
Da’awa: Wani mai amfani da Facebook ya yi ikirarin cewa Najeriya ce kasa mafi tsadar mai a cikin kasashen masu arzikin man fetur.

Hukunci: Yaudara ce. Binciken DUBAWA ya gano cewa Najeriya ba ita ce mafi tsadar mai ba a cikin kasashen masu arzikin man fetur.
Cikakken Bayani
Najeriya na daya daga cikin manyan kasashen Afrika masu arzikin man fetur, inda take samar da kusan ganga miliyan 1.3 a kowace rana. Duk da wannan arziki, ‘yan kasa da dama na ganin ana saida mai a farashi mai tsada idan aka kwatanta da sauran kasashen da ke da irin wannan albarkatun kasa.
A cikin wallafar Mustapha Sani Abdullahi a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa Najeriya ce kasa mafi tsadar mai a duniya cikin masu arzikin man fetur.
“Kunga yadda suke satar man fetur din Najeriya amma kuma ba zasu sayar ma talakawan kasa da sauki ba. Duk cikin kasashen duniya masu arzikin man fetur, Najeriya tafi kowace kasa saida man fetur da tsada kuma tafi kowace kasa tauye hakkokin ‘yan kasa. Kai tafi kowace kasa karancin albashi.” a cewar Mustapha.
Wannan labarin ya jawo cece-kuce inda aka yada shi sau 9, mutum 12 suka yi sharhi da 76 danna alamar martani, kamar yadda muka zakulo a ranar 10 ga Oktoban 2025.
DUBAWA ta gudanar da bincike don tantance wannan ikirari ta hanyar kwatanta farashin man fetur a Najeriya da sauran kasashe masu arzikin mai.
Tantancewa
Binciken DUBAWA ya gano wani rahoto daga kafar da ke kididdiga da samar da alkaluma kan harkokin yau da kullun, Statista wanda ya nuna cewa akwai kasashe masu arzikin mai kamar Saudi Arabia, Iran, Kuwait, da Venezuela da suke da farashin mai mai sauki saboda gwamnati na saka tallafi mai yawa.
Amma akwai kuma kasashe irin su Norway da Angola da Najeriya da suke saida mai a farashi mai tsada, saboda babu tallafi a can.
Jaridar ThisDay ta tabbatar cewa bayan cire tallafin mai, Najeriya ta shiga cikin kasashen Afrika masu tsadar mai, amma har yanzu tana kasa da wasu kasashen Turai da kuma wasu kasashen yammacin Afrika.
Sai dai rahoton jaridar Punch ya ce duk da hauhawar farashin, Najeriya har yanzu tana da farashin mai mafi rahusa a yammacin Afrika, idan aka kwatanta da Ghana, Ivory Coast, da Benin.
Dalilan da ke haddasa hauhawar farashi
- Cire tallafin mai: Wannan ya sa kamfanonin man fetur ke sayarwa bisa farashin kasuwa, ba tare da taimakon gwamnati ba.
- Tsadar canjin kudi: Lokacin da dala ta tashi, farashin mai da ake shigo da shi daga waje ma yana tashi.
- Haraji da sufuri: Tsadar jigilar mai da karin kudin gwamnati na kara farashin lita daya.
Wadannan abubuwa ne suka sa mai ya yi tsada a Najeriya, amma hakan ba yana nufin Najeriya ce ke da mafi tsadar mai a duniya ba.
A Karshe
Da’awar da aka yada cewa Najeriya ce kasa mafi tsadar man fetur a duniya cikin masu arzikin mai ba gaskiya ba ce. Najeriya na fama da hauhawar farashin mai bayan cire tallafi, amma akwai wasu kasashe kamar Norway, Angola, da ke saida mai a farashi mafi tsada.