Yaudara ce kawai! Batun wai an karkata bayanin da kungiyar dattawan Arewa ta yi kan mallakar albarkun kasa.

Yaudara ce kawai! Batun wai an karkata bayanin da kungiyar dattawan Arewa ta yi kan mallakar albarkun kasa.
Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: (@calidvoiceeco) a shafinsa na Facebook ya wallafa wani bidiyo da ya nuna kakakin Kungiyar Dattawan Arewa NEF Abubakar Jiddere ya ce wai albarkun kasan dake arewacin Najeriya na mutanen arewacin Najeriya ne kadai kuma bai kamata sauran yankunan kasan ko jihohin kasan sun amfana da su ba.

Yaudara ce kawai! Batun wai an karkata bayanin da kungiyar dattawan Arewa ta yi kan mallakar albarkun kasa.

Hukunci: Yaudara ce! Ba mu gainda kakakin kungiyar NEF ta fadi haka ba.

Cikakken Labari

@calidvoiceeco a shafinsa na Facebook ya ce a wani bidiyo da ya (saka a nan) ya nuna cewa kakakin Kungiyar Dattawan Arewa Abubakar Jiddere ya ce duk albarkun kasan dake arewa na mutanen arewacin Najeriya ne kadai.

Bidiyon ya nuna hoton kakakin kungiyar NEF da dattawan Arewa tare da taken ‘dabobbi cikin sufar dan adam’ a dalilin wannan furucin da ake zargin sun yi.

An saka wadannan hotuna tare da bidiyon sannan da da’awar da ke cewa LABARAI DA DUMI-DUMI: Dattawan Arewa sun ce duk albarkun kasan dake Arewacin Najeriya na ‘yan arewa ne kadai, inda suke cewa bai kamata  sauran yankunan kasan ko jihohin su amfana da su ba.

Zuwa ranar 12 ga Agusta 2026 mutum 266,000 sun duba bidiyon, 2,900 suna son bidiyon, 852 sun kara wallafa bidiyon, 875 sun mai da martani, 207 sun ajiye bidyon.

Wani @Bala Maikarauka ya rubuta cewa “Wadannan ba dattawan arewa bane amma shugabanin Fulani ne da suke wakiltan kabilar su”.

Shi ma @polycarp sunday a martanin da ya maida ya ce “Ba dabobbi bane. Suna da masaniyar abin da suke yi tare da gwamnatin kasar Britaniya. Duk albarkun kasan dake jihohinsu sun zama nasu sannan man fetur din dake kudancin kasan na kowa da kowa ne. Wasu dai basa shan barasa amma suna buguwa daga barasan.

Tatancewa 

Sakamakon binciken da DUBAWA ta gudanar ya nuna cewa jaridar Guardian ta buga labari da aka wallafa a watan Janairu 2026 “NEF ta yi kira ga shugabanin Arewa da su yi magana kan masana’antar tace zinare”.

Rahotan ya nuna cewa kakakin kungiyar ya koka da yadda ake sace zinaren Najeriya a jihar Legas duk da cewa an hako shi daga yankin Arewacin Najeriya.

Ya ce ba kuskuren na kudurin da aka kafa bane sannan ba wai ba a sani bane amma da gangar ake yin haka domin kwace tattalin arzikin kasan.

“Hakan na kwace daraja daga hannun ‘yan arewa zuwa hannun wasu suka rika suka ci gaba wanda hakan ke kara matsaloli da suka hada da tallauci, rashin aikin yi da rashin tsaro a arewa.

Jaridar Punch ta rawaito cewa ‘Kungiyar Dattawan Arewa ta soki shirin aiyukkan tace zinare na Legas. A labaran da ta wallafa ranar22 ga Janairu 2026.

Bidiyon da aka saka a nan ya nuna bayyana abin da kakakin kungiyar ya fada a takardar da kungiyar ta fitar.

Kakakin ya yi tambayan cewa menene ya sa masana’antar da za ta tace zinaren da aka hako daga arewa za a kai shi jihar Legas inda yake cewa kamata ya yi arewa ta amfana wajen tace zinaren.

“Zinaren da muke da shi a arewa daban yake domin a  jihohin Zamfara, Kebbi, Neja, Kaduna haka kafa uku kadai ya isa a samu zinare.

Ya yi tambayan dalilin da ya sa ba za a gina matattar zinare a arewa ba sai dole a jihar Legas?.

Wannan martani da kakakin kungiyar NEF ya yi ya nuna cewa kungiyar na magana kan satan zinaren da ake k]hakowa ne daga arewa a jihar Legas amma ba magana kan mallaka ba kamar yadda aka ce wai ya fada.

Jaridar BusinessDay ta rawaito cewa maitaimakwa wa ministan albarkun kasa kan harkokin yada labarai SegunTomori ya ce ‘Dr Dele Alake bai ce Gwamnatin Tarayya ce ke da mallaka ko ta gina matattar zinaren dake jihar Legas ba. Matattar zinaren da ake magana akai fannin dake zaman kan ta ce ta gina shi sannan gwamnatin tarayya bata da ikon umartan fannin dake zaman kansa inda zai gudanar da kasuwancin sa ba.

Wani takarda da jaridar 21st Century Chronicles ya wallafa a watan Janairu 2026 ya nuna cewa kungiyar ta nisanta kanta daga martanin da ake cewa wai ta yi na cewa albarkin kasan arewa na mutane arewa ne kadai.

Sai dai kuma a 2025 jaridar Punch ta rawaito cewa kungiyar NEF ta ce akwai albarkun kasa 44 dake wurare 500 a Arewacin Najeriya sannan burin ta shine amfani da wadannan albarkun kasan domin samar da ci gaba a kasan amma ba ta mallake shi ba.

A Karshe

Kungiyar NEF ta soki gina matattar zinare a jihar Legas amma bata ce duk albarkun kasan dake Najeriya na mutane arewa ne kadai ba ko kuma mutanen dake arewa ne kadai ya kamata su amfana da albarkun kasan da ake hakowa daga arewa ba.

Wannan maganar yaudara ce kawai.

Wannan bincike an gudanar da shi ne a karkashin shirin Cibiyar Bunkasa Aikin Jarida da Kirkire-kirkire (CJID) tare da tallafin Tarayyar Turai (European Union).