African LanguagesHausa

Bidiyon ‘yan kasuwa a Legas ne ake amfani da shi a sunan bakin haure marasa matsugunnai a Toronto na kasar Kanada.

Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X ya wallafa wani bidiyon da ke nuna mutane suna sayar da kayayyaki a bakin wani layin dogo, da zargin cewa bakin haure ne wadanda ke zama a wannan wurin saboda rashin samun gidaje a Toronto.

Bidiyon ‘yan kasuwa a Legas ne ake amfani da shi a sunan bakin haure marasa matsugunnai a Toronto na kasar Kanada.

Sakamakon bincike: KARYA. Bincikenmu ya nuna mana cewa an dauke bidiyon ne a jihar Legas, Najeriya, a kusa da layin dogo.

Cikakken bayani

Layin dogon garin Oshodi da ke Legas Najeriya na da mahimmanci sosai ga hanyoyin jirgin kasar Legas, inda wannan layin dohon ne ke hada Oshodi da sauran manyan yankunan da ke cikin Legas, ta yadda ya ke saukake sufuri a cikin jihar da ma rage yawan cunkuson da ake yawan samu kan titunan birnin mai yawan al’umma.

Ranar 10 ga watan Yulin 2023, jami’an Hukumar kula da tabtace muhalli da laifuka na musamman sun kai samame kan ‘yan kasuwan da ke sayar da kayayyaki a kusa da layin dogon Oshodi da gadan Apongbon.

Wannan ya biyo bayan umurnin gwamnan jihar ne Babajide Sanwo-Olu, na cewa a haramta saye da sayarwa a kan manyan hanyoyin da tituna a cikin birnin Legas, Wannan matakin kuma ya zama tilas ne dan kare muhalli daga hadarukka da kuma tabbatar da kariyar rayukan jama’a da kaddarorinsu.

Sai dai a waje guda, wani mai amfani da shafin X, Nya Pfannerstill (@Nyapfanner), ya wallafa bidiyo na wani jirgin da yake wucewa a tsakanin mutanen da ke kokarin saye da sayarwa a kusa da layin dogon. A cewar mai wannan shafin, mutanen suna kan layin jirgin ne a Toronto na Kanada, kuma dukkansu bakin haure ne wadanda ke zama a wurin saboda rashin matsugunnai.

Taken wannan bidiyon shi ne, “Ganin yadda ba su da wurin zama, ya zama dole wa bakin hauren Trudeau su koma zama kusa da layin jirgin GO a Toronto.”

Wannan labarin ya dauki hankalin jama’a dan sama da 184,000 suka kalla, wasu 170 suka sake wallafa batun a shafukansu a ranar Talata 20 ga watan Fabrairun 2024.

Da muka lalubi inda ake tsokaci mun sami bayanai da dama da ke musunta gaskiyar wannan da’awar.

Mai shafi, @markbull2, ya ce, “Wanna ba layin jirgin kasa na GO a Toronto ba ne.” Mai shafin @LoveMyWood cewa ya yi, “sauke wannan labarin wannan ba layin jirgin kasa na GO ba ne.”

Ganin yadda labarin ya dauki hankali ne ya sa muka yanke hukuncin tantance gaskiyar wannan labarin.

Tantancewa

Mun duba halataccen shafin X na Tokunbo Wahab, kwamishinan jihar Legas na Muhalli da Ruwa, inda muka ga tsokacin da ya yi ranar 13 ga watan fabrairun 2024 dangane da bidiyon da ke yawo.

Ya fayyace cewa Legas ne ba Toronto ba kamar yadda ake zargi. Inda ya kuma cigaba da fadada bayaninsa a wasu sakonnin da ya wallafa, ya ce mataki ne da jihar Legas ta dauka dan rage yawan afkuwar hadarurruka kuma ba shi da alaka da rashin matsugunnai wa bakin hauren da ke Kanada.

A cewarsa: “A matsayin martani ga bidiyon da ke yawo na wadanda ke saye da sayarwa a kusa da layin dogo, Ma’aikatar Muhalli da Ruwa na jihar Legasa tare da jami’an hukumar kula da Muhalli (MAI) da safiyar nan suka fara korar mutane daga wuraren da ke kusa da jirgin.”

Har ila yau, DUBAWA ta gudanar da bincike na mahimman kalmomi a Google ta kuma duba bidiyon a cikin manhajan google din da ke tantance asalin hotuna da bidiyoyi, inda ta gano cewa an ma wallafa bidiyo a wasu shafukan wadanda su ma suka karyata batun, misali a nan da nan.

A Karshe

Bincikenmu ya nuna mana cewa bidyon da wani mai amfani da shafin X ke zargi wai layin jirgin kasar GO ne a Toronto layin dogo ne a jihar Legas, dan haka wannan batun karya ne.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
Translate »