
Da’awa: Bidiyon da ake yadawa a kafafen sada zumunta ya nuna cewa wani bera ya katse wata mai gabatar da labarai ta tashar Al Jazeera yayin da take gabatarwa

Hukunci: Ƙarya ce. An haɗa bidiyon ne ta hanyar amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira, AI. Babu wata shaida ko tabbacin wannan lamari ya faru a cikin dakin yaɗa labaran Al Jazeera.
Cikakken Bayani
An yaɗa wani bidiyo mai ɗaukar dakikoki goma (10 seconds) wanda yake nuna cewa wani bera ya katse wata mai gabatar da labarai a tashar Al Jazeera yayin da take shirinta kai tsaye.
A cikin bidiyon, an ga mai gabatarwar ta firgita ta tashi daga kujerarta cikin sauri bayan ganin beran, amma daga baya ta dawo cikin nutsuwa ta zauna ta ci gaba da karanta labarai.
Bidiyon, wanda a kallon farko kamar na gaske, ya samu karɓuwa sosai. A ranar Lahadi, 12 ga Oktoba, 2025, ya samu martani 98, sharhi 21, kuma an yada shi sau 43 a Facebook. Haka kuma an yaɗa shi a X (Twitter a baya), TikTok, da WhatsApp.
Masu amfani da kafafen sada zumunta da dama sun gaskata cewa bidiyon na gaske ne daga dakin labaran Al Jazeera da ke Doha, Qatar. Bidiyon ya kuma sanya mutane dariya da bayyana ra’ayoyi daban-daban daga ‘yan Najeriya da wasu ‘yan Afrika.
Wani mai amfani da Facebook, Salis Muhammad Moriki, ya rubuta cewa: “Da irin wannan ya faru a wani gidan talabijin na Afrika ko Najeriya, labarin zai zama daban sosai.”
Shi kuma Musa Mamman ya ce: “Na tabbata zuciyarta ta tsaya na ɗan wani lokaci! Gaba ɗaya ban zata wani dakin labarai irin wannan mai tsafta zai iya samun beraye ba, duk da cewa kamar an kore shi daga wani wuri na waje.”
Saboda yadda bidiyon ya bazu sosai kuma zai iya yaudarar jama’a, DUBAWA ta gudanar da bincike don tabbatar da sahihancinsa.
Tantancewa
DUBAWA ta yi bincike ta hanyar nazarin bidiyon, inda ta gano alamun amfani da fasaha da ke nuna cewa an canza shi.
A lokacin da mai gabatarwar ta firgita ta koma bayan teburi, daga baya lokacin da ta dawo, ta ajiye hannayenta a saman wani ɓangare da babu komai, abin da ke nuna rashin daidaito a cikin bidiyon.

Kafin ɓera ya shigo da bayan ɓera ya wuce
Haka kuma, lokacin da ta koma baya, kujerar ta juya baya, amma lokacin da ta dawo ta zauna ba ta daidaita kujerar ba – ta zauna ne kamar babu kujera a wurin. Wannan yana daya daga cikin alamun da ke nuna an gyaran bidiyon da fasahar AI.

Hotunan daban-daban na mai gabatarwa tana guduwa daga teburi, tana dawowa, sannan tana zama a kujera ba tare da ta daidaita kujerar ba.
DUBAWA ta kuma yi binciken faya-fayan bidion (visual analysis) domin gano ko bidiyon na gaske ne ko an kirkira shi.
Ta hanyar Amfani da fasahar binciken AI mai suna Deepware, ta nuna cewa kimanin kashi 39% na bidiyon an kirkira shi da fasahar kwaikwayon mutum.

Hoton sakamakon binciken Deepware.
An kuma sake sanya bidiyon a wata fasahar tantance AI mai suna Sensity, wanda ya fitar da sakamako da ke cewa bidiyo “abin zargi ne”.

Hoton sakamakon binciken Sensity.
Binciken DUBAWA bai samu wani rahoton jarida ko sanarwa daga Al Jazeera da ke tabbatar da cewa wannan lamari ya faru ba.
A Karshe
Binciken DUBAWA ya gano cewa bidiyon ba na gaske ba ne, an ƙirƙire shi ne ta amfani da fasahar AI domin ya yi kama da na gaske.