Gwamnan Kano ya yi kuskure wajen bayyana sakamakon shekarar ta 2025 na jiharsa a jarrabawar SSCE na cikin gida wadda hukumar NECO ke shiryawa kowace shekara 

Da’awa: Gwamnan jihar Kano Abba Yusuf ya yi da’awar cewa daliban da suka rubuta jarrabawar kammala makaranta na SSCE a shekarar 2025 sun fi na kowane jiha nasara.

Gwamnan Kano ya yi kuskure wajen bayyana sakamakon shekarar ta 2025 na jiharsa a jarrabawar SSCE na cikin gida wadda hukumar NECO ke shiryawa kowace shekara 

Hukunci: Karya ne. Bayan da ta tantance sakamakon duk jarabawan da akan yi na kammala makaranta  SSCE na cikin gida wanda hukumar NECO ke shiryawa, jaridar Premium Times ta gano cewa jihar Kano ba ta yi ko kusa da wadanda suka kasance a kan gaba ba.

Cikakken bayani

Ranar 18 ga watan Satumban 2025, a shafinsa na Facebook, gwamnan jihar Kano Abba Yusuf ya yi da’awar cewa jihar Kano ce ta fi taka rawar gani tsakanin duka jihohin kasar a sakamakon jarrabawar kammala karatun sakandare na NECO da SSCE.

Gwamnan ya kuma kara da cewa duk wannan hujjoji ne tasirin sauye-sauyen da gwamnatinsa ta gudanar a fannin ilimin jihar.

“Abun alfahari ne da jihar Kano ta zama jiha ta farko a jarabawan SSCE da hukumar NECO ta gudaar,” ya rubuta.

“Irin wannan nasarar da ba’a taba yi ba na nuna jagorancin da gwamnatin mu ke yi a fannin ilimi, wanda ke bayar da fifiko wajen zuba jari a kai-a kai, da gina ababen more rayuwa da samar da abubuwan da ake bukata wajen koyarwa, domin su ne abubuwan da gwamnti ta fi yin la”akari da su yanzu.”

Mr. Yusuf ya kuma yi da’awar cewa jihar Kanon ce ya zo na farko har ya sha kan jihohin Legas da Oyo wadanda suka zo na biyu da na uku bi da bi.

Tuni dai aka wallafa wannan da’awar ta sa a manyan jaridu da gidajen talibijin wadanda suka hada da Tribune, Business Day, Guardian, Channels Television, da  TVC.

Abun da alkaluma ke nunawa

Bayan tantance alkaluman jarabawar da NECO ta shirya a shekarar 2025, jaridar PREMIUM TIMES ta gano cewa ba jihar Kano ce ta zo na farko ba. Bacin haka ma abin da ya faru a zahiri shi ne fiye da rabin daliban da suka dauki jarabawar ba su iya cin jarabawa biyar da mafi karancin makin da ake bukata ba hatta a Lissafi da Turanci.

Abun da Kano ta yi jagoranci da shi shi na yawan dalibai domin jihar ce ke da fiye da kashi 10 cikin 100 na yawan daliban da suka dauki jarabawan yayin kashi biyar ne kacal suka yi nasarar cin guda biyar hatta lissafi da turanci – wadanda su ne mafi mahimmanci idan dai har mutun na da niyyar shiga jami’a a Najeriya.

Kano na daya daga cikin jihohin da ke kasa a sakamakon jarabawar na 2025 

Jihar Kano ta kasance a mataki na 29 cikin jihohi 37 har da babban birnin tarayya Abuja, amma ba na farko ba kamar yadda gwamnan ke da’awa.

Haka nan ma ba ta wuce jihohin Legas da Oyo ba.

Hasali ma jihar ta wuce jihohi takwas ne kadai wadanda suka hada da Yobe, Adamawa, Plateau, Borno, Jigawa, Katsina, Zamfara, da Sokoto.

Alakluman NECO na shekarar 2025

Yayin da suke sanar da sakamakon a makon da ya gabata, rajistaran NECO farfesa Dantani Wushishi, ya ce jimilar dalibai 1,358,339 wadanda suka hada da maza 680,292 da mata 678,047 females–suka rubuta jarabawar

Mr Wushishi ya ce kashi 60.26 cikin 100 (818,492) na wadanda suka rubuta jarabawan ne suka sami akalla kredit a maudu’i biyar a ciki har da lissafi da turanci.

Ya kuma kara da cewa wasu kashi 84.26 sun sami kredit biyar da sama su ma har da Lissafi da Turanci.

Top-performing state 

PREMIUM TIMES ta tantance alakaluman jarabawar inda ta gano cewa jihar Abia ce ta zo na farko bisa makin da ake bukata a tabbatar da irin rawar da jiha ta taka.

Bayanan da aka samu daga hukumar jarabawar na nuna cewa kashi 83.31 cikin 100 na dalibai 11,260 da suka zauna wa jarabawan a jihar Abia sun yi nasara da akalla kredit biyar, har da lissafi da turanci.

Abin da jihar Kano ta samu a jarabaawar 2025 na NECO SSCE (Internal)

A waje guda kuma, fiye da rabin daliban Kano – kashi –  50.16 –  sun fadi domin kashi 49.84 cikin 100 ne kadai na dalibai 136,7622 suka sami akalla kredit biyar hade da Lissafi da Turanci.

Jihohi takwas ne kadai suke karkashin jihar Kano wadanda suka hada da: Yobe ( kashi 48.13), Adamawa (kashi 47.99), Plateau ( kashi  46.46), Borno ( kashi  44.72 ), Jigawa ( kashi 43.81), Katsina ( kashi 42.89), Zamfara (kashi  42.12) and Sokoto ( kashi 35).

Kuskuren gwamna Yusuf

Abin da gwamnan Kano ya rika barazana da shi a matsayin “taka rawar gani” asali yawan dalibai ne. 

Alhali kuma lkaluman da aka samu daga NECO wadanda gwamnan ya yi amfani da su na nuna jerin yadda jihohin ne suka yi a jarabawan.

Idan ana batun yawan dalibai ne a jarabawan, jihohin Kano, Legas, Oyo da Binuwai ne suka fi yawan dalibai. Sai dai wannan sakamakon da aka fitar ba yawan wadanda suka rubuta ya ke dubawa ba. 

Alal misali kashi 49 cikin 100 na wadanda suka rubuta jarabawar a jihar Kano suka kai mizanin da ake bukata yayin da a jihar Legas kashi 71 cikin 100 suka kai mizani da wani kashi 60.07 a jihar Oyo 

Ko da shi ke saboda yawan daliban Kano idan har aka kwatanta da yawan daliban sai a ga kamar su suka fi nasara duk kuwa da cewa kashi 49 da rairaye ne na yawan daliban suka yi nasara.

Sakamako Jiha da jiha a 2025: ALKALUMAN NECO 

A takaice dai jihar Kano ta fi yawan daliban da ba su yi nasara ba a jarabawar yayin da kashi 51 na dalibai 68,159 suka fadi kashi 49 na dalibai 68,159 ne suka yi nasara.

Dan haka yayin da kashi 49.84 ke zaman sakamakon mutane 68,159. A jihar Abia kashi 83.31 ya zo ne daga dalibai 9,381 kacal.

Haka nan kuma duk da cewa jihar Kano ke da dalibai kashi 10 cikin 100 na jimilar daliban da suka yi jarabawar, kashi biyar na wannan adadin na jihar Kano duk sun fadi.

Jihohi 10 na farko wadanda suka fi taka rawar gani a jarabawar 2025 NECO SSCE

Jihohi 10 na farko

  1. Abia – 83.31 per cent
  2. Imo – 83.09 per cent
  3. Ebonyi  – 80.60 per cent
  4. Anambra – 76.80 per cent 
  5. Bayelsa – 73.88 per cent
  6. Delta – 73.10 per cent
  7. Osun – 72.64 per cent 
  8. Ogun – 72.21 per cent 
  9. Lagos – 71.76 per cent 
  10. Ekiti – 68.50 per cent

Jihohi 10 na karshe a jarabawar SSCE da hukumar NECO ta shirya a shekarar 2025

Jihohi 10 na karshe

28. Bauchi – 52.62 per cent

29. Kano – 49.84 per cent

30. Yobe – 48.13 per cent

31. Adamawa – 47.99 per cent

32. Plateau – 46.46 per cent

33. Borno – 44.72 per cent

34. Jigawa – 43.81 per cent

35. Katsina – 42.89 per cent

36. Zamfara – 42.12 per cent

37. Sokoto – 35.00 per cent

A Karshe

Da’awar cewa jihar Kano ce ta fi taka rawar gani a jarabawar SSCEn da hukumar jarabawar NECO ke shiryawa ba dai dai ba ne. Bayan da ta tantance duk alkaluman jarabawan jaridar Premium Times ta gano cewa Kano ba ta zo na farko kamar yadda ake da’awa ba.

Exit mobile version