African LanguagesHausa

BINCIKE: Buhari ya kaddamar da filin tashi da saukar jiragen sama na naira biliyan ₦15 a jihar Nasarawa sai dai yabi sahun manyan ayyuka marasa tasiri a Najeriya

Getting your Trinity Audio player ready...

Bayan gina shi a fadin kasa mai girman hekta 1,000, filin tashi da saukar jiragen saman na birnin Lafiya da aka tsara za a rika saukar jiragen dakon kaya a jihar Nasarawa da aniya ta samar wa jihar sauyi a fannonin albarkatun kasa da ayyukan gona. Shekaru uku bayan kaddamar da wannin filin jiragen sama babu jirgin da ya sauka, wajen ajiye kayayyaki shiru kake ji, baki dayan filin jirgin saman ya zama kufayi an bari komai na lalacewa.

Yadda wayar da ta zagaye filin jirgin saman ta zama zmamaye da ciyayi ya nuna yadda wannin filin jiragen sama da aka tanada don al’umma ya zama matattara ta beraye da macizai, wannan shine makomar wannan filin jirgi da aka tanada don saukar jiragen sama na dakon kaya da aka kashe naira miliyan dubu 22.

Jaridar PREMIUM TIMES ta ziyarci wannan filin jiragen sama a wani lokaci cikin watan Janairu, da ganin yadda maigadin wajen cikin wasu kaya marasa launi ke kallon motar ya nuna alamu da ke cewa ziyarar wajen ya zama bakon abu, ba ko da yaushe ake zuwa ba.

Wannan aikin samar da filin jiragen sama ba zai zama irin ayyukan da gwamnati kan yi na bogi ba, aiki ne da ake fatan zai sabunata fata na al’umma da suka ba da filin gonakinsu don samar da wannan filin jiragen sama da zai sauya rayuwarsu cikin fatan da suke da shi.

“Tabbas, na yi farin ciki a watan Nuwamba,2015 lokacin da Gwamna Al-Makura ya bayyana yin wannan aiki a Lafia,” a cewar Mohammed Abubakar wani dan tireda da ke zaune a kusa da wannan filin jirgin sama.

Ga Abubakar da wasu mutane da ke zaune a yankin da suka ba da gonakinsu don wannan aiki, watsar da wannan filin tashi da saukar jiragen sama ya nuna rashin amfani da dama da karya alkawura, tsohon gwamnan yayin alkawarin cewa filin tashi da saukar jiragen saman zai zama sila ta samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arziki, abin da suke ganin ya cancanci su sadaukar da gonakin don samun wannan amfani.

A ranar 24 ga watan Fabrairu,2022 Mista Abubakar da makotansa sun sake samun karfin gwiwa a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar (commissioned) da wannan filin jiragen sama na dakon kaya, sai dai bincike da jaridar PREMIUM TIMES ta gudanar ya gano cewa wannan aiki bai kammala ba.

INVESTIGATION: Commissioned by Buhari, Nasarawa’s ₦15 billion airport joins Nigeria’s white elephant projects

Kofar shiga filin jiragen sama [Wanda ya dauki hoto -James Aparshe]

“Duka muna farin ciki da wannan ci gaba. Wannan filaye namu ne, na mallaki kimanin hekta bakwai daga ciki, muna bukatar ci gaba cikin al’umma, muna fatan a samar da ayyuka ga yaranmu daga wannan jiragen dakon kaya da za a rika kawowa,” 

”Mista Abubakar dan shekaru 63 ya fadawa PREMIUM TIMES cewa “Kimanin shekaru 11 tun da aka fara batun wannan aiki, shekaru uku kuma da aka kaddamar da aikin har yanzu babu labarin wanann filin jirgin sama.”

Tambayar da kowa ke yi ita ce : Me yasa aka yi watsi da wannan aikin samar da filin tashi da sauran jiragen saman dakon kayan?

Domin amsa wannan tambaya PREMIUM TIMES ta ziyarci wannan filin jiragen sama a lokuta da dama tun daga watan Janairu zuwa Yuli,2025 don ganin halin da filin yake ciki, mun kuma samu bayanai daga al’umma da masu zaman kansu don ganin kudaden da aka warewa wannan aiki.

INVESTIGATION: Commissioned by Buhari, Nasarawa’s ₦15 billion airport joins Nigeria’s white elephant projects

Hasumiyar filin jiragen sama [Hoto -James Aparshe]

Tushen Labarin

A shekarar 2015, a lokacin Gwamna Al-Makura ya sanya hannu a wata yarjejeniya da wani kamfani mallakar ‘yankasar China  Tongyi Group Engineering, don gina (construct) filin tashi da saukar jiragen sama karkashin wata yarjejeniya tsakain gwamnati da masu zaman kansu (PPP), kamfanin shi zai ba da kudi kaso 75 cikin dari na kudaden da za a kashe don wannan aiki.

Sai dai yadda aka kai ga ba da aikin wannan kwangila akwai kumbiya-kumbiya, saboda gwamnati ta gaza ba da bayanai kan sharudan da aka gindaya a wannan kwantiragi, kasa da shekara guda sai wannan aiki ya tsaya bisa umarnin gwamnati, babu wani bayani ko nawa gwamnati ta kashe a aikin ko kuma nawa bangaren kamfani ya kashe.

PREMIUM TIMES ta mika bukatar sani karkashin dokar fadin albarkacin baki ta FOI zuwa bangaren gwamnati don jin cikakken bayani game da wannan kwantiragi, haka nan ta kuma mika irin wannan bukata ga bangaren kamfanin na kasar China.

Gwamnatin ta ki ba da bayani, abin da ya sabawa dokar ta FOI, sai dai a bangaren na kamfanin na Tongyi Group, ta hanyar lauyan kamfanin sun ba da bayanansu inda suka ce an dakatar da aikin kwantiragin a ranar 10 ga watan Nuwamba,2016, sai dai yaki amincewa da ba da bayani cikakke.

INVESTIGATION: Commissioned by Buhari, Nasarawa’s ₦15 billion airport joins Nigeria’s white elephant projectsSashen kashe gobara da aka manta da shi[Hoto -James Aparshe]

“Mune lauyoyin kamfanin Tongyi Group Limited, wadanda za mu kira wadanda muke wa aiki. Wannan aikin kwantiragi gwamnatin jihar Nasarawa ta ba wa kamfanin da muke tsayawa, an kuma dakatar da shi a ranar 10 ga watan Nuwamba,2016,’’ a cewar ofishin lauyoyin da ke tsayawa kamfanin Tongyi Group.

PREMIUM TIMES daga baya ta gano cewa an sake ba da aikin wannan gina filin jirgin sama ga kamfanin gine-gine na Triacta Nigeria Limited, kamfanin da aka yi takkadammar gina filin jirgin saman kasa da kasa na Gusau da shi, anan ma gwamnatin taki ba da bayanai kan kudaden da aka ware don yin wannan aiki.

Jaridar ta PREMIUM TIMES nan ma ta mika bukatarta ta neman bayani karkashin dokar ta FOI zuwa ga kamfanin Triacta inda ta bukaci sanin kudade da aka warewa aikin da sharudan da aka gindaya da abubuwan da ake son cimmawa, kamfanin ya aiko da bayanai kan abubuwan da ake son ganin yayi. Kamfanin ya aiko da bayanai kan abubuwan da aikin ya kunsa, kuma ya nuna cewa an biya shi kudadensa baki daya kuma ya kammala aikinsa.

A cewar kamfanin na Triacta, kwantiragin da fari na  ₦6.45 biliyan ne wanda aka bashi ya samar da titin jirgin sama mai nisa da fadin 2.2km x 45m da hanyar da kananan motoci za su bi mai nisa da fadin  150m x 30m da wurin tsayawar jirgi  70m x 70m, sai aikin zagaye filin jirgin, suma dai kamfanin basu ba da bayani kan kudaden da wancan kamfani ya kashe ba.

Bayan da Al-Makura ya bar ofis a 2019, Abdullahi Sule ya ci gaba da aikin, bayanan da PREMIUM TIMES ta samu sun nunar da cewa Gwamna Sule ya sabunta kwantiragin daga biliyan ₦6.5 zuwa biliyan 11 inda ya kafa hujja da karin wasu ayyuka da basa cikin kwantiragi na farko.

Wannan ya hadar da aikin fadada hanyoyin da jirgin kan bi da wajen tsayawarsa  inda aka fadada da mita 150m x 150m na zubin kankare a gefen wajen tsayawar jirgin da hanyar da yake bi. An yi wadannan gyare-gyare a ranar 4 ga Janairu,2022 kwanaki 40 kafin Shugaba  Buhari ya kaddamar da filin tashi da saukar jiragen saman. 

A amsar da kamfanin na Triacta ya aikawa PREMIUM TIMES, Triacta yace akwai karin wasu ayyuka da aka bayar a watan Janairu,2022 kuma an kammala su sai dan karashe da ya kamata a yi idan an sanya fitulu wanda baya cikin ayyukan da aka bawa Triacta. 

Kamfanin ya kara da cewa karin kudaden aikin kwantioragin da ake samu na faruwa ne saboda hauhawar farashin kayayyaki muhimmai misali mandisel da kwalta.

INVESTIGATION: Commissioned by Buhari, Nasarawa’s ₦15 billion airport joins Nigeria’s white elephant projectsHanyar da mota za ta bi a filin jirgin sama (Hoto -James Aparshe)

Nawa ne kudaden da gwamnati ta kashe?

Bayan da aka yi ta mika bukatar samun bayanai daga bangaren gwamnati ita kuma taki ba da bayanan kudaden da ta kashe a wannan aiki, kasancewar babu wani bayani a hukumance PREMIUM TIMES ta sake nazartar kasafin kudi na jihar ta Nasarawa 2016-2024.

Nazarin ya nunar da cewa gwamnatin jihar ta ware kudade miliyoyi dubbai a aikin filin jiragen saman.Kasafin ya nunar da cewa an ware biliyan ₦5 a 2015 da 2016 da 2017 (biliyan ₦15) sannan an ware biliyan ₦4 a 2018 da 2019. A shekarar 2022 da 2023 da 2024 gwamnati ta ware biliyan ₦1 da miliyan ₦35 da miliyan₦900 daya bayan daya.   

Da ta bibiya kudaden da aka saki, PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa an saki biliyan ₦15 ga aikin da aka yi watsi da shi.                 

Hasumiyar filin jirgin ba a kammala ba, wajen ajiye kayayyaki wani bangare ya lalace, bangaren masu kashe gobara ya balbalce saboda rashin amfani da shi ko zuba kaya marasa inganci.

Dauki daga Gwamnatin Tarayya

Shugaba Buhari ba wai kawai ya kaddamar ko bude wannan filin tashi da saukar jiragen sama da ba a kammala ba, ya kuma bude matakai ne na yadda gwamnatin tarayya za ta karbi iko da wannan fili.

Karkshin kundin tsarin mulkin Najeriya filayen jiragen sama na karkashin wani jerin abubuwa ne karkashin majalisa, ma’ana ko da gwamnatin jiha ta gina su to gwamnatin tarayya ita za ta karbi iko da su, sai ta mayarwa jiha kudadenta.

INVESTIGATION: Commissioned by Buhari, Nasarawa’s ₦15 billion airport joins Nigeria’s white elephant projectsFuskar sashin da ake zuwa hawa jirgin in zaa yi tafiya   (Hoto -James Aparshe)

A shekarar 2024 majalisar dokokin tarayya ta amince Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mayar wa gwamnatin jihar Nasarawa kudade biliyan ₦9, to sai dai kuma tun bayan mika wannan filin jiragen sama bai fara aiki ba.

Wada Yahaya,tsohon kwamishinan gidaje da ayyuka a jihar ta Nasarawa ya bayyana cewa akwai sauran ayyuka da ya kamata a kammala kafin wannan filin jiragen sama ya fara aiki.

“ A kwai sauran tsare-tsare a hanyar da jirgin kan bi kafin ya tashi da ya kamata a yi, haka kuma akwai wasu sassa da ke bukatar a kammala aikinsu kafin gwamnatin tarayya ta karbi wurin baki dayansa.’ A cewar Yahaya a zantawa da PREMIUM TIMES  ta hanyar wayar tarho.

Amma Mista Al-Makura ya jaddada cewa filin tashi da saukar jiragen saman aikinsa ya kai “sama da kashi 90 cikin dari” kafin ya bar gwamnati. 

”Aikin filin tashi da saukar jiragen saman ya kai kaso 90 cikin 100 a 2019, kaso 10 cikin 100 da yayi saura ya hada da kammala aikin hasumiya da wurin masu kula da tashi da saukar jiragen sama.” kamar yadda ya fadawa jaridar ta PREMIUM TIMES. “Wannan fili tashin jiragen sama na amfani da shi daga lokaci zuwa lokac don aiki da ya shafi jami’an gwamnati.”

Ya kuma yi alkawari na cewa zai ba da wasu bayanai na kafa hujja ga da’awarsa, sai dai yaki amincewa a samu lokaci na tattaunawa da shi kan batun.

INVESTIGATION: Commissioned by Buhari, Nasarawa’s ₦15 billion airport joins Nigeria’s white elephant projectsWani sashi da ke nuna bangare na hanyar da za ta kai ka ga wajen da ake tashi (Hoto-James Aparshe)

PREMIUM TIMES ta tuntubi ma’aikatar harkokin sufurin jiragen sama ta gwamnatin tarayya da sashin da ke kula da bunkasar harkokin jiragen saman sai aka hada ta da mai magana da yawun ma’aikatar Odutayo Oluseyi shi kuma ya hada jaridar da daraktar sufurin jiragen sama-matakin da ya haifar da alamar tambaya ganin cewa shi mai magana da yawun ma’aikatar na da hurumi kan duk abin da zai fadi na ma’aikatar baki daya. Duk zuwan da aka yi ga daraktan sashin kula da sufurin bai haifar da wani sakamako ba kasancewar ana cewa daraktan yayi tafiya. 

Wani jami’i a sashen  Lar Jimam, da yayi alkawari na tsara gudanar da tattaunawa da daraktan daga bisani mai dauko rahoton idan ya kira wayarsa baya dauka.

Dabi’ar gina filayen jiragen sama a jihohi

A fadin Najeriya gwamnatoci na ci gaba da gina filayen jiragen sama cikin shekaru goma da suka gabata sai dai da dama suna nan an gina basa aiki.

Cikin wadannan filayen jiragen saman sun hadar da Muhammadu Buhari Airport (Ebonyi) da Akwa Ibom Airport (Uyo) da Bayelsa International Airport da Ogun Cargo Airport da MKO Abiola International Airport (Osun) da Ekiti Cargo Airport da Anambra Cargo Airport (Umuleri) da Abia Airport da Wachakal Airport (Damaturu) da Dutse International Airport.

Sauran sun hadar da Gusau Airport da Zamfara Airport da wacce ake son samarwa ta Auchi Airport da Gombe Airport. Najeriya kawo yanzu na da kimanin filin tashi da saukar jiragen sama 32.

Wani rahoto na Nairametrics (report) ya bayyanar da cewa a shekarar 2022 biyar daga cikin wadannan filayen jiragen sama kaso 89.7 cikin 100 na yyukan da ake bukata a wannan fanni su suke bayarwa ga fasinjoji miliyan 16 a Najeriya. Sauran filayen jiragen saman 27 na aiki ne na kaso 10.3 cikin dari na ayyukan da ake bukata a fannin.

Manyan filayen jiragen saman sune: Murtala Muhammed International Airport (Lagos) da Nnamdi Azikiwe International Airport (Abuja) da Port Harcourt International Airport da Mallam Aminu Kano International Airport (Kano) da Akanu Ibiam International Airport (Enugu).

Babban Darakta a hukumar da ke lura da harkokin sufurin jiragen sama ta The Nigerian Civil Aviation Authority (NCAA), Musa Nuhu,yayi magana kan yawaitar filayen jiragen sama a Najeriya wadanda ya bayyana da zama babban nauyi ga kasa.

”Wasu daga cikinsu na karbar jirage daya ko biyu a mako-wasu ma sai jiragen manyan mutane kadai ke sauka, dole a duba wannan batu domin suna janye kudade da abubuwan da NCAA ke da su.” kamar yadda yayi gargadi.

Baya ga nauyi da suke tattare da shi, wasu daga cikin wadannan filayen jiragen sama a kwai zargin cin hanci da rashawa a kansu da sanya kudade inda bai dace ba, alal misali ana zargin cewa ana amfani da filin tashi da saukar jiragen sama na Zamfara ana fasakaurin albarkatun kasa irin zinare zuwa kasashen waje.

A shekarar 2021, gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa ta haramta tashin jirgi a Zamfara don dakile “safarar zinare da makamai.”

Kwararru na bayyana cewa akasari wadannan filayen jiragen sama aikinsu na takaita ne ga gwamnoni da wasu masu hannu da shuni kalilan wadanda ke amfani da su don bukatar kansu.

Tashoshin jiragen kasa hanya mafi karbuwa

A shekarar 2023 tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rattaba hannu  kan wata kwaskwarima ga kundin tsarin mulki inda aka ba da dama na sanya hannun gwamnatin jiha ta zuba jari wajen samar da layin dogo na jiragen kasa.

Shekaru uku kenan da samun wannan dama amma jihohi kadan ne suka amfana da wannan tsari.

Duk da yake kwararru na cewa samar da layin dogo na cin makuden kudade, yafi zama abin karbuwa da ke tafiya da kowa a fagen sufurin al’umma idan aka kwatanta da sufurin jiragen sama.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »