|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook ya yada wani bidiyo da ke nuna yadda sojoji ke bincikar wani mutum inda yayi da’awar cewa an dauki bidiyon ne a Najeriya.

Hukunci: Yaudara ce. Bincike da DUBAWA ta gudanar ya nuna cewa bidiyon na da alaka ne da kasar Sudan ba Najeriya ba.
Cikakken Labarin
A ranar 15 ga Satumba,2026 wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Lucky Okechukwu Biafra, ya yada bidiyo kamar yadda aka (alkinta nan) yana nuna mutane sanye da kakin soja suna bincikar wani mutum da za a iya cewa fararhula ne. Hotuna ne guda biyu aka jera daya daga sama hannun dama daya kasa hannun hagu.
Hato na farko ya nuna bayani daga Garba Shehu na cewa ‘Boko Haram da Fulani masu fashin daji masu fafutuka ne na ‘yantar da Arewacin Najeriya.” Hoto na biyu ya nuna Sarkin Musulmi daga Sokoto na Allah wadarai da kisan da ake wa ‘yanfashin daji da ‘yanta’adda.
A taken labarin Lucky na kira da a samar da ‘yancin gashin kai ga yankin Biafra inda yayi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta kawo karshen kalifanci a Sokoto da Najeriya don kare rayuka.
Taken Labarin na cewa ne “#MDD ki kawo karshen Masarautar Sokoto yanzu. Ki kawo karshen Najeriya da kare rayukan al’umma yanzu.”
Ya zuwa ranar 21 ga Satumba,2026 wannan wallafa ta samu wadanda suka kalla 3,000 da tsokaci biyar da yadawa sau 45 da masu nuna sha’awa 125.
Duba da matsalar tsaro a kasar, DUBAWA ta lura cewa wasu daga cikin masu tsokaci sun aminta da abin da mai da’awar ke cewa.
Wani mai amfani da shafin Facebook, Ebong Udofia, ya rubuta cewa “Me ke faruwa! Shin shi ma Sultan danta’adda ne?”
Wani shima mai amfani da shafin Illyasu Muazu, yayi tsokaci da harshen Larabci “قتله?” wanda ma’anarsa shine a “kashe shi” duk da cewa mai kalaman bai ce ga da wanda yake ba kai tsaye..
Ganin cewa irin wannan da’awa na iya jawo tashin hankali musamman a arewacin Najeriya DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike kan wannan bidiyo don tantancewa.
Tantancewa
DUBAWA ta nazarci wannan bidiyo inda ta gano abubuwa da dama, da fari mun lura da wasu mutane sanye da kayan damara zagaye da wani farar hula da aka kama ana masa tambayoyi.
Mun kuma lura cewa kayan sojojin na dauke da tuta mai launin ja da fari da baki hadi launin kore.

Hoton bidiyon
Wani binciken na daban kuma da ya nazarci kalar kayan sojan da tutar ta nunar da cewa tuta ce ta kasar Sudan.
Tutar kasar Sudan
DUBAWA ta kuma lura cewa harshen da ake amfani da shi a cikin bidiyon da aka nada na kasar waje ne ba irin na kabilun Najeriya ba, daga nan sai muka duba muryar a bincike tahanyar amfani da Google Gemini don tantance harshen da ake maganar.
Manhajar ta nunar da cewa harshen Larabci ne na kasar Sudan,kuma ta nuna cewa budiyo ne na wani mutum da aka kama ana tambayarsa kan me ya kawo shi wannan yanki, me kuma yake yi.
DUBAWA ta kuma nazarci sassa na bidiyon, sai muka ga an wallafa wannan bidiyo tun kafin ma wannan lokaci an wallafa shi a shafin Facebook a ranar 25 ga Yuli,2026.
Kuma nazari cikin bayanan shafin Facebook na mai amfani da shafin na Facebook ya nuna cewa mutumin yana zaune ne a Tambul wani birni a tsakiyar Sudan. Kuma mai wannan shafin bisa al’adarsa yana wallafa bidiyo irin wannan da suke da alaka da jami’ai masu kayan sarki.
Wani shafin Facebook da aka tantance, Esmat Ismail Ali, da hoton kasar Sudan a matsayin hotonsa a Facebook ya yada bidiyon a ranar 27 ga watan Yuli,2026.
Itama wata kafar yada labarai a shafin intanet mai suna Sudan War Monitor, ta wallafa irin wannan bidiyo inda ta ba da rahoto kan fafatawar da aka yi tsakanin dakarun sojan Sudan na Sudanese Armed Forces da Rapid Support Forces.
Taken labarin da aka rubuta na cewa,”An kama daya daga cikin dakarun Rapid Support Forces(RSF) a baya-bayan nan a fafatawar da aka yi a yankin Kordofan…”
A wani ci gaban kuma dakarun sojan kasar ta Sudan sun bayyana cewa sun kama yankin al-Mazroub da ke jihar Kordofan ta Arewa bayan fafatawar da aka yi da dakarun RSF.
Kasar Sudan na fama da matsalar yakin basasa inda ake fafatawa tsakanin dakarun na kasar Sudan SAF karkashin jagorancin Janar Abdel al-Burhan, da dakarun da ke tawaye na RSF karkashin jagorancin Mohamed Dagalo (da aka fi sani da Hemedti)
Karshe
Wannan bidiyo daga kasar Sudan ya fito ba Najeriya ba, don haka alakanta wannan bidiyo da halin rashin tsaro da ake fama da shi a Najeriya yaudara ce.
An gudanar da wannan aiki karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci-gaba (CJID) bisa daukar nauyin Kungiyar Tarayyar Turai.
