Getting your Trinity Audio player ready...
|
Cikakken bayani
A duk sadda ake magana dangane da matsaloli ko laluran da kan shafi kwakwalwa da cututtukan kwakwalwa a Najeriya, yawancin mutane sukan yi tunanin wadanda ke yawo a kan titi sakamakon tabin hankali, ko kuma neman dalilin kaucewa alhakin da ya rataya a wuyar ka. Sai dai lafiyar kwakwalwa wani babban bangare ne na rayuwarmu, kuma matsalolin da ke da nasaba da kwakwalwa ba sabon abu ba ne ana samun su a-kai-a kai, fiye da yadda muke tsammani.
Wadansu na iya fama da matsalar kwakwalwa ko kuma dai rashin lafiyar da ke da nasaba da kwakwalwa ba tare da saninsu ba saboda rshin sani ko kuma duhun kai. Bacin haka, wadansu kan yi amfani da kalaman bare da sun fahimci banbancin da ke tsakaninsu ba. Dan haka, daga karshen wannan bayanin, za ku fahimci ma’anar kowace kalma, da yadda ake amfani da ita sa’anan ku iya gane lokutan da mutane ke bukatar kula da kwakwalwarsu.
Mene ne Lafiyar Kwakwalwa?
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, lafiyar kwakwalwa ya kunshi yanayin lafiyar hankali da tunanin dan adam, wanda ke taimaka ma sa wajen shawo kan matsalolin rayuwa, da gano ire-iren abubuwan da suka iya da wadanda suke da kwarewa a cikinsu, ya koyi abu yadda ya kamata, ya yi aiki yadda ya kamata, ya kuma bayar da gudunmawa ga al’ummar da yake ciki.
Lafiyar kwakwalwa bangare ne na lafiyar dan adam da ke da mahimmanci sosai saboda yana tasiri kan yadda mutun ke yanke shawarwari, kulla dangantaka da tafiyar rayuwarmu ta yau da kullun. Hukumar WHO ta kwatanta lafiyar kwakwalwa a matsayin ‘yancin dan adam wanda ke da mahimmancin gaske ga cudanyar da mutun kan yi a al’umma da cigaban zamantakewa da tattalin arziki.
Yayin da wasu mutane ke kwatanta shi a matsayi wani yanayi wanda mutun ba shi da wata matsala ta rashin daidaito a yanayin hankali, fahimta da tunani, wato dai babu rashin lafiya, batun lafiyar kwakwalwa ya wuce nan. Wannan ya kasance haka ne saboda lamarin na tattare da sarkakiya kuma ya banbanta daga mutun zuwa mutun.
Bisa bayanan Cibiyar Shawo Kan Cututtuka wato CDC, lafiyar kwakwalwa ya hada har da lafiyar yanayin jin dadi ko ma rashin jin dadin dan adam, da yanayin zamantakewa wanda ke yawan tasiri a kan yadda mutane kan yi tunani, da yadda su kan ji da ma irin abubuwan da suke aikatawa.
Wani malami a fannin ilimin kwakwalwa kuma wadda ta girka gidauniyar Sandra Anyahaebi, lafiyar kwakwalwa ya kunshi lafiyar mutun baki daya kama daga ruhu zuwa jiki, har zuwa hanakli.
“Lafiyar kwakwalwa kalmomi ne da ke nufin lafiyar mutun baki daya wanda ya hada da ruhu, da jiki da hankali da komai da koai,” ta bayyana.
Wata mai kula da lafiyar kwakwalwar kuma wadda ke aiki wajen tabbatar da daidaito tsakanin jinsi da yanayin zamantakewar da ke tabbatar da hadin kai, Fimbiya Bitiyong ta ce lafiyar kwakwalwa lafiya hankali ne da yanayin jin dadin dan adam.
“Idan ana duba batun lafiyar kwakwalwa, ana la’akari ne da kiwon lafiyar mutun baki daya daga wanda ya shafi hankali zuwa zuciya. Kamar dai yadda aka tattauna lafiyar jiki ne inda ake la’akari da gabobin jiki. Dan haka lafiyar kwakwalwa ma yana la’akari da lafiyar hankali da na zuci, ke nan yadda mutun ke ji, domin su ne abubuwan da ya kamata a fi mayar da hankali a kansu.”
Mene ne rashin lafiyar kwakwalwa?
Ana iya fahimtar rashin lafiyar kwakwalwa bisa la’akari da wasu abubuwan da kan bayyana, wadanda suka hada da tunani mai mahimmanci, iya kama kai da halayya marasa tayar da hankali.
Yawanci, rashin lafiyar kwakwalwa ya kan zo da matsala sosai a yanayin da mutumin da abun ya shafa ke fahimtar abubuwa, ke iya shawo kan lamuran da suka shafi zuciya da kzma hali. Ya na da alaka da wahala ko nakasa a daya daga cikin manhimman gabobin da ke kula da hayyacin dan adam.
Ms Anyahaebi ta ce rashin lafiyar kwakwalwa ko kuma cututtukan kwakwalwa, matsalolin kwakwalwa ne da aka riga aka gano, yayin da yanayin kwakwalwa ke zaman alamun da ke da alaka da rashin lafiyar kwakwalwar da ba a riga an gane ba.
Ta yi bayanin cewa lafiyar kwakwalwa yawanci yana kan wani mizani ne, dan haka, mutun ba zai iya tashi daga wadanda ke da kwakwalwa mai lafiya zuwa mara lafiya ba ko kuma wanda ke da lalurar da za’a iya ganewa kai tsaye a kwakwalwa. Akwai dan tsakani, kuma wannan tsakanin ne kwararru a fannin ilimin kwakwalwar ne ke kira yanayin lafiyar kwakwalwa.
“Yawanci ana iya gane rashin lafiyar kwakwalwa. Dan haka ana iya amfani da sunayen biyu wato rashin lafiyar kwakwalwa da tabin hankali. Amma idan har ana so a banbanta tsakaninsu, rashin lafiyar kwakwalwa da tabin hankali yawanci akan gane su a fahimce su nan da nan a kimiyance wadanda kuma yawancin likitocin kwakwalwar sukan yi amfani da su wajen fahimtar sauran kananan matsalolin kwakwalwar da za’a iya dangantawa da wadanda aka riga aka gane.
“Misali, idan mutun na fama da damuwar da ke tasiri a kan aikin da ya ke yi, da dangantakarsa da mutane da sauran su, wasu na iya kiran wannan yanayin lafiyar kwakwalwa, amma da gaske ne ana iya amfani da duka biyun wajen kwatanta abu daya. Tabin hankali da rashin daidaiton kwakwalwa na nufin yanayi ko kuma cututtukan da ke da nasaba da kwakwalwa, wadanda kwararru za su iya ganewa, yayin da yanayin kwakwalwa ya ke tsaka-tsaki wato inda mutun ke samun alamun matsala da kwakwala amma ba’a kai ga fahimtar ko mene ne ba.
“Idan mutun na samun matsala wajen cin abinci, da bacci da ma da laulayi, ana iya cewa alamun na nuna abin da ke da nasaba da kwakwalwa.. Abun da ya sa suke cewa haka shi ne dan ba’a kai ga tantance matsalar ko cutar ba. Amma idan har aka gane abin da ke damun mutun misali kamar damuwa, ko kuma bipolar – wanda matsanancin damuwa ne da ke kawo sauyi a yanayi ko halayyar mutun ta yadda ba zai iya yin abubuwan da ya saba yi na yau da kullun ba – da suaransu. A wannan lokacin ana iya cewa mutun na fama da tabin hankali ko kuma rashin daidaito a kwakwalwa.
Madam Bitiyong ta kuma amince cewa ana iya amfani da bayanan biyu dan kwatanta abu daya. Sai dai ta ce abun da ya kamata a yi la’akari da shi idan ana maganan yanayin kwakwalwa shi ne dole sai akwai damuwa a ciki.
Ta yi bayanin cewa yawancin nau’o’in wadanda suka hada da damuwa da bipolar da schizophrenia – inda mutun ya kan gaza banbanta tsakanin abun da ke faruwa a zahiri da abun da ya ke gani shi kadai a kansu — duk sukan kasance a karkashin tabin hankali ne.
“Idan muna maganan rashin daidaito na kwakwalwa, wannan shi ne sadda hankali da tunanin mutun suka fuskantar kalubale ta yadda mutun zai rika yin abubuwa kusan kamar ba a cikin hayyacinsa ya ke ba.”
“Akwai wasu abubuwan da sukan rikita lafiyar kwakwalwa na wani gajeren lokaci, misali idan mutun na jimami. Na wani gajeren lokaci mutun na iya fuskantar damuwa da tashin hankali. Duk da haka wannan bai kai a kira shi tabin hankali ba tunda na wani gajeren lokaci ne. Amma idan mu ka fara ganin abubuwa kamar Down Syndrome — wanda wani yanayi ne da ake haifar mutun da shi, inda yawan kwayoyin halittar da ya kamata a ce yana da shi ya gota da guda daya wanda yawanci ya kan hana shi rayuwa kamar wadda ke da daidai yawan da ya kamata. Sai kuma Asperger — wanda shi ma a kan haifi mutun da shi ne amma ya fi tasiri a kan halayya da tunani, inda yawanci su kan yi ta maimaita abubuwa kuma ba su san sauyi, muna iya cewa wadannan rashin daidaito ne a kwakwalwa tun da su dindindin ne ba wai suna tafiya bayan wani tsawon lokaci ba.”
A shekarar 2019, Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa mutun daya cikin kowani mutane takwas na fama da wani nau’in matsala na kwakwalwa. Misalan sun hada da fargaba, damuwa, matsalar cin abinci, schizophrenia, Bipolar, PTSD – (wanda matsananciyar damuwa ce da kan addabi mutun bayan ya ga wani abun da ya tayar mi shi da hankali matuka ko kuma ya wahalar da shi misali mutun da je yaki) halayan da suka fita sigar abubuwan da al’ummar ta amince da su, rashin son shiga mutane, yawan fargaba, tsoron wani abu, fargabar shiga cikin al’umma, daukar abubuwan da basu taka kara sun karya ba da mahimmancin gaske cikin wani yanayi na damuwa da matsin lamba, da dai sauran abubuwan da ke da nasaba da kwakwalwa.
Duk da cewa ana yawan kiran rashin daidaito a kwakwalwa tabin hankali, idan aka ce rashin daidaito, yawanci ya kan kunshi nau’o’in abubuwa da yawa da ke da nasaba da kwakwalwa.
Wadanne nau’o’i ne ake kira yanayin lafiyar kwakwalwa?
Yanayin lafiyar kwakwalwa yana iya nufin nau’o’i da yawa na matsalolin da ke da nasaba da kwakwalwa, da kalubale wajen amfani da kwakwalwa da dai sauran abubuwan da kan kawo matukar damuwa ko illoli da abubuwan da ke janyi hadarin yiwuwar raunata kai.
Kuna iya samun ciakken jaddawalin sunayen abubuwan da ake kira yanayin lafiyar kwakwalwa a a cibiyar lafiyar kwakwalwa ta Amurka a nan
Madam Bitiyong ta kuma kwatanta yanayin lafiyar kwakwalwa a matsayin yanayin lafiyar dan adam ko da yana fuskantar kalubake ko kuwa a’a.
“Yanayin kwakwalwa na da nasaba da yanayin lafiyar dan adam baki daya. Ba wai rashin daidaito ne ko cuta ba. Yanayin lafiyar jikin dan adam ne kadai. Yana iya kasancewa ko jikin na da lafiya ko ba shi da shi.”
Wa ke da hadarin kamuwa da matsalar kwakwalwa?
Wannan ya danganci abubuwa da yawa. Kowani mutun, a kowani lokaci na iya fuskantar matsalar kwakwalwa. Akwai abubuwa da yawa a tsarin ginin jikin mutun wadanda watakila ya samu daga dangi, ko al’ummar da yake rayuwa da ma sauran sigogin da kan taru su kare lafiyar mutun ko kuma su ba shi rashin lafiya.
Yayin da wasu suke da jimirin irin wadannan abubuwan, duk wadanda suka samu kansu a yanayi mai tsauri kamar talauci, tashin hankali, nakasa da rashin daidaito sun fi samun kansu cikin hadari mafi muni. Lafiyar kwakwalwa da abubuwan da ke da nasaba da halittun da ke kewaye da mu, kamar kwayoyin halitta, da basirar sanin yadda za’a tinkari abubuwa masu sosa rai ka iya ragewa ko kuma kara hadarrurrukan.
Me ke janyo matsalolin kwakwalwa?
Ko wani dan adam kan fuskanci matakai daban-dabanna rayuwa, kuma duk abubuwna da aka fuskanta a kowane mataki kan yi tasiri a kan lafiyar kwakwalwar mutun.
Wata dangantaka mai sarkakiya tsakanin, mutun, da yanayin zamantakewa , matsalolin da kan zo da tsarin rayuwar da mtun ke ciki da raunin da ya ke da shi duk su ne suke tasiri kan irin lafiyar kwakwalwar da kowan dan adam ke da shi. Alal misali, yanayin kwakwalwar mutun da abubuwan da ke da nasaba da yanayin ko tsarin yadda muke amfani da halittun da muke kewaye da su, kamar yadda mu ke ma’amala da mutane a batutuwan da suka shafi zuciya, da kwayoyin da muke amfani da su da kwayoyin halittan da aka haife mu da su, duk suna iya hadasa matsalolin kwakwalwa.
Rayuwa cikin yanayin zamantakewa, tattalin ariziki, siyasar yanki da yanayin muhalli kamar talauci, tashin hankali, rashin daidaito da karancin muhalli mai inganci su ma duk suna iya kara hadarin kamuwa da matsalolin kwakwalwa.
Wadannan abubuwan suna iya bayyana a kusan kowani matakin rayuwar dan adam, amma wadanda sukan bayyana a shekarun farko na rayuwar dan adam sun fi kasancewa da matsala. Misali, iyaye masu yawan tsawata yaransu, duka ko cin zarafi ta hanyar cin karfin yaro da azabtarwa su kan kasance kalubale ga lafiyar kananan yara, domin zalunci na daya daga cikin abubuwna da suka fi janyo matsalar kwakwalwa a yara.
Abubuwan da ke kawo kariya ma su kan afku a rayuwar mutun wadanda su ne ma sukan taimaka wajen tabbatar da juriya, da karfin iya shawo kan matsaloli masu kaifin gaske. Wadannan abubuwan sun hada da kwarewa a fannin zamantakewa wajen iya zama da mutane da hulda da su da kuma halayya wato kyawawan halaye, dangantaka nagari, ilimi mai inganci, aikin yi mai kyau, ungwanni masu kariya da kyakyawar alaka ko kuma dankon zumunta tsakanin mutanen da ke rayuwa a al’umma daya, da dai sauransu.
Kula da lafiyar kwakwalwa
Akwai wuraren da aka samar musamman dan kula da lafiyar kwakwalwar mutane ko kuma dai duk wata cuta da ke da nasaba da kwakwalwa.
Kamata ya yi a yi nazarin duk wata matsala ta kwakwalwa daga tushe, kuma wannan nauyi ne da ya rataya a kan kowa, kama daga gwamnati zuwa al’umma. Ya na da mahimmanci a nemi hanyoyin biyan bukatun mutanen da ke fama da matsalolin da ke da nasaba da kwakwalwa.
Kula da lafiya ya shafi kusan kowani fanni, kama daga kananan hukumomi har zuwa manyan asibitocin da ke kula da lafiyar kwakwalwar. Ya kamata duk ayyukan da aka shirya dan kula da lafiyar kwakwalwar mutane ya kamata a hada su da ayyukan kiwon lafiyar da ake wa kowa da kowa. Kuma ta hanyar raba ayyukan yi wadanda ba kwararru a fannin ba za su sami damar bayar da gudunmawarsu wajen inganta lafiyar wadanda ke bukatar taimako musamman wajen kare kananan yara, kiwon lafiyar makarantu da kurkuku.
A Karshe
Kula da lafiyar kwakwalwa yana da mahimmanci sosai. Dan haka a yunkurin da kasa ke yi wajen inganta lafiyar kwakwalwar al’umma, yana da mahimmanci a ce an biya duk bukatun wadanda ke fama da kalubalen da ke da nasaba da lafiyar kwakwalwa.