Takardun kudin naira dubu daya. Asalin hoton: Ndokwa Reporters
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani mai amfani da shafin X, @Sebastineogb, ya wallafa wani bidiyo ya na da’awar cewa Hukumar da ke yaki da masu wa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ce ta gano takardun kudi da dama wadanda suka riga suka rube cikin wata kwantena a Abuja

Hukunci: Yaudara ce kawai! Wannan bidiyon sake yada shi kawai ake yi domin tun a 2022 aka dauka kuma na takardun kudin da aka lalata ne wadanda aka gano a barikin ‘yan sandan Wadata da ke jihar Binuwai.
Cikakken bayani
Lamarin tattalin arzikin Najeriya ya jefa mutane cikin wani yanayi na takaici. Tsananin rayuwa ce ta hadu da wasu manufofin da aka aiwatar ba tare da cikakken nazarin yadda zai shafi al’umma ba suka kara ta’azzara lamarin. Shi ya sa ma ‘yan Najeriya yanzu kusan kowani loakci suke komawa ga soshiyal mediya su yi korafi.
Ba da dadewan nan ba babban bankin Najeriya CBN ya sanar da sauye-sauyen da suka shafi cire kudi a ATM inda kudin da ake caza idan mutun ya cire kudi a harabar bankin ya banbanta da wanda za’a dauka idan mutun ya cira a waje. Wannan na nufin kara rashin kudi wa ‘yan Najeriya duk sadda suka je cire kudin da suka yi wa zufa.
Wasu ‘yan Najeriya sun yi Allah wadai da wannan matakin, wanda ake sa ran kaddamarwa ranar daya ga watan Maris 2025, tare da kushe karin harajin da ya riga ya zama wani babban nauyi wa ma’aikata a kasar. Haka nan su ma ‘yan kasa sun yi kuka da rashin shugabanci nagarin da ake fama da shi a kasar set to begin on March 1, 2025, criticising the growing tax burden on the working population. Other concerned citizens also decried poor leadership in the country.
Da ya shiga mahawarar a dama da shi, wani mai amfani da shafin X, @Sebastineogb, ya wallafa wani bidiyo da zargin wai kwanan na EFCC ta gano kudaden da suka rube a barikin ‘yan sandan da ke Wadata, Abuja.
Ya yi wa labarin taken “Labari da Dumi-Dumi: EFCC ta gano wasu kudaden da aka boye cikin waya kwantena a Wadata, Abuja. Shi ya sa ‘yan siyasanmu ba za su taba shiga Al-Janna ba, dubi kudadenmu. Zaben shugabanin da ba nagari ba yana da illa sosai.”
Wasu daga cikin mabiyansa sun yadda cewa kwanan nan aka fitar da bidiyon kuma sun yi Allah wadai da “son kan” shugabannin Afika wadanda suka gwamnace cin kudin kasa a maimakon inganta rayuwar al’umma wadanda dama can kudin na su ne.
An wallafa labarin a shafin Facebook kamar yadda muka gani a wadannan makalun, wato nan, nan da nan.
Tantancewa
Mun fara da nazarin bidiyon, inda daga nan ne ma muka gano cewa tuna a shekar 2022 aka fara wallafawa. Mazauna unguwar ta Wadata ce suka gano cewa akwai wasu jakunan kudade a kusa da barikin sojojin Wadatan da ke jihar Binuwai. A lokacin an ce takardun kudin sun shafe shekaru a boye.
To sai dai a wancan lokacin wata majiyar EFCC ta fadawa jaridar PUNCH cewa jakunan kudin sun fito daga babban bankin Najeriya ne wato CBN.
Majiyar ta bayyanawa mai kudin ya siyo su ne daga EFCC bayan da aka lalata su, sa’annan ya kawo su wurin ya kara yayyagawa dan yin amfani da su wa wani abu na daban.
Haka nan kuma, ‘yan sandan Binuwai sun tabbatar cewa sun taba gayyatar mai shagon, Mr. Isah Suleiman, dan yi masa tambayoyi. Daga nan ne Isah ya mika musu izinin amfani da takardun kudin wanda ya karba daga CBN.
‘Yan sandan sun bayyana cewa lalatatun takardun daga CBN dama an yi amfani da su ne wajen sarrafa maganin sauro.
A Karshe
An wallafa bidiyon ne kawai dan yaudarar jama’a. Tun a 2022 aka fara ganin bidiyon.
