Babu kwararan hujjojin da suka tabbatar da sahihancin bidiyon da ke da’awar wai mahara sun kashe kiristoci ‘yan gida daya, da ma wasu karin mutane a Najeriya

Video claiming gunmen killed entire Christian family, others in Nigeria unsubstantiated
Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani a shafinsa na Instagram ya wallafa wani bidiyo dake nuna cewa mayakan jihadi kuma ‘yan Fulani sun kashe wasu Kiristoci ‘yan gida daya tare da yin garkuwa da jarirai biyu.

Babu kwararan hujjojin da suka tabbatar da sahihancin bidiyon da ke da'awar wai mahara sun kashe kiristoci ‘yan gida daya, da ma wasu karin mutane a Najeriya

Hukunci: Babu isasshen hujja! Sakamakon binciken da muka gudanar ya nuna cewa an saka bidiyon tun a ranar 9 ga Yuni 2026 sannan babu kwararran hujojjin dake nuna alakan kawo harin da kisan Kirstoci ‘yan gida daya ba.

Cikakken Labari 

@_didier.neza a shafinsa na Instagram ya wallafa bidiyo a shafinsa da ya nuna cewa mayakan jihadi ‘yan Fulani sun kashe wasu Kiristoci ‘yan gida daya tare da yin garkuwa da jarirai biyu.

Bidiyon da ya kai tsawon sakan 58 ya nuna wasu mutane maza dauke da makamai yayin da suke awon gaba da jarirai biyu bayan sun kashe mutane da dama gawanwakinsu na kwance a kasa. Ana iya jin kukan jariran yayin da maharan ke tafiya da da su a kan babura.

A ranar 29 ga Agusta 2026 mutum 33,800 sun duba bidiyon, 1,600 na son bidiyon, 1,200 sun kara wallafa bidiyon, 522 sun mai da martani da 442 da suka kara wallafa bidiyon.

Mutanen da dama da suka kalli bidiyon sun amince da bidiyon.

@Uli_suedstadt ya ce “A bai wa Kiristoci makamai”.

@marjpacariem shima ya ce “Ubangiji Yesu ka ceci mutanen ka Amin!!!

@goose2436 ya ce “Muna nan zuwa domin ku”

Ganin ce-ce-ku cen da wannan bidiyo ya jawo da alamun yadda bidiyon ka iya tada rikicin adini ya sa DUBAWA ta gudanar da bincike.

Tantancewa 

Sakamakon binciken da DUBAWA ta gudanar ya taimaka wajen nuna asalin bidiyon wanda Tintini Tinti ya fara sakawa a shafinsa na Facebook ranar 9 ga Yuni 2026.

Sai dai kuma bidiyon farko da aka fara sakawa babu da’awar cewa mayakan jihadi ‘yan fulani sun kashe Kiristoci ‘yan gida daya ba.

Sannan wanda ya saka bidiyon bai fadi sunayen mutanen da aka kashe ba, wurin da kisan ya faru da ranar da abin ya faru ba.

DUBAWA ta gana da wnu bafulatani Modibbo Sani domin tabbatar da yaren da ake yi a bidiyon wanda shine ya fasara abin da ake fada a bidiyon.

“…Ndiyam yana nufin ruwa kenan. Sannan Chappan e nai e dido na nufin 42 wata killa suna irga gawawwakin mutanen da suka kashe”. In ji Sani.

DUBAWA ta yi amfani da na’uran ‘Google Earth’ domin gano inda aka yi kisan amma ta kasa.

Gidan jaridar ta yi kokarin gano rahotanin da gidajen jaridu suka fitar game da bidiyon amma bata ga ko daya ba.

A Karshe 

Abin da gidan jaridar ta gano shine bidiyon na yanan gizo tun a ranar 9 ga Yuni 2026 sannan babu kwararran hujojjin da suka tabbatar da wuri, ranan da kisan ya faru ko kamar yadda bidiyon ya nuna ya shafi Kiristoci ‘yan gida daya.

Wannan bincike an gudanar da shi ne a karkashin shirin Cibiyar Bunkasa Aikin Jarida da Kirkire-kirkire (CJID) tare da tallafin Tarayyar Turai (European Union).