya sanadin tashin hankali ne ya sa DUBAWA tantance sahihancin labarin.
Tantancewa
DUBAWA ta fari da binciken rahotanin da aka yi a kafofin yada labarai masu nagarta dan tantance ko an kashe mata, an bizine su kafin daga baya aka sake hako su daga kaburburan da aka sa su a can a karamar hukumar ta Kebbe da ke jihar Sokoto.
Wannan binciken ya tabbatar da cewa lallai ‘yan bindiga sun kai hari a wasu al’ummomin da ke karamar hukumar Kebbe kuma an hallaka da dama. To sai dai rahotannin ba su fayyace ko wadanda abin ya shafa mata ne kadai ba, ko ma wai su 37 ne. Haka nan kuma rahotannin ba su ce an rufe su kafin daga baya aka hako su ba.
Alal misali, jaridar Daily Trust, a rahoton da ta wallafa ranar 16 ga watan Agustan 2026, mai taken, ‘yan bindiga sun kai samame kan wasu al’ummomin jihar Sokoto sun kashe 32,” sun yi labarin cewa an kashe mutane 32 a al’ummar Ungushi da ke karamara hukumar Kebbe.
Bisa bayanan rahoton, mazauna sun ce maharan sun kai harin kansu ne yayain da suke sallar juma’a sa’annan bayan nan suka kutsa cikin garin baki daya suna harbi kan duk wadanda suka gani.
Wani daga cikin mazaunan wanda ya shaida lamarin da idonsa ya fadawa jaridar cewa maharan sun yi ta tafiya suna dawo wa suna kashe mutane kafin jami’an tsaro suka iso.
Rahoton ya ce sai ranar Lahadi mazauna suka iya komawa suka fara gano gawawwakin wadanda abin ya shafa.
Daily Trust ta rawaito mazaunan na cewa, “Yau wasu suna jana’izar wadanda aka samu yayin da wasu kuma suke yawon neman gawawwakin wadanda suka hallaka. Daga karshe dai mun gano gawawwaki 32.”
Haka nan kuma jaridar ta rawaito wani mazauni shi ma wanda ya san abubuwan da suka faru a lokacin ya na cewa mazaunan Ungushi baki daya sun tabbatar da kasancewar gawawwaki akalla 30, ko da shi ke ana iya sake gano wasu karin gawawwakin. Dan haka adadin wadanda suka hallakar ya banbanta ko a tsakanin mazaunan da ke labarin harin. Amma duk da haka, rahoton Daily Trust ya bayyana utane 32 ne kadai ba 37 ba.
Du da cewa wan labarin ya ce an gano gawawwaki kuma an binne su, babu wani bayanin da ya shafi hako gawawwaki.
DUBAWA ta kuma yi bitan rahoton da aka wallafa a shafin Legit.ng ranar 18 ga watan Agustan 2026, wanda shi kuma ya yi labarin cewa an kashe akalla mutane 28 a Ungushi. Rahoton ya bayyana wasu daga cikin wadanda suka hallaka, a cikinsu har da babban limamin masallacin juma’ar Izala da ke Ungushi, da Imam Aliyu da wasu manoma da ‘yan kasuwa da mazauna garin.
Rahoton ya ambato mai magana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Sokoto, DSP Ahmed Rufa’i ya na tabbatar da da adadin na cewa an gano akalla gawawwaki 28.
A nan ma babu labarin kisar wasu mata 37 wadanda aka rufe kafin aka sake hakowa.
Haka nan kuma kamfanin dillancin labaran Anadolu (AA) ta yi rahoton cewa ranar 18 ga watan Agustan 2026 an hallaka akalla mutane 28 a ciki har da Imam Aliyu da babban limamin masallacin juma’ar Izala da ke Ungushi.
AA ya kwatanta wadanda abin ya shafa a matsayin manoma, ‘yan kasuwa, malaman addini da sauran mazauna garin. Shi ma wannan rahoton bai yi batun hako wasu gawawwaki ba.
Duka rahotannin da muka yi bita sun tabbatar da afkuwar wannan harin mai muni a karamar hukumar Kebbe amma basu goyi bayan karin bayanin da aka yi a da’awar da aka wallafa a wannan shafin na Facebook ba.
Akwai kuma sabani a yanayin yadda aka kwatanta wadanda suka kai harin. Yayin da mujallar Hausaland ta ce maharan “‘yan bindigan Fulani ne”, rahotanni maus sahihancin da muka yi bita sun kira su ‘yan bindiga, da masu dammarar makamai da kuma ‘yan ta’addan da mai yiwuwa suke da alaka da kungiyar ‘yan ta’addar Lakurawa
Rahotannin dai sun tabbatar da afkuwar hari amma ba su ce Fulani ne maharan ba ko ma wadanda abin ya shafa Hausawa ne zalla.
A Karshe
Rahotanni masu sahihanci sun ce ‘yan bindiga sun kai hari a Ungushi da wadansu al’ummomin da ke karamar hukumar Kebbe a jihar Sokoto inda suka hallaka da dama. To sai dai rahotannin da muka yi bita basu ce matan Hausawa 37 na daga cikin gawawwakin da aka tsinta ba ko kuma an hako su daga kabarin da aka rufe su daga baya. Dan haka wannan da’awar yaudara ce kawai.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar Koyon Aikin Jarida da Kirkire-Kirkire da Ci-gaba (CJID) da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai ta EU.
