Babu hujjar cewa bidiyon da ya kareda yanar gizo na nuna yadda mazauna jihar Zamfara ke kokarin tserewa daga mahara ne

Old abduction video involving Bello Turji recycled as recent incident
Getting your Trinity Audio player ready...
,

Da’awa: Wani BIG JOE OF LAGOS (@ JosephOnuorah) a shafin sa na X ya wallafa wani bidiyo da ya kai tsawon dakiku 38 inda yake nuna wasu mata, yara kanana da wasu mutane yayin da suke kokarin tsallaka wani rafi inda yake cewa mutanen mazaunan Birinin Magaji ne a jihar Zamfara sannan suna kokarin guje wa harin mahara ne.

Babu hujjar cewa bidiyon da ya kareda yanar gizo na nuna yadda mazauna jihar Zamfara ke kokarin tserewa daga mahara ne

Hukunci: Babu isasshen hujja. Tun a watan Yunin 2026 bidiyon ke yanar gizo kuma mun gaza tabbatar da harin da maharan suka kai wa kauyen Birinin Magaji dake jihar Zamfara.

Cikakken Labari

Kafaffen sada zumunta na yanar gizo sun ci gaba da zama hanyoyin yada labarai musamman labaran rashin tsaro. Sai dai yadda labaran ke yaduwa kan zama da wahala wajen iya gane labaran da ya faru a yanzu da wadanda suka dade.

A ranar Litini 24 ga watan Agusta 2026 wani BIG JOE OF LAGOS a shafin sa na X (@ JosephOnuorah) ya wallafa wani bidiyo mai tsawon sakan 38 inda ya nuna mutane da dama inda a ciki da mata da yara kanana yayin da suke kokarin tsallaka wani rafi. Da’awar da aka yi a bidiyon ya nuna cewa mutanen mazaunan kauyen Birnin Magaji ne dake jihar Zamfara yayin da suke kokarin guje wa harin mahara.

Da’awar ya kuma kara nuna cewa bayan hare-haren da mahara suka yi a  kauyen Birnin Magaji a jihar Zamfara mata da yara kanana na kokarin tsallaka wani rafi domin guje wa harin mahara. Shin menene Tinubu zai kara dawowa ya yi a Aso Rock?

A yanar gizo zuwa ranar 26 ga Agusta 2026 da’awar (da aka saka a nan) mutum 128,300 sun duba, 956 sun kara wallafa shi, 916 sun nuna suna so, 60 sun mai da martani da 84 sun saka alamar takarda.

Wasu a shafukan su na yanar gizo sun tattauna tabarbarewa tsaro, shugabanci a fannin siyasa da matakan da gwamnati ke dauka game da rashin tsaro.

Wani @Iam_Turnt22, ya yi tambayar cewa ko mutanen da abin ya shafa sun ga gwamnonin su na da dana yanzu. @akanjiabiodun01 ya zargi mazauna kauyuan da shugabanin su na siyasa wajen taimaka wa ‘yan ta’adda sannan @DaddyBKnK ya yi tambayar cewa menene ya sa mutanen ba su yi amfani da hanyar da shugaban kasa Bola Tinubu ya gina ba.

Bisa ga martanin da mutane suka yi game da bidiyon ya nuna cewa mutane na ganin lamarin da bidiyon ke nunawa lamari ne da ya faru a cikin kwanakin nan wanda hakan ya jawo ce-ce-ku-ce game da siyasa. A dalilin haka ya sa muka gudanar da bincike domin tabbatar da lokacin da aka dauki bidiyon da lamarin da yake nunawa.

Tantancewa 

DUBAWA domin tabbatar da cewa da bidiyon na nuna matsalar rashin tsaron da ake fama da shi a kauyen Birnin Magaji ya faru a cikin kwanakin nan ya sa ta yi amfani da na’urar ‘Google Lens’ domin tattance shi.

Sakamakon ya nuna cewa wannan bidiyo ya dade yana shawagi a yanar gizo kafin ranar 24 ga Agusta 2026.

Sakamakon ya nuna cewa wani Alhaji Ismail Salisu Adamu Tumfafi ya wallafa bidiyon a kafar Facebook ranar 4 ga Yuni 2026 sannan da da’awar da aka rubuta da Hausa “Innalillahi Wainna Ilaihirrajuun Wannan Wace Rayuwa ce”.

Da’awar ya bayyana da Turanci cewa wannan bidiyo ba na mutane bane dake shakatawa a bakin rafi ba amma bidiyo ne dake nuna yadda mutane ke kokarin tsira daga hare-haren mahara a Birnin Magaji jihar Zamfara. Ya nuna yadda mata da yara kanana ke sadaukar da ransu wajen mutuwa a ruwa domin gujewa harin mahara.

Sakamakon ya nuna cewa bidiyon ya yi tsawon kwanaki 81 yana shawagi a yana gizo kafin aka wallafa shi a X ranar 24 ga Agusta 2026. Amma wurin da lamarin ya faru wato kauyen Birnin Magaji dai-dai yake da wanda aka saka a watan Yuni wanda hakan ke nuna cewa bidiyon tsoho ne.

DUBAWA ta kuma gano bidiyon a YouTube a shafin @neptuneprimetv8957 inda suma suka wallafa wannan bidiyon a shafinsu ranar 6 ga Yuni 2026 da da’awar “mata, yara na guduwa daga wani kauye a jihar Zamfara a dalilin harin ‘yan bindiga”.

Bidiyon da aka saka ranar 6 ga Yuni ya nuna cewa bidiyon ya yi sama da tsawon watani biyu a yanar gizo kafin aka saka shi a X. 

Sakamakon binciken ya nuna cewa wani @secmxx a shafin sa na X ya wallafa wannan bidiyon a shafinsa ranar 2 ga watan Yuni 2026. Sannan ya sake saka wani bidiyo dake nuna wadannan rukunin mutane yayin da suke kokarin tsallaka rafi.

Da’awar da aka rubuta a bidiyon ya nuna cewa “mata da yara kanana na kokarin tsallaka rafi domin guje wa harin mahara a kauyen Birnin Magaji a jihar Zamfara jiya”.  Da’awar ya nuna cewa mutane na guje wa harin mahara daga kauyukan su domin rage yawan mace-mace da yin garkuwa da mutane da maharan ke yi.

DUBAWA ta kuma gudanar da bincike domin ganin ko akwai gidajen jaridun da suka wallafa labarin harin da mahara suka yi a kauyen Birinin Magaji yayin da bidiyon ke shawagi a yanar gizo a watan Yuni.

Gidan jaridar ta yi amfani da kalamai da suka hada da ‘Birnin Magaj’, ‘Zamfara’, ‘Harin mahara’, ‘mata da yara kanana na gudu’ da dai sauran su inda inda suka gano wani da’awar da Rundunar sojin Najeriya  da gidan jaridar News Africa, Ohamadike TV, da sauran su suka yi a shafin su na Facebook amma babu gidan jaridar da ta wallafa labarin harin.

Sakamakon binciken ya tabbatar cewa kafaffen sada zumunta na yanar gizo sun yi da’awa game da bidiyon wanda aka saka tun a watan Yuni amma duk da’awar da aka yi babu wanda ya tabbatar da lokacin da maharan suka kai wa wadannan mutane hari a jihar Zamfara.

A takaice dai bidiyon an saka shi a yanar gizo ne tun a watan Yunin 2026 sannan aka sake saka shi ranar 24 ga watan Agusta 2026.

A Karshe

Sakamakon da DUBAWA ta gudanar ya tabbatar da cewa bidiyon da BIG JOE OF LAGOS ya saka a matsayin sabuwan bidiyo dake nuna harin da mahara suka kai wa mutane a cikin kwanakin nan tsoho ne wanda tun a watan Yuni 2026 bidiyon ke shawagi a yanar gizo. Gidan jaridar ta kasa tabbatar da lokacin da harin ya faru.

Wannan bincike an gudanar da shi ne a karkashin shirin Cibiyar Bunkasa Aikin Jarida da Kirkire-kirkire (CJID) tare da tallafin Tarayyar Turai (European Union).