Kanumfari Asalin hoton: Medical News Today
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Bayanan Facebook da dama na da’awar cewa idan har aka jika kanumfari a ruwan zafi, ya na iya kawar da rashin haihuwa.

Hukunci: Karya ce! Sakamakon bincike da ma bayanan da muka samu daga kwararru duk sun karyata hakan.
Cikakken bayani
Kwanan nan, masu amfani da soshiyal mediya suka fara yada wasu bayanan da ke zargin wai idan aka jika kanumfari a ruwan zafi ya na iya kawar da rashin haihuwa, ya ma bukaci mata da su gwada su gani.
Bayanan, wadanda ke dauke da hoto daya da bayani iri daya, ya bayyana cewa wannan tsimin na ruwan zafi da kanumfari na iya sa macen da ba ta ganin jinin hailarta ta fara gani, sa’anann kuma ya na kara daure farjin mace, ya kuma warkar da ita daga irin cututtukan da kan shafi gaban mace.
Bacin haka, bayanin ya ce akwai kuma wasu karin alfanu kamar karawa mata sha’awa da da wanke mahaifa. Haka nan shi ma namiji na iya samun kuzari daga tsimin. Duk wanda ke sha’awar amfani da tsimin ana bayar da shawarar shan shi da safe da yamma dan samun sakamako mai inganci.
To amma shin hakan gaskiya ne? DUBAWA ta gudanar da bincike dan tantance gaskiyar lamarin.
Tantancewa
Kanumfari na daya daga cikin kayan kanshin da aka dade ana amfani da su wajen yin wasu magunguna. To sai dai har yanzu ana gudanar da bincike kan ainihin karfin shi da ma yadda ake amfani da shi. Ana hasashen cewa yana da sinadaran da ke fitar da kwayoyin cuta daga jiki da ma wadanda ke kare mutun daga kamuwa da illolin kwayoyin cutar.
Wani nazarin da aka yi kan kaifin kanumfari, da wasu kayan kanshin na ‘yan China har da abin da suke kira doya a kan beraye mata ya nuna cewa kayayyakin na aiki. Wadanda suka gudanar da binciken sun gano cewa shan jikakken kanumfarin na iya taimakwa wajen samun haihuwa domin zai fitar da cututtuka ya rage kumburi ya kuma farfado da wuraren da suka bushe.
To sai dai haka sun bayyana bukatar amfani da sinadaran kan ainihin matan da suke neman haihuwar dan tabbatar da kaufin su a zahiri
Wani binciken kuma a kimiyyar haihuwa ya bukaci ya gano karfin kanumfari a kan jikin mace ya nuna cewa ana bukatar a gudanar da bincike na musamman a kan kanumfari kafin a kai ga tantance irin taimakon da ya ke bayarwa. Ko da shi ke binciken ya nuna cewa akwai abubuwa da dama da ke tasiri a kan kaifin maganin da aka yi da kanumfarin alal misali, irin kanumfarin da yadda aka tsinko shi, yawan da ya dace a yi amfani da shi, tsawon lokacin da ya kamata a yi ana amfani da shi da ma abin da ya janyo matsalar tun farko.
DUBAWA ta tuntubi likitan mata wato Obstetrician da Gynaecologist, Qudus Lawal, wanda ya fada mana cewa wannan zargin ba komai ba ne illa karya.
Likitan ya ce babu wata hujja a kimiyyance da ke goyon bayan wannan da’awar. Ya fada mana cewa akwai binciken da aka yi a kan dabbobi a baya, amma duk da cewa akwai wadanda suka sami sauki, akwai rahotannin da ke nuna cewa a wasu kara tabarbarewa lamarin ya yi musamman maza.
A Karshe
Zargin cewa kanumfarin da aka jika a ruwa zai iya warkar da rashin haihuwa da suaran wasu cututtukan da suka shafi mata ba gaskiya ba ne domin babu hujjoji na kimiyya da suka goyi bayan wannan da’awar.
