African LanguagesHausa

Cutar Lassa Fever: Yadda ake kamuwa da ita, alamu, kariya da magani yayin da NCDC ta ayyana dokar ta baci a kan cuta

A watan da ya gabata, watan Maris 2023, Cibiyar Kule da Cututtuka ta kasa NCDC ta ayyana dokar ta baci kan Lassa Fever ko kuma masassarar Lassa. Dr Ifedayo Adediba, darakta janar na cibiyar ta ce an ayyana dokar ta bacin ne bayan da aka yi nazarin hadarin cutar da kuma karuwar da aka samu a yawan mutanen da suka kamu da cutar.

A rahotonta,  dangane da halin da cutar ke ciki, hukumar ta ci mutane 104 suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da cutar a bana, daga cikin mutane 636 din da suka kamu da ita a jihohi 22, abun da ya tabbatar da cewa kwayar cutar ta dawo da karfinta.

Mece ce Lassa Fever ko kuma Masassarar Lassa?

Lassa fever zazzabi ne da ake samu daga dabbobi  wanda ya fara bulla a garin Lassa da ke jihar Bornon Najeriya a shekarar 1969. Kwayar cutar ta yi kamari a yawancin yankunan yammacin Afirka wadanda suka hada da Laberiya, Saliyo, Guinea da Najeriya. Sa’annan kwayar cutar Lassa ce ke janyo masassarar wadda ke da dangi da kwayar cutar da aka fi sani da Arenavirus – kwayoyin cutar da ake samu daga fitsari, ko yawu, ko ruwan jikin nau’in berayen da ke dauke da cutar. 

Mutun na iya samun Lassa fever kai tsaye daga berayen da ke dauke da cutar ko kuma bahayarsu kuma ma’aikatan lafiya kan samu daga mutanen da ke dauke da cutar idan har sun taba ruwan jikinsu.

Dokar ta baci kan Lassa Fever: Me hakan ke nufi?

Bisa bayanan Dr Sandra Mba, shugabar sashen da ke kula da Lassa fever a NCDC, idan  aka ayyana dokar ta baci, a kan fadada kwamitin da ke sanya ido kan cutar zuwa matakin kasa ta yadda za’a karfafa yunkurin da ake yi wajen shawo kan cutar ta Lassa Fever a kasar baki daya.

Dr Mba ta ce dokar ta bacin da aka sa a Lassa fever ya zo ne bayan da sakamakon nazarin da aka yi dangane da hadarin cutar ya nuna cewa akwai yiwuwar samun karuwa sosai a yaduwarta cikin kasar. Ta kuma kara da cewa dokar ta bacin za ta taimaka wajen samar da matakai daban-daban wadanda za su yaki cutar domin EOC za ta sami damar amfani da kayayyakin gwamnati daga wasu mahimman sassan gwamnati wadanda ke da kwarewa da kayan aiki irin su ma’aikatar noma da cigaban karkara, ma’aikatar muhalli da ma wadansu kamfanonin fararen hula ko masu zaman kansu.

Yanayin kamuwa da cutar 

Ina iya kamuwa da Lassa fever ta wadannan hanyoyin:

1. Taba berayen da ke dauke da cuta: Mutane kan kamu da cutar da zarar sun taba fitsari, bahaya, miyau ko jinin berayen da kan kamu da cutar wadanda aka fi sanin su da beraye masu nau’in Mastomys, wadanda kuma suka fi yawa a yankin yammacin Afirka.

2. Yaduwa daga mutun zuwa mutun: Mutum zai iya kamuwa da cutar idan har ya taba jini, fitsari, yawu ko kuma dai duk wani abun da ke da ruwa a jikin wanda ke dauke da kwayar cutar. 

3. Taba kayayyakin da ke da kwayar cutar a jikinsu: Ana iya samun kwayar cutar daga kayayyakin da aka shafawa cutar irinsu zanen gado, riguna da kayayyakin aiki a asibiti.

4. Cin abincin da ke da cutar a jikinshi: Cin abincin da ke fitsari ko kashin berar da ke dauke da cutar ma zai iya haddasa cutar a jikin dan adam.

5. Ana iya shakar cutar ta iska: Akwai kzma hujjar cewa cuta ce da ake iya kamuwa da ita ta shakar iska idan tana ciki. Wannan na farauwa musamman a dakunan gwaji.

Alamu

Kusan mutane  takwas cikin goma  na mutanen da kan kamu da cutar ba su ganin wasu alamu, kuma inda akwai alamu, yawanci su kan bayyana ne daga daya zuwa uku bayan mutun ya kamu da cutar. Wasu lokuta ba su da kaifi wata sa’a kuma sukan kasance da kaifi sosai.

Alamun  da akan fara gani sun hada da zazzabi, ciwon kai, zafin jiki, ciwon makogwaro, tari da kasala. Wadannan alamu sun yi kama na irin cututtukan da ake yawan kamuwa da su a rayuwar yau da kullun dan haka daga farkon kamau da Lassa Fever ba’a iya ganewa ko ita ce domin ba za’a iya banbanta ta da sauran cututtukar cikin sauki ba.

Yayin da cutar ke kara yaduwa a jikin mutun ne alamun da suka fi tsanani suke bayyana, wadanda suka hada da ciwon ciki, amai, gudawa, da matsala wajen numfashi sai kuma fitowar jini daga baki da hanci da sauran gabobin jiki. Wasu lokutan da cutar kan iya tsanani ta kan yi lahani a mahimman gabobin dan adam wanda yawanci kan kai ga rashin rai.

Abubuwan da ke tattare da hadari

Akwai abubuwa da yawa da ke kara wa mutun yiwuwar kamuwa da Lassa fever. Wadannan sun hada da:  

1. Zama ko kuma tafiya a yankunan da ke fama da cutar: Ganin yadda cutar ta fi kamari a yankunan yammacin Afirka, mutanen da ke zama a wurin ko kuma wadanda ke yawan zuwa yankin sun fi fuskantar hatsarin kamuwa da cutar.

2. Taba Berayen da ke dauke da cutar: Ainihin hanyar da aka fi kamuwa da cutar ita ce ma’amala da berayen da ke dauke da cutar ko kuma kashin su. Wadanda ke aiki da beraye kamar manoma ko kuma wadanda ke aiki a dakunan gwaje-gwaje sun fi kasancewa cikin hadarin kamuwa da cutar.

3. Taba ruwan jikin wanda ke dauke da cutar: Ma’aikatan lafiya da iyalan wanda ke dauke da cutar na fuskantar babban hadarin kamuwa da ita su ma domin mutun na iya samun Lassa fever daga wani idan har ya taba jini, fitsari ko kuma dai wani nau’in ruwan da ke fita daga jikin wanda ke dauke da cutar.

Rigakafi da kariya

Matakai da yawa ne ake dauka idan har ana so a yi rigakafin da zai hana mutun kamuwa da cutar. Wadannan matakan za su iya taimakawa wajen rage hadarin kamuwa da cutar:

1. Kada a taba beraye ko a guji inda su ke: An fi kamuwa da cutar ne idan an taba bera ko kuma wani sinadarin da ya fito daga jikin shi. Dan haka a guji taba su ko kuma ma ajiye abinci inda za su iya zuwa su sa baki ko su yi bahaya a kai.

2. Tsabtace kai da muhalli: Wanke hannu da sabulu da ruwa na iya hana kamuwa da Lassa fever. Tsabtace muhalli ta yadda beraye ba za su iya rayuwa a wurin ba yana da mahimmanci.

3. Amfani da kayayyakin kariya: Idan har za’a share kashin su da sauaransu, yana da mahimmanci a yi amfani da kayyakin da za su kare jikin mutun daga tabawa, kayayyaki irinsu safar hannu, takunkumin tare fuska, maganin kariya da dai sauransu dan kare kai daga taba wani abu mai ruwa daga jikin berar. 

4. Ilimantar da al’umma: Fadakar da al’umma dangane da Lassa fever da yadda ake kamuwa da ita na iya taimakaw wajen kare cutar daga yaduwa. Wannan zai iya hadawa da talla ko kuma sanarwa dangane da mahimmancin wanke hannu, kashe beraye ko korarsu daga inda kasancewarsu ke zaman hadari sai kuma tsabtace abinci.

5. Rage habakar beraye: Rage yawan beraye ta hanyar dana tarko da sa musu magani na iya rage yaduwar cutar.

Magani

Babu wani magani takamai-mai na Lassa Fever, kula da wanda ya kamu da shi yawanci  tallafi ne kawai. Wadanda ke da nau’in cutar mai tsanani wata kila sai an hada da asibiti inda za su sami irin kulawar da suke bukata kamar karin ruwa da shakar iska da karin jini.

Ana kuma iya bayar da magungunan da ke dakusar da karfin kwayoyin cuta wadanda ake kira antiviral. Magana irin su ribavirin, sun nuna cewa ana iya amfani da su daga farkon kamuwa da cutar. Sai dai nassarar magungunan har yanzu abu ne da babu tabbaci domin ba lallai ne su yi aiki ba. 

Hade da kulawar da za’a iya ba su, kula da duk wata matsalar da ka iya tasowa yana da mahimmanci. Misali, wadanda ke zubar da jini na iya bukatar karin jini ko kuma wadansu abubuwan da ke da nasaba da jini. Yayin da wadanda za su fiskanci matsalar numfashi kuma su ma za su bukaci tallafi ta wannan fannin.

A karshe

Lassa fever cuta ce mai hadarin gaske wadda aka fi samu a yankunan da ke yammacin Afirka. Cutar ta kan yadu daga berayen da ke dauke da ita ne zuwa mutane, su kuma wadanda suka kamu da ita na iya baiwa wadansu, musamman na kusa da su bayan sun taba jini, miyau, fitsari ko kashi ko ma dai duk wani abun da ruwa a jikin su. Alamun Lassa fever sun hada da zazzabi, ciwon kai, ciwon jiki, tari da kasala.

Show More

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button
Translate »