Bidiyon da Gumi ke barazanar wai “zai rikita Najeria,” an gyara shi ne ta yadda zai yaudari jama’a

Video of Gumi threatening to “turn Nigeria upside down,” manipulated
Sheikh Ahmed Gumi. Hoto: ICIR Nigeria.
Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Napa Boy a shafinsa na Facebook ya wallafa wani bidiyo da ya nuna shahararren malami adinin musulunci da ke Kaduna Ahmad Gumi ya na barazanar rikirkita Najeriya idan har ba a yi komai game da aiyukkan ‘yan bindiga ba.

Bidiyon da Gumi ke barazanar wai "zai rikita Najeria," an gyara shi ne ta yadda zai yaudari jama'a

Hukunci: Karya ce! Bidiyon an canza shi domin a ainihin bidiyon Gumi bai fadi haka ba sannan shi kansa malamin ya musanta fadan hakan.

Cikakken Labari 

A ranar Juma’a 21 ga Agusta 2026 Napa Boy a shafinsa na Facebook ya wallafa wani bidiyo dake nuna Ahmad Gumi inda yake magana kan aiyukkan ‘yan bindiga inda har yake barazanar rikirkita Najeriya idan har ba a dauki mataki kan aiyukkan mahara ba.

Bidiyon da (aka saka a nan) da da’awar “Uban Ijele odene ku saurare shi”.

A ranar Juma’a 28 ga Agusta 2026 mutum 8,400 sun nuna shi’awar su da bidiyon, 1,400 sun mai da martani, 3,700 sun sake wallafa bidiyon, 1,000 sun saka alamar takarda.

Anthony Isaiah ya ce ‘Shine shugaban kasa?”

Anyagri Kande ya yi tambaya “Wannan mutumin yana nan yana shakan iskan ‘yanci? Idan har dai da gaske ne Najeriya ba da gaske take ba”.

Hon. Fidelis Nwachukwu ya rubuta cewa “A gode wa Allah cewa ya kira su mahara wanda hakan yake nuna cewa ba jahili bane”.

Tantancewa 

Dubawa ta gudanar da bincike kan bidiyon inda ta gano cewa bidiyon an canza shi. Bidiyon ya nuna wani dattijo dake sanye da tabarau da fararen kaya inda yayin da yake magana akwai hotan wani mutum sanye da tabarau da bakin hula. A bidiyon akwai wuraren da za a ga hotunan mahara dauke da makamai da hotunan wasu hadiman gwamnati.

Zuwa karshen bidiyon za a ga an nuno mutane da yawa a waje wanda hakan be nuna yadda aka yi amfani da dabaru da dama wajen canza bidiyon.

Datttijon dake sanye da tabarau da kansa da wurin da aka dauke shi yana magana basu canza ba amma sakamakon binciken da aka gudanar ya nuna banbanci a yadda bakinsa da sauran bangarorin jikinsa suke yayin da yake magana.

DUBAWA ta yi amfani da na’uran ‘Google’ domin tabbatar da inda aka samo bidiyon ko an yi wa bidiyon kwaskwarima musamman ta banganren da Gumi ke magana.

Gidan jaridar bata gano rahotani da gidajen jaridu suka fitar ba game da maganar da Gumi ya yi ba.

Daga nan DUBAWA ta yi amfani da dabarar Hive’s AI detection tool inda sakamakon ya nuna an yi amfani da AI kashi 0.8% sannan yayin da yake maganan sakamakon ya nuna an yi amfani da AI kashi 97.9%

Bidiyon da Gumi ke barazanar wai "zai rikita Najeria," an gyara shi ne ta yadda zai yaudari jama'a

DUBAWA ta yi amfani da  Zhuque AI Detector wanda ya nuna cewa akai alamin kashi 18.55% da ba a yi amfani da AI ba.

Video of Gumi threatening to “turn Nigeria upside down,” manipulated

Screenshot of Zhuque AI Detector’s analysis classifying the video as “Not likely to be AI-generated” with an AI probability of 18.55%.

An yi amfani da  VigilAI wanda ya nuna alamun kashi 85% na cewa bidiyon bogi ne.

Video of Gumi threatening to “turn Nigeria upside down,” manipulated

Screenshot of VigilAI’s analysis flagging the clip as a deepfake with an 85% deepfake chance and a 96% synth-signature match.

Sakamakon binciken da aka gudanar da dabarun AI guda uku ya nuna banbanci a hotuna da magana a bidiyon.

DUBAWA ta yi magana da Gumi ta wayar hannu inda Gumi ya musanta fadan hakan inda yake cewa karya ne kazafi ne kawai ake yi masa a yi watsi da su.

Ya ce abin yana kama da abin ban dariya musamman yadda ake nuna cewa ya ce zai kona kasan gaba daya.

Gumi ya ce shi dan Najeriya ne dake kishin kasan sa domin ya bauta wa kasar sa a matsayinsa na soja da likita inda yake cewa likita ba zai kona kasa ba.

Musun da Gumi ya yi ya zo dai-dai da sakamakon binciken da DUBAWA ta samu.

A Karshe 

Bidiyon da ya nuna Gumi na barazanar rikirkita kasar nan idan har ba da dauki mataki ba game da aiyukkan mahara ba karya ne. DUBAWA ba ta gano rahotanin da gidajen jaridu suka fitar ba wanda ya tabbatar da barazanar da Gumi ya yi ba sannan shi kansa Gumi ya musanta fadan magana irin haka.

Wannan bincike an gudanar da shi ne a karkashin shirin Cibiyar Bunkasa Aikin Jarida da Kirkire-kirkire (CJID) tare da tallafin Tarayyar Turai (European Union).