|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook ya yada wani bidiyo inda ya nuna wasu mutane a wani waje mai kama da sahara, yayi da’awar cewa ‘yanfashin daji ne ya kuma yi kira ga ‘yansanda su bibiye su.

Hukunci: Karya ce. Shedu sun nuna cewa wannan bidiyo na da alaka ne da sojojin Rapid Support Forces (RSF) a kasar Sudan.
Cikakken Labarin
Yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar tarin kalubale, rahotanni na masu fashin daji na cigaba da yaduwa cikin sauri tun kafin ma mutane su bincika su tabbatar da abubuwan da ake fadi bisa kafa hujja da shedu.
Sau tari tsaffin bayanai ana iya ganin suna sake bayyana a matsayin labarai da dumi-duminsu da basu da wata alaka da bidiyon sai a dauki bayanan akai su wani waje.
A baya-bayan nan wani mai amfani da shafin Facebook mai suna mc ese jomo, ya yada wani bidiyo da aka alkinta shi (nan) inda aka nuna sojoji dauke da makamai ake cewa mayakan sakai ne masu dauke da makamai. Yayi kira ga jami’an ‘yansanda a Najeriya da su bibiyi wadannan ‘yanfashin daji da aka nuna a bidiyon.
Bidiyon mai tsawon dakika 54, ya nuna yadda wadannan mutane ke tafiya suna magana a wani harshe da ba a san wane harshe ba ne.
A daya bangaren biyon da aka raba gida biyu, mutum na magana a dangane da wannan bidiyo. Yace “Ogogi ‘yansanda na dauka kuna fadin cewa kuna da na’urar gano masu yin bidiyo da ake yadawa to ga wasu ‘yanfashin daji suna daukar hotunan kansu a kokarta a gano inda suke.”
Ya zuwa ranar 21 ga watan Afrilu, 2026, da aka ga wannan wallafa ta samu wadanda suke nuna sha’awarsu 1,200 da masu tsokaci 1,15 da wadanda suka sake yada wannan bidiyo 425 da wadanda suka kalla sama da mutane 5,000.
DUBAWA ta nazarci tsokacin da ake yi, ta fahimci abin da dama masu amfani da shafin ke tunani a dangane da wannan da’awa.
@Liz Achonwu yayi martani da cewa, “Zauna kana jiran ‘yansanda, babu abin da zai faru, a karshe dai abin da za su iya yi shine su zo suna fadawa mutane labarai na karya.”
@Arikya S. Man yace “Amma Malam wannan ba Najeriya ba ce.”
@Anasko Anasko yayi nasa tsokaci da cewa, “Abokina kana batawa kanka lokaci ne, ba za su gano inda suke ba kasancewar ‘yanfashin dajin da mahukunta a kasar suna da alaka ta kusa.”
Wannan bidiyo babu bayanai sosai a dangane da asalin inda ya fito, wasu daga cikin masu amfani da shafin sun bayyana mabanbantan ra’ayoyi, ciki kuwa har da masu cewa wannan bidiyo ba a Najeriya ba ne.Wannan ya sanya DUBAWA ganin dacewar gudanar da bincike kan wannan lamari.
Tantancewa
DUBAWA ta raba bidiyo inda ta nazarce shi ta hanyar amfani da manhajar InVID ta gudanar da bincike.Mun gano rahotanni da suka bayyana masu dauke da makaman a matsayin mambobi daga sojojin Rapid Support Forces (RSF).
Rahotannin da muka nazarta mun ga cewa an wallafa su a harshen Turkish a kafar Tamaturk, wacce ta alaka bidiyon da tashin hankali da ake ciki a yankin El Fasher da ke cikin yankin Darfur. Mutanen da ake gani a bidiyon mambobi ne na mayakan RSF lokacin da suke murna bayan cimma nasara a wata fafatawa da aka yi da su.
Duk da cewa sun sanya kaya mabanbanta, mun kwatanta su da irin kayan da dakarun na RSF ke sawa.Duk da cewa wannan bidiyo na mai da’awar bai fita da kyau ba, akwai wasu alamu da suka nuna akwai kamanceceniya. Dakarun na RSF babu wasu kaya da za a ce su kadai suke sawa saboda akwai wasu hotunan da su ma sun tabbatar da hakan.
Hoto daga shafin Facebook da aka wallafa (Hagu), tare da wasu hotunan da suke nuna dakarun na RSF da wasu kayan da ke zama mabanbanta (dama).
Kasancewar ana jiyo muryoyi a cikin bidiyon sannan wasu shedu da ake da su sun tabbatar da cewa na ‘yanSudan ne da dakarun na RSF, DUBAWA ta nemi shigar masana don jin ta bakinsu a dangane da wannan harshe da ake magana da shi.
Mun tuntubi Abdallah Hussein, wani dankasar ta Sudan, sai dai bamu samu amsa daga gare shi ba kasancewar bai amsa sako da aka aika masa ba.Sai muka tuntubi Musa Salihu malami a jami’ar Tarayya ta Kashere wanda ke da masaniya kan banbance da ke akwai a dangane da harshen Larabci (Arabic) a wannan yanki.
A cewarsa harshen da ake magana da shi a bidiyon harshen Larabci ne wanda a ko da yaushe sojojin na RSF ke amfani da shi, sai dai ya lura cewa harshen na dan sauyawa saboda kebanta da wani yanki, kuma mutanen da ke wajen suna cikin yanayi ne na murna.
DUBAWA ta kuma gano cewa babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta fitar da rahoton ko ta alakanta wannan bidiyo ga Najeriya ko ‘yanfashin dajin.
A karshe
Wannan bidiyo bai nuna cewa mayakan ‘yanfashin daji ne a Najeriya ba. Shedu sun tabbatar da cewa dakaru ne na mayakan na Rapid Support Forces (RSF)da ke Sudan. Wannan da’awa don haka karya ce.
