
Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook ya wallafa wani bidiyo da ya nuna malamin nan da ake yawan cece-kuce a kansa, Ahmed Gumi na kira ga Gwamnatin Tarayya ta sasanta da ‘yanfashin daji inda ya bukaci a duba walwalar ‘yanfashin dajin a cikin kasafin kudin Najeriya.

Hukunci: KARYA CE. Nazarin DUBAWA ya gano cewa an samar da wannan bidiyo ne ta hanyar amfani da kirkirarriyar basira ta AI, kuma babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta bayyana shehin malamin yayi wannan kalami.
Cikakken Sako
Wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Prime Entertainment, ya yada wani bidiyo mai tsawon dakika 30, inda aka nunar da wannan babban malamin addini da ake yawan cece-kuce akansa na kira ga gwamnatin Najeriya da ta sulhunta da ‘yanfashin daji ta kuma duba walwalarsu a cikin kasafin kudi na kasa.
Ya zuwa ranar 27 ga watan Nuwamba, 2025 wannan karamin bidiyo ya samu martani 27,000 akwai masu tsokaciu 28,000 da mutane 15,000 da suka sake yada bidiyon.
A sashin tsokaci na bidiyon akwai mabanbantan ra’ayoyi kan wannan da’awa sai dai mafi akasari sun fi karkata ne ga sukar wannan shawara da aka bayar.
Ga misali Malafakumo Ibe ta nuna mamakinta ne, inda take ganin ta yaya ne ma malamin zai yi irin wannan furuci duba da halin tabarbarewar tsaro da ake fama a kasar. Sai ta ce “Shin wannan malami da ake kira Gumi yafi karfin gwamnati ne? Tambaya ce kawai.”
Ohaeri Bright yace “Bara na yi bayani, yana nufin a samu wani sashi na kasafin kudin Najeriya sai a ce an ware misali naira miliyan dubu 5 a duk shekara don kula da walwalar ‘yanta’adda.”
Har ila yau kuma akwai wadanda suke ganin cewa wannan bidiyo an yi shine da fasahar AI.
Wani mai amfani da shafin na Facebook mai suna VicVic yace “Wannan fa aikin AI ne amma shin wa ke zama a gaba a yin sulhUn da ‘yanbindiga? ” Wani ma mai amfani da shafin Kangoma Turay, yace “ wannan bidiyo ne da aka kirkire shi da fasahar ta AI, ku lura da sauti irin na mutum-mutumi daga kasa-kasa.”
Duba da yadda aka samu mabanbantan ra’ayoyi da ma halin matsalar tsaro da ake ciki a Najeriya, hakan ya sanya DUBAWA ganin wajibcin gudanar da binciken gano gaskIya kan da’awar.
Tantancewa
DUBAWA ya gudanar da nazari kan wannan bidiyo don gano sahihancinsa. Bincikenmu ya gano cewa akwai wasu abubuwa da suka sabawa hoton bidiyo na gaskiya a tattare da bidiyon.
Yanayi na motsawar jiki bai kama da na gaskiya ba, bidiyon baya tafiya yadda ya kamata, kuma an lura akwai banbanci na murya, idan aka kwatanta da bidiyo na gaskiya wanda na Gumin ne yana magana.
Domin tantance abin da ake zargi, mun yi amfani da TruthScan AI, wanda ake amfani da shi don tantancewa da gano asalin magana, kuma manhajar ta tabbatar da cewa kaso 96 cikin dari ya nunar da cewa wannan muryar dorata aka yi akan budiyon, ta hanyar amfani da kirkirarriyar fasaha ta AI.Sakamakon nazarin muryar da aka tantance. Tushe: TruthScan AI
Har ila yau mun kuma yi amfani da wata manhajar mai suna (Attestiv Video Deepfake Detector) don sake fayyace wannan bidiyo kuma sakamakon ya nunar da cewa an yi kokari sosai wajen sauya fuskar, kuma bidiyon bai kama da na gaskiya ba, wanda kuma alamu ne da ake gani idan an yi amfani da fasahar ta AI wajen kirkirar bidiyo.
Sakamako na nazarin bidiyon. Tushe: Attestiv Video
Mun kuma nazarci tattaunawa da aka yi da malamin a baya-bayan nan, amma mun gaza gano inda yake kira na a shigar da batun walwalar ‘yanbindiga a kasafin kudi na kasa.
A Karshe
Babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta nuna ko ba da rahoto cewa Ahmed Gumi yayi kira na a shigar da walwalar ‘yanbindiga a cikin kasafin kudin kasa. Nazari da aka yi kan bidiyon ya nunar da cewa wannan bidiyo da muryar duka hada su aka yi ta hanyar amfani da kirkirarriyar fasaha ta AI. Don haka wannan da’awa karya ce.
Shin da gaske ne shugaban kasar Afurka ta Kudu ya bukaci Najeriya ta saki Nnamdi Kanu?
Hoton da aka yada a shafin X cewa an kama mambobin IPOB ko ESN an yi shi ne tun a 2021
Juyin mulki a a Jamhuriyar Bene da bai nasara ba: Shin shugaban Najeriya na iya aikawa da dakarun soja zuwa wata kasa ba tare da amincewar majalisa ba?
Shin sojan Amurka sun kaddamar da hari kan mayakan ISWAP a yankin Tafkin Chadi?