Allon Makarantar Maga, Jihar Kebbi, Nijeriya. MallakadHoto: BBC.
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani bidiyo da ake yadawa a WhatsApp ya nuna cewa ‘yan mata 25 da aka sace daga makaranta a Maga, Jihar Kebbi, an kashe su ta hanyar yanke wuyansu.

Hukunci: Karya ce. Binciken DUBAWA ya gano cewa bidiyon ba shi da alaƙa da Najeriya, kuma ana kyautata zaton ya fito daga yankin Afirka ta Tsakiya.
Cikakken Bayani
A yayin da matsalar rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a Najeriya, wani bidiyo mai tayar da hankali ya fara yawo a WhatsApp, inda ake ikirarin cewa ‘yan mata 25 da aka sace daga makaranta a Maga, Jihar Kebbi, an “yanka su kamar kaji.”
Bidiyon mai tsawon minti 1 da sakan 12 ya nuna hotunan kisan gilla masu matuƙar tayar xa hankali, inda ake ganin an kashe wasu mutane.
A cikin rubutun da aka saka cikin bidiyon, an ce: “An sace ‘yan mata 25 daga makaranta a Maga, Jihar Kebbi a ranar Lahadi an yanka su kamar kaji… Gaskiya wannan al’amari ya wuce gona da iri…”
Wannan ikirari na iya janyo tsoro da fushin jama’a a kafafen sada zumunta, musamman ganin tarihin sace ɗalibai a Najeriya.
Saboda muhimmancin batun da kuma haɗarin yaɗa labarin ƙarya, DUBAWA ta gudanar da bincike don tantance gaskiyarsa.
Tantancewa
DUBAWA ta fara ne da nazarin sauti da hoton da ke cikin bidiyon.
Bincike ya nuna cewa harshen da ake magana a bidiyon ba Ingilishi ba ne, kuma ba ɗaya daga cikin manyan harsunan Najeriya ba ne. Don tabbatar da hakan, DUBAWA ta yi amfani da manhajar Google Gemini wajen fassara sautin.
Sakamakon ya nuna cewa ana amfani da haɗin Arabic da Swahili cikin bidiyon.
A ɓangaren Larabci, an ji wani mutum addu’ar buɗe taro a addinin musulunci, da kuma karanta ayar Al-Qur’ani, musamman Suratul Muhammad aya ta 4.
A ɓangaren Swahili kuma, mai magana yana bayani ga jama’a yana danganta kisan a matsayin “umarnin addini.”
Binciken hotuna ya nuna wasu rashin daidaito. Mayakan da ke cikin bidiyon suna sanye da kakin soja da ba ya kama da na sojojin Nijeriya ko na kungiyoyin da aka sani kamar ISWAP ko ‘yan bindiga.

Hoton bidiyo da aka zaƙulo
Wannan ya nuna cewa bidiyon ba a Najeriya ba ne.
An sha danganta kungiyar ADF da ke amfani da Swahili wajen yaɗa bidiyoyin farfaganda tare da aiwatar da munanan hare-hare ciki har da yankan mutane a yankunan Beni da Ituri.
Binciken masana tsaro daga Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Jami’ar Sojojin Amurka da ke West Point ya dade yana danganta irin wadannan alamu da ƙungiyar ADF, wadda ke aiki a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC) da wasu sassan Afirka ta Tsakiya.
Babu hujjar kisan dalibai a Kebbi
Don tabbatar da ikirarin sace daliban, DUBAWA ta gudanar da binciken kalmomi a Google kan lamarin da ake magana a Maga, Jihar Kebbi.
Rahotanni sun tabbatar cewa an sace daliban a ranar 17 ga Nuwamba, 2025 a makarantar mata GGCSS, Maga, amma daga baya an ce an kubutar da su.
Rahotanni sun nuna cewa an sako daliban a ranar 25 ga Nuwamba, 2025, kuma an mika su ga gwamnati, wanda hakan ya sabawa ikirarin cewa an kashe su.
DUBAWA ta kuma tuntubi Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kebbi ta hannun Kakakinta, Bashir Usman, wanda ya tabbatar cewa babu wani rahoton kisan daliban da aka sace a jihar.
“Dalibai mata 25 da aka sace a Maga an sako su kuma an hada su da iyalansu tun shekarar 2025”, in ji shi.
A Karshe
Bidiyon da ake yadawa a WhatsApp da ke ikirarin cewa an yanka dalibai mata 25 da aka sace a Maga, Jihar Kebbi, karya ne.
