|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin X ya wallafa bidiyon da ke da’awar wai ‘yan bindiga ne ke daukar sabbin mambobi a Najeriya.

Hukunci: Babu Isashen Hujja. DUBAWA ba ta sami hujjojin da suka tabbatar cewa mutanen da ke cikin bidiyon mahara ne a Najeriya.
Cikakken bayani
Ranar 18 ga watan Agustan 2026 wani mai amfani da shafin X, wanda ma ya tantance shafinsa KILIYA (@musa_kiliya), ya wallafa bidiyon da ke nuna wasu mutane suna rarrafe cikin wani ramin yakin da aka rufe da itatuwa, a wani abin da ya yi kama da atisaye.
Mai amfani da shafin ya yi da’awar wai bidiyon na nuna yadda ake daukar sabbin mambobi ne a sansanin atisayen ‘yan bindiga a Najeriya.
Bidiyon (wanda za ku iya gani a nan) an yi masa taken, “‘Yan bindiga na daukar sabbin mambobi.”
Wasu daga cikin masu amfani da shafin sun dauki bidiyon a matsayin wata hujjar da ke nuna yadda kungiyoyin ‘yan bindiga ke daukar ma’aikata, yayin da wusu kuma suka nuna damuwarsu dangane da abin da wannan ke nufi ga yanayin tsaron kasar.
Wani mai amfani da shafin, Dawam Samson (@DawamSamson), ya ce, “Marabanku a Najeriya inda ‘yan bindiga ke gudanar da ayyukansu a bayyane ba tare da an dauki mataki a kan su ba.”
Abubakar A. A Zetariu (@tripleA) kuwa tambaya ce ya yi kan martanin sojojin Najeriya inda ya ce “Shin dakarun sojojon Najeriya ba su ganin wannan ne? Musamman sojojin sama?”
Shi kuma, Moustapharr (@MustapharNuura…) cewa ya yi “Hasbunallahu wani’imal wakil, wannan babban abin tsoro ne. Ya Allah, ga wargaza su ka kuma la’anta wadanda ke tallafa mu su da goya mu su baya.”
Sai dai, ISMAH@2013 (@ismah2013) ya yi shakkun sahihancin wannan da’awar inda ya “kun tabbata wannan Najeriya ce?”
Daga 20 ga watan Agustan 2026 mutane sama da 136,500 sun yi ma’amala da bidiyon, mutane 79 sun yi tsokaci yayinda wasu 246 suka sake wallafawa.
DUBAWA ta kuma gani wasu labaran masu kama da wannnan wadanda su ma ake yadawa a cikin shafin Facebook, a nan, nan, nan da nan.
Ganin yadda Najeriya ke cigaba da fama da kalubalen tsaro, musamman a yankin arewacin Najeriya da ma yadda mutane ka iya amfani da irin wannan labarin su hadasa rudani su kuma firgita al’umma ne ya sa DUBAWA tantance wannan labarin.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da tantance muhallin inda ake gudanar da atisayen. Na farko dai kamar dajin sahara ne dan haka muhallin na kama da yankin Sahel.
Haka nan kuma bidiyon ya nuna ‘yan bindiga ne ko kuma a ce wasu mayaka suna gudanar da atisaye, sai dai ba za’a iya tantance irin atisayen da ake yi ba ko ma takamaiman inda suke.
DUBAWA ta yi nazaren harshen da su ke amfani da shi cikin bidiyon inda ta gano cewa ba Hausa ba ne kuma ba Fulatanci ba ne, wadanda dai sune harsunan da aka fi amfani da su a yankin arewacin Najeriya.
Mun yi amfani da manhajar fassara ta Google Gemini dan fassara kadan daga cikin abubuwan da suke fada acikin bidiyon inda mu ka ga cewa larabci ne, musamman ma wani nau’i na irin larabcin da ake yi a Sudan ko Chadi.
Fassarar a turanci na cewa, “Come on, boy! Get in! Get inside! Get underneath! Come on! Crawl (stay low), hey! Hurry, hurry! Crawl here, crawl! Crawl! Keep your head down! Crawl! Low to the ground, boy, stay low! Fast, fast… stay low! Hey guys, come on quickly underneath!”
Wannan na nuna mana cewa bidiyon ya yi mafari daga wajen Najeriya ne.
DUBAWA ta kuma sake sanya bidiyon cikin manhajar tantance hotuna ta InVID dan cire mahimman hotuna a bidiyon a yi nazarinsu. Daga nan mun sanya mahimman hotunan da muka samu cikin manhajojin Google, TinEye da Yandex. Sai dai binciken da muka yi bai ba mu hujjoji masu kwarin da ke danganta bidiyon da mahara a Najeriya ba.
A Karshe
Yayin da bidiyon ke nuna atisaye, babu isashen hujjar da ke nuna cewa ‘yan bindigan Najeriya ne ke daukar sabbin mambobi kamar yadda ake da’awa.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar Koyon Aikin Jarida da Kirkire-Kirkire da Ci-gaba (CJID) da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai ta EU.
