|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da Facebook ya wallafa wani bidiyo da ke nuna wani jagoran masu fareti na rera cewa a bashi bindigar AK-47 domin kai hari kan Kiristoci a majami’unsu na Enugu da Jos.

Hukunci: Gaskiya ne. Bidiyon da ke yawo a yanar gizo na gaske ne kuma ba ƙirƙirarre ba ne. Shugaban ƙungiyar Izala ya tabbatar da ingancin bidiyon, inda ya yi alawadai da lamarin sannan ya yi kiran da a kama tare da gurfanar da duk waɗanda ke da hannu a ciki.
Cikakken Bayani
Wani mai amfani da Facebook mai suna Masara Kim Usman, ya yaɗa wani bidiyo da ke nuna mambobin ƙungiyar Agaji ta Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) suna gudanar da faretin motsa jiki tare da rera waƙoƙin amfani da kalamai na barazanar tsaro.
Sakon da aka gani tare da bidiyon yana cewa, “Wani mai tsatstsauran ra’ayi a Najeriya yana jagorantar faretin ‘yan agajin Musulmi suna kiran ‘A ba ni AK47 domin in shiga cikin arna a Jos, da kuma Enugu a ranar Lahadi in ba su wuta yayin da suke bauta.”
A cikin bidiyon (an adana a nan), wani jagora sanye da tufafin ƙungiyar Agaji ta JIBWIS yana jagorantar samari da ƙananan yara yayin gudanar da faretin.
Jagoran, wanda yake magana da harshen Hausa, ya nemi a ba shi bindigar AK-47 domin ya tafi Enugu da Jos don kai hari kan Kiristoci yayin da suke gudanar da bauta a majami’u a ranakun Lahadi, yayin da mambobin ke amsa waƙar.
Kalaman na cewa, “A ba ni AK!… Na je Enugu!… Cikin arna!… Ran Sunday!… Suna murna!… Suna taɓi!… Na ba su wuta!… Ru-du, ru-du-du!… Na je can Jos!”
Wannan sako da bidiyon sun janyo fushi, damuwa, da maganganu da dama a kafafen sada zumunta, inda mutane da yawa ke kira ga jami’an tsaro su shigo tsakani saboda kalaman ke nuna tunzura jama’a zuwa ga rikicin addini.
Ƙungiyar kare hakƙin ɗan adam ta Amnesty International reshen Najeriya ta buƙaci hukumomi da su binciki bidiyon da ke tunzura jama’a.
Dubawa ma ta sami buƙatu da dama daga mutane don tantance gaskiyar bidiyon.
Muna samun bidiyoyi masu kama da wannan suna yawo a dandalin Facebook, Instagram, X (Twitter), da TikTok.
Ganin yadda da’awar ta yaɗu cikin sauri da kuma yuwuwar barazanar addini ta haifar da rigimar addinin jama’a a faɗin ƙasar, DUBAWA ta gudanar da bincike don tabbatar da ingancin bidiyon.
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da bincike kan bidiyon. Binciken gani da ido bai nuna wata alamar ƙirƙira ta AI, alamar bogi, ko haɗa sauti da hoto ta hanya mai cutarwa ba.
Haka kuma mun lura cewa mutanen da ke cikin bidiyon suna sanye da rigunan ƙungiyar Agaji ta JIBWIS (Yan Agaji).

Hoton bidiyon da ke yawo idan aka kwatanta shi da mambobin Yan Agaji.
Don tabbatar da abin da muka lura, mun yi amfani da manhajar tantancewa ta Google SynthID. Na’urar ba ta gano wata shaidar ƙirƙira ko tambarin bogi na fasaha ba.

Sakamakon SynthID.
Mun kuma yi amfani da na’urar Hive AI wajen bincikar bidiyon, wanda shi ma ya tabbatar da cewa bidiyon na gaske ne ba ƙirƙirarre ba.

Sakamakon Hive AI.
Sannan mun gudanar da binciken hoto wanda ya nuna cewa bidiyon ya fara yawo ne a kafafen sadarwa a ranar 26 ga Oktoba, 2026, kamar yadda aka gani nan, nan, nan, da nan.
DUBAWA ba ta sami damar tabbatar da ko taron na ɓangaren JIBWIS na Jos ne (ƙarƙashin jagorancin Sani Yahaya) ko kuwa ɓangaren Kaduna ne (ƙarƙashin jagorancin Abdullahi Bala) ba, ko kuma ko mahalarta taron mambobi ne masu rajista na ƙungiyar da aka ba wa izinin yin hakan.
Sakamakon binciken kalmomi da muka yi, ya kai mu ga wata sanarwa da sakatariyar JIBWIS ta Najeriya ta fitar. Sanarwar, wacce shugaban ƙungiyar na ƙasa, Abdullahi Bala ya sanya wa hannu, ta yi alawadai da tunzura jama’a sannan ta buƙaci a gaggauta kama tare da bincikar mutumin da ke cikin bidiyon.
Ya ce, “Irin waɗannan kalaman nuna ƙarfi, firgitarwa, da barazana ga wata al’umma ba su da alaƙa ko kaɗan da ka’idoji, koyarwa, da manufofin da aka kafa ƙungiyar a kansu.”
Shugaban ya jaddada cewa sanya rigar ƙungiyar Agaji ta JIBWIS ko kasancewa a cikin mambobinta ba ya nufin cewa mutum yana wakiltar ƙungiyar ko yana aikata abin da ƙungiyar ta ba shi dama ya aikata ba.
Ya ƙara da cewa amfani da irin wannan damar zai iya kasancewa wani yunkuri ne na dai-daiku ko mutanen da ke waje don ɓata sunan ƙungiyar.
A Ƙarshe
Bidiyon da ke yawo da ke nuna wani sanye da kayan ƙungiyar Agaji ta JIBWIS yana rera waƙa da kiran a ba shi bindigar AK-47 don kai hari kan Kiristoci a Enugu da Jos gaskiya ne.
